141228xiaochi.mp4
|
To daga Beijing ziyararmu ta kai mu birnin Xi'an wanda yake da dogon tarihi na sama da shekaru dubu shida. Wannan birni a nan ne aka fara kafa birnin kasar baki daya. Yana jawo hankalin masu yawo bude ido saboda kayayyakin tarihu da al'adu da dama da ake dashi a wajen.
Makulashe snacks da muka dandana a kan titunan wannan birni da ake yi da shinkafa da dabino da wake ga su nan dai iri iri wanda za ka mika kudinka a baka ba sai ka tsaya dakin cin abinci ba.