Yan wasan Jamus Thomas Muller, da Miroslav Klose, da Sami Khedira ne dai suka ciwa kungiyar tasu kwallaye biyu-biyu, kafin Abdrew Schurrle ya jefa kwallo cikon ta 7 a ragar Brazil. Ana kuma daf da tashi ne, Oscar ya ramawa Brazil kwallo daya tilo da suka samu.
Wannan sakamako dai ya daga matsayin Klose na Jamus, wanda a yanzu ya zamo 'dan wasa mafi yawan zura kwallo, a tarihin gasar cin kofin duniya da kwallaye 16, sama da tsohon 'dan kwallon Brazil Ronaldo wanda ke da kwallaye 15 a wasannin da ya buga cikin gasar.