in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Tarayyar Najeriya
2014-05-04 16:14:13 cri

Jamhuriyar tarayyar Najeriya tana kudu maso gabashin Afirka ta yamma, kuma tana daura da mashigin tekun Guinea da tekun Atlantic a kudanci. Fadin kasar ya kai kimanin muraba'in kilomita 923768, kuma birnin Abuja shi ne fadar mulkin kasar.

Yanayin kasa a arewacinta ya fi na kudancin kasa tudu, kuma akwai koguna da dama a kasar. Yanayin kasar ya hada da yanayin zafi da na iska, akwai yanayin zafi, da na damina a kasar, yayin da matsakaicin mizanin yanayin zafi ke tsakanin Salsiyos 26 zuwa 27.

Yawan mutanen kasar ya kai miliyan 168 bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2011, kuma akwai kabilu sama da 250 a kasar, da suka hada da kabilar Hausa-Fulani dake arewacin kasar, wanda yawan mutanenta ya kai kashi 29 bisa dari na daukacin jama'ar kasar, sai kabilar Yoruba dake yammacin kasar, mai yawan mutanenta da ya kai kashi 21 bisa dari, da kuma kabilar Igbo dake gabashin kasar, da yawan mutanenta ya kai kashi 18 bisa dari, da ma sauran kabilu da dama.

Kimanin rabin mutanen kasar na bin addinin Musulunci ne yayin da kashi 40 bisa dari Kirista ne, sai kuma kashi 10 bisa dari dake bin sauran addinai.

Shugaban kasar mai ci, kuma babban kwamandan rundunar sojin kasar Najeriya shi ne Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

Huldar da ke tsakaninta da kasar Sin: Tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Najeriya a ranar 10 ga watan Faburairun shekarar 1971, sassan biyu sun raya huldar hadin gwiwa da abokantaka yadda ya kamata. Sa'an nan a shekarar 2005 shugabannin kasashen 2 sun cimma ra'ayi daya kan kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Kana a shekarar 2009, a karon farko kasashen 2 suka tattauna kan manyan tsare-tsaren da za su aiwatar.

A shekarun da suka gabata, manyan jami'an kasashen 2 sun yi mu'amala tsakaninsu yadda ya kamata. Kuma a watan Afrilun shekarar 2002, shugaba Jiang Zemin na kasar Sin ya ziyarci Najeriya. A watan Oktoba na shekarar 2004, Adolphus Nduneweh Wabara, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya ziyarci Sin, kuma a watan Nuwamba na wannan shekara, Wu Bangguo, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya ziyarci Najeriya. Haka kuma a watan Afrilu na shekarar 2005, shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya ya ziyarci Sin. A watan Afrilu na shekarar 2006, shugaba Hu Jintao na Sin ya ziyarci Najeriya. A watan Nuwamba na shekarar 2006, shugaba Obasanjo ya halarci taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. A watan Faburairu na shekarar 2008, shugaba marigayi Umaru Yar'Adua na Najeriya ya ziyarci kasar Sin. A watan Satumba na shekarar 2012, Aminu Tambuwal, shugaban majalisar wakilan Najeriya ya halarci babban taron shugabannin masana'antu na kasa da kasa da aka yi a kasar Sin. Kuma a watan Yuli na shekarar 2013, shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ziyarci kasar Sin, kana a watan Nuwamban shekarar 2013, Zhang Dejiang, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya ziyarci kasar Najeriya.

Sin da Najeriya sun daddale yarjejeniyoyin da suka shafi cinikayya, da tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, kuma sun kafa hadadden kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da ciniki. Najeriya tana kan gaba a matsayi na uku cikin jerin kasashen Afirka dake yawan cinikayya da kasar Sin, kuma ita ce babbar kasuwa ta biyu a Afirka ga kayayyakin kasar Sin, wadda har wa yau kasa ce da kasar Sin ke yawan zuba jari. A shekarar 2013, yawan kudin ciniki a tsakanin sassan biyu ya kai dalar Amurka biliyan 13 da miliyan 590.

Sin da Najeriya sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da suka shafi al'adu da jami'o'insu. Jami'ar Lagos da ta Azikiwe na da cibiyar Confucius ta koyar da yare da al'adun Sinawa. A shekarar 2010, wasu kafofi biyu na gidan talibijin na kasar Sin, wato CCTV4 da CCTV9 sun fara gabatar da shirye-shiryensu a Najeriya. A kuma watan Mayun shekarar 2012, an kafa cibiyar al'adun Najeriya a nan Beijing, babban birnin kasar Sin. A yayin ziyarar Zhang Dejiang, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a Najeriya cikin watan Satumbar shekarar 2013 ne kuma, aka bude cibiyar al'adun kasar Sin da aka kafa a Abuja, hedkwatar Najeriyar. (Maryam, Tasallah, Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China