in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Tarayyar Afirka
2014-04-24 17:23:09 cri

Asalin kungiyar tarayyar Afirka ko (AU) a takaice, kungiya ce ta hadin kan Afirka da aka kafa a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 1963. A ranar 9 ga watan Nuwambar shekarar 1999 kuma, aka zartas da sanarwar "Sirte" a taron kolin kungiyar hadin kan Afirka karo na hudu, inda aka tsai da kudurin kafa kungiyar tarayyar Afirka, kungiyar da daga baya a watan Yulin shekarar 2002 ta maye gurbin kungiyar hadin kan Afirka.

An sanya ranakun 25 ga watan Mayu, da 9 ga watan Satumba na kowace shekara a matsayin "Ranar Afrika", da "Ranar Tarayyar Afrika" domin tunawa da kafuwar kungiyoyin OAU da AU.

Kungiyar AU na kunshe da kasashe mambobi 54. Kuma shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz na kasar Mauritania ne ke shugabantar kungiyar a wannan zagaye, bayan hawansa kujerar a ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2014, inda zai yi wa'adin aikin na shekara daya. Shugabar kwamitin kungiyar ita ce tsohuwar ministar harkokin cikin gidan kasar Afrika ta kudu, uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, wadda ta lashe zaben da aka yi a taron kolin kungiyar karo na 19 a watan Yulin shekarar 2012, ta kuma kama aiki a watan Oktobar shekarar 2012.

An kafa hedkwatar kungiyar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Adireshinta na shafin intanet shi ne: http://www.au.int/.

Dangantakar dake tsakanin kungiyar AU da kasar Sin: Kasar Sin na yin cudanyar sada zumunta da hadin kai yadda ya kamata da kungiyar AU, da hukumar da ta gabace ta wato OAU, ta kuma ba su iyakacin taimakonta.

Tun bayan da aka kafa kungiyar AU a shekarar 2002, kasar Sin na aikawa da tawagogi don halartar taron shugabannin kungiyar a kowace shekara. A watan Maris na shekarar 2005, kasar Sin ta kasance daya daga cikin rukunin farko na kasashen da ba mambobin kungiyar ba wajen aikewa da wakilinta ga kungiyar.

A 'yan shekarun baya, Sin da kungiyar AU sun kara zurfafa dangantakarsu. A watan Nuwamba na shekarar 2008, an shirya taron shawarwari kan manyan tsare-tsare karo na farko a tsakanin Sin da AU a hedkwatar AU. A watan Janairu na shekarar 2011, karo na farko ne Sin da AU sun shirya taron shawarwari a tsakaninsu kan manufofin diplomasiyya. A watan Oktoba kuma, an zartas da kuduri a taron manyan jami'ai karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, inda aka amince da kwamitin AU ya zama mamba a hukunce ta dandalin.

A watan Fabrairu na shekarar 2013, shugabar kwamitin AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta kawo ziyara a Sin, babban sakataren JKS Mista Xi Jinping da wakilin majalisar gudanarwa ta Sin Mista Dai Bingguo sun gana da ita bi da bi. A ranar 25 ga watan Mayu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga taron koli na musamman da AU ta shirya don taya murnar ranar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar Hada Kan KasashenAfirka, OAU. A wannan rana kuma, shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Zhang Dejiang ya halarci liyafar da ofisoshin jadakancin kasashen Afirka da ke Sin suka shirya don taya murnar ranar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar OAU.

Sin da AU sun inganta mu'ammala da samun sulhuntawa a tsakaninsu a fannonin sauyin yanayi, da shawarwari zagaye na Doha na kungiyar cinikin duniya wato WTO da dai sauran manyan batutuwan duniya da na kasashen Afirka. AU ta nuna goyon baya ga kasar Sin a kan abubuwan da suka shafi babbar moriyar kasar Sin. Kasar Sin ta bayar da taimako ga AU wajen karfafa kwarewarta a fannin raya kasa, da kiyaye zaman lafiya. (Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Danladi Jin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China