in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Kenya
2014-05-04 16:13:43 cri

Jamhuriyar Kenya kasa ce dake gabashin Afirka, layin ikwaita ya ratsa tsakiyarta, yayin da kuma babban kwarin gabashin Afirka ya ratsa ta daga kudu zuwa arewa. Fadin kasar ya kai murabba'in kilomita 582,646. Birnin Nairobi shi ne hedkwatar kasar Kenya, akwai kuma tudai da dama a kasar. Tsayinta ya kai mita 1500 daga kasan teku. Zafin yanayi ya kai digiri 22 zuwa 26, yayin da sanyi ke kaiwa digiri 10 zuwa 14.

Kasar Kenya na kunshe da mutane miliyan 41(a shekarar 2011), yayin da aka samu kabilu 42 a kasar. A cikin jama'arta, kashi 45 cikin dari suna bin addinin Furotesta, yayin da kashi 33 cikin dari suke bin addinin Katolika, yayin da kashi 10 cikin dari suke bin addinin Musulunci, yayin da saura kuma suke bautawa kayayyaki da bin addinin Indiya.

Shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta ya hau makaminsa a watan Maris na shekarar 2013, yayin da ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 9 ga watan Afrilu na shekarar 2013.

Dangantaka tsakaninta da Sin: Sin da Kenya sun kulla huldar diplomasiya tsakaninsu a ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 1963. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantakar tana bunkasa cikin sauri.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya a shekarar 1978, yayin da suka daddale yarjejeniyar ba da kariya ga zuba jari a shekarar 2001, yayin da suka kafa kwamitin kulawa da cinikayya tsakaninsu da zuba jari da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da fasaha a watan Maris na shekarar 2011.

A watan Satumba na shekarar 1980, Sin da Kenya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin al'adu. Kamfanin dillancin labaru na Xinhua, da gidan talibijin na CCTV na kasar Sin, da gidan rediyon na CRI dukkansu sun kafa hedkwatarsu ta Afirka a Nairobi. Tashar rediyon FM ta farko da gidan rediyon CRI ya kafa a ketare ta fara aiki a birnin Nairobi a watan Faburairu na shekarar 2006, yayin da tashar rediyon FM ta Mombasa ta fara aiki a watan Janairu na shekarar 2011. Bayan haka, reshen tashar talibijin ta CCTV a nahiyar Afirka ya kafu tare da fara aikinsa a birnin Nairobi a watan Janairu na shekarar 2012. A watan Disamba na shekarar 2012 kuma, an fara gabatar da jaridar China Daily ta Afirka a birnin Nairobi. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China