in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar kasar Angola
2014-05-04 16:14:00 cri

Jamhuriyar kasar Angola tana kudu maso yammacin nahiyar Afirka, fadin kasar ya kai murabba'in kilomita miliyan 1 da dubu 246 da dari 7. Luanda shi ne babban birnin kasar. Kasar tana da yankin dake da sararin kasa, da duwatsu da kuma tuddai. Yankin yammacin kasar dake bakin teku na cikin kwari, yayin da kuma gabashin kasar ke sashen tudu. Haka kuma kaso 65 bisa dari na yankunan kasar na da tsayin mita 1000 zuwa 1600 daga lebur din teku.

Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2013, yawan mutanen kasar Angola ya kai miliyan 20 da dubu 700. Inda daga cikinsu kaso 49 bisa dari ke bin darikar Roman Katolika ta addinin Kirista, sai kuma kaso 13 bisa dari dake bin wasu darikun addinin na Kirista, yayin da kuma sauran 'yan kasar ke bin addinan gargajiya.

Shugaban kasar mai ci Jose Eduardo Dos Santos ya hau kan kujerar mulkin kasar ne a watan Satumbar shekarar 1979.

Huldar dake tsakaninta da kasar Sin: Angola ta kafa huldar diplomasiya da kasar Sin a ranar 12 ga watan Janairun shekarar 1983, har ya zuwa yanzu kuma kasashen biyu na gudanar da dangantakarsu yadda ya kamata. A kuma watan Nuwambar shekarar 2010, kasashen biyu suka kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.

Angola ta kasance babbar aminiyar cinikayya ta biyu ta kasar Sin a Afirka, inda a shekarar 2013, yawan ciniki tsakaninsu ya kai dalar Amurka miliyan dubu 35 da dari 9 da arba'in. Kafin wannan wato a shekarar 2011, kasashen biyu suka sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar kwadago.

A halin yanzu, kasuwar ba da kwangilolin ayyuka ta kasar Angola ta kasance ta biyu ga kasar Sin a dukkanin fadin Afirka. Inda ya zuwa karshen shekarar 2012 da ta gabata, yawan kwangilolin aikace-aikace da kasar Sin ta kulla da Angola ya kai dalar Amurka biliyan dubu 40.2. Haka nan yawan kamfanonin kasar Sin mallakar gwamnati da masu zaman kansu a kasar ta Angola suka kai sama da dari daya, yayin da Sinawa masu ayyuka daban daban kimanin dubu dari biyu ke zaune a kasar Angola. (Jamila Zhou, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China