in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar demokuradiyyar tarayyar kasar Habasha
2014-05-04 16:14:27 cri

Jamhuriyar demokuradiyar tarayyar kasar Habasha, kasa ce dake arewa maso gabashin Afirka. Tana kuma da fadin murabba'in kilomita wajen miliyan 1 da dubu dari daya, fadin kasar ya kunshi tudai da suka kai kashi biyu bisa ukunta, ciki hadda masu tsayin da ya kai kimanin mita 3000 daga kasan teku. A sabili da haka, aka radawa Habasha sunan "Jigon nahiyar Afirka".

Yawan al'ummar kasar sun kai miliyan 91 bisa kididdigar shekarar 2011, dake kunshe da kabilu sama da 80. A birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar kadai, akwai mutane sama da miliyan 4 bisa kididdigar shekarar 2011 da ta gabata.

Shugaban kasar Habasha, Mulatu Toshome ya hau mukaminsa ne a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2013, yayin da shi kuma Hailemariam Dessalegn ya zama firaministan kasar.

Dangantaka tsakaninta da Sin: Sin da Habasha sun kulla huldar diplomasiya a ranar 24 ga watan Nuwambar shekarar 1970. A cikin shekarun da suka wuce, dangantaka tsakanin kasashen biyu tana bunkasa kamar yadda ake fata.

An fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Habasha a fannonin tattalin arziki da fasaha ne a shekarar 1971. Kuma kawo yanzu Sin ta taimakawa Habasha wajen gudanar da ayyuka 19, da suka hada da gina hanyoyi, da cibiyoyin jiyyar dabbobi, da tasoshin samar da wutar lantarki, da ayyukan samar da ruwa da sauransu. A shekarar 2012, jimillar cinikayya tsakaninsu ta kai dala miliyan 1839.

A shekarar 1988, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin al'adu. Ya zuwa yanzu kuma, Sin ta karbi daliban Habasha 529 da suka sami guraben karo karatu daga gwamnatin kasar Sin.

Kwalejin Confucius ta farko ta fara aiki a kasar Habasha ne a watan Faburairun shekarar 2010. Kuma daga shekarar 1974 zuwa yanzu, Sin ta tura rukunin likitoci har sau 17 zuwa Habasha, wadanda suka kunshi jimillar likitoci 270. Kuma har zuwa yanzu, wani rukuni na likitoci 15 na ci gaba da aiki a kasar.

Daga watan Agusta na shekarar 2005 zuwa yanzu, Sin ta tura matasa masu aikin sa kai sau 3 zuwa kasar Habasha, wadanda yawansu ya kai mutane 72. Har wa yau Habasha ta kasance kasar Afirka ta farko da matasa masu aikin sa kai suka halarta, kuma kasar da Sinawa ke iya zuwa yawon shakatawa bisa radin kansu. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China