in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar da ke tsakanin Sin da Nijeriya
2013-07-08 14:55:08 cri
A ranar 10 ga watan Febrairu na shekarar 1971 ne, aka kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen Nijeriya da Sin, tun kuma wannan lokaci ake gudanar da dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunta tsakaninsu yadda ya kamata.

A watan Afrilu na shekarar 2005, shugaban kasar Nijeriya na lokacin, Olusegun Obasanjo ya kawo ziyara kasar Sin a hukunce, inda aka daddale hadaddiyar sanarwa tsakanin kasashen biyu. A watan Afrilu na shekarar 2006, shugaban kasar Sin na lokacin Hu Jintao ya kai ziyara kasar Nijeriya, inda ya yi muhimmin jawabi a zauren majalisar dokokin kasar mai taken "Kara kokari don raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare ta sabon nau'i tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma kasashen biyu sun ba da hadaddiyar sanarwa. Sai kuma, daga ranar 27 ga watan Febrairu zuwa ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2008, shugaban kasar Nijeriya na lokacin Umaru Musa 'yar Addu'a ya kawo ziyara kasar Sin, inda kasashen biyu suka ba da hadaddiyar sanarwa tare. Ban da wannan kuma, a watan Yuli da muke ciki, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan shi ma zai kawo ziyara nan kasar Sin.

A cikin 'yan shekarun nan, bangarorin biyu sun kara inganta hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da hakar iskar gas da man fetur, da manyan ababen more rayuwa, da aikin gona da aikin raya kimiyya da fasaha, kuma an samu babban ci gaba sosai a wadannan fannoni. A shekarar 2005, jimillar kudin cinikayyar bangarorin biyu ya kai dalar Amurka biliyan 2.83, adadin da ya karu da kashi 29.6 cikin 100 bisa na shekarar da ta gabata. Nijeriya ta zama babbar abokiyar huldar kasar Sin a nahiyar Afrika, kana wata babbar kasuwa ce da Sin take saka jari a kasar, inda a shekarar 2009, yawan kudin cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da ta Nijeriya ya kai biliyan 6.5.

A watan Maris na shekarar 2008, jami'ar Nnamdi Azikiwe ta Nijeriya da jami'ar Xiamen ta kasar Sin sun yi hadin gwiwar kafa wani kwalejin confucius wanda ya kasance na farko a Nijeriya. Daga ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 2009, an kafa kwalejin confucius ta biyu a birnin Lagos da ke tarayyar Nijeriya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China