in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Goodluck Jonathan
2013-07-08 13:13:42 cri

Goodluck Ebele Jonathan

An haifi Goodluck Ebele Jonathan a watan Nuwamba na shekarar 1957 a jihar BAYELSA ta kasar Nijeriya, ya sami digirinsa a fannin ilmin dabbobi a jami'ar Fatakwal. Ya taba zama malamin a kwalejin samar da ilmi na jihar RIVERS, mataimakin direktan hukumar raya yankunan da ke samar da man fetur da ma'addinai.

A shekarar 1998 ya shiga jam'iyyar demokuradiyya ta jama'ar kasar Nijeriya PDP, inda ya shiga fagen siyasa, daga shekarar 1999 zuwa watan Disamba na shekarar 2005 ya zama mataimakin Gwamnan jihar BAYELSA, daga baya ya zama Gwamnan jihar bayan an tsige tsohon Gwamnan jihar a lokacin.

A watan Afrilu na shekarar 2007, ya ci zaben zama mataimakin shugaban kasar Nijeriya. A ranar 6 ga watan Mayu na shekarar 2010, shugaba mai ci a waccan lokaci Umaru Yar'Adua ya rasu sakamakon rashin lafiya, abin da ya sa, aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasar. A watan Afrilu na shekarar 2011, ya lashe zaben shugaban kasar.

Bayan hawansa mukamin shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya ci gaba da aiwatar da manufar ba da afuwa ga masu fafutuka a yankin Niger Delta wadda tsohon shugaban kasar Umaru Yar'Adua ya kirkiro, abin da ya kara hadin gwiwar al'umman kasar da ba da tabbaci ga zaman karko a yankin Niger Delta, ban da haka, ya samu ci gaba sosai wajen kyautata yanayin samar da wutar lantarki da makamashi, da kara karfin raya muhimman ababen more rayuwa.

Yayin da yake rike da mukamin mataimakin Gwamnan jihar BAYELSA, Goodluck Jonathan ya taba kawo ziyara nan kasar Sin a shekarar 2000.

Daga ran 9 zuwa ran 12 ga watan Yuli na shekarar 2013, Goodluck Jonathan zai fara ziyarar aiki a kasar Sin.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China