in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya isa Dar es Salaam na Tanzania
2013-03-25 16:04:27 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya isa birnin Dar es Salaam na kasar Tanzania a ranar 24 ga wata domin ziyarar aiki da ake fatan za ta habaka hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasar ta Tanzania, wacce ke gabashin nahiyar Afirka.

Bisa tsarin ziyarar shugaba Xi, zai tattauna da takwaransa na Tanzania Mrisho Kikwete kan muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar dake tsakanin kasashen nasu, inda kuma daga bisani shugabannin biyu za su rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kuma musayar al'adu.

Kasar ta Tanzania ce dai ta biyu baya ga Rasha a jerin kasashen da shugaba Xi ya ziyarta tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Sin a farkon wannan wata na Maris da muke ciki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China