in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kayayyaki kirar Sin sun inganta zaman rayuwar jama'ar Afirka
2013-03-23 15:55:54 cri






A birnin Yiwu da ke gabashin kasar Sin, ana iya samun 'yan kasuwa masu dimbin yawa daga yammacin Afirka, wadanda su kan aika da kayayyakin da suka saya daga birnin zuwa biranen Ikko da Abuja a Tarayyar Najeriya da kuma birnin Dakar na kasar Senegal don sayarwa. Wadannan 'yan kasuwa sun kasance daya daga hanyoyin da kayayyaki kirar kasar Sin suke bita hannun su zuwa kasuwannin Afirka.

Da misalin karfe tara na dare, wasu 'yan kasuwa Hausawa da suka fito daga kasashen Najeriya da Nijar suna gaisuwa da juna da kuma tattaunawa a cikin wani dakin cin abinci na halal da ke cibiyar birnin Yiwu. Wannan lokaci ne da suka fi jin dadi a ko wace rana, wato bayan kammala aiki, su kan zo cin abinci, su yi hira tare da musanyar labarun da suka samu.

Kabilar Hausa wata babbar kabila ce a yammacin Afirka, wadda ta shahara sakamakon nuna bajinta wajen kasuwanci. A wannan zamanin yau, ban da ci gaba na kasuwanci a kasashensu, har ma sun zo kasar Sin don habaka wannan sana'ar tasu.

Malam Ibrahim Inuwa, wani bahaushe ne da ya fara kasuwanci a birnin Yiwu a shekara ta 1997. A wancan lokaci, ya kan je Yiwu don sayen kayayyakin ado na kasar Sin sau biyu a shekara. Bayan shekaru 8 kuma, sai ya yi rajista a birnin, sanan nan ya bude kamfaninsa a nan. Muhimmin aikinsa dai shi ne aikawa da kayayyaki kirar kasar Sin zuwa ga 'yan uwansa da ke birnin Kano. Ya ce, dalilin da ya sa ya zabi kasar Sin da kuma birnin Yiwu shi ne sabo da ya yi amana da ingancin kayayyakinsu. Yana mai cewa,

"kayayyaki kirar kasar Sin na da inganci sosai, kuma akwai araha, wadanda suka taimaka ma zaman jama'a."

Kayayyakin da 'yan kasuwa daga yammacin Afirka su kan saya sun hada da tufafi, kayayyakin dafe-dafe, kananan kayayyakin wutar lantarki, kayayyakin wasan yara da dai sauransu. Hakan ana iya gano cewa, kayayyakin sun shafi fannoni daban daban na zaman jama'ar Afirka.

A ganin Ibrahim Inuwa, yawancin yankunan Afirka na fama da talauci yanzu, wanda ya haddasa jama'a suka gaza sayen kayayyakin masarufi masu tsada. Kayayyaki kirar kasar Sin kuwa na da inganci da kuma araha, wadanda suke biya bukatun jama'ar Afirka musamman na masu fama da talauci, da kuma kyautata matsayin zamansu.

Amma ba dukkan 'yan Afirka ne ke ganin cewa, kayayyaki kirar kasar Sin na da inganci da araha ba. A idanun wasu daga cikinsu, ko da yake kayayyaki kirar kasar Sin na da araha, amma ba su da inganci. Game da wannan batu, Malam Ibrahim ya yi bayanin cewa, akwai dalilai da dama da suka haddasa wannan. Ya ce, ana iya samun kayayayyki iri daban daban a kasuwar Yiwu, kuma kudin ko wane hawa-hawa ne ya danganta da aljihun mutum. Wasu masu samar da kayayyaki na kasar Sin ba su san kasuwar Afirka sosai ba, a ganinsu, Afirka na fama da talauci, don haka su kan gabatar da kayayyaki mafi araha kuma marasa inganci ga 'yan kasuwa daga Afirka. A wani bangaren kuma, wasu 'yan kasuwa daga Afirka su kan dora muhimmanci kan farashin kaya kawai a maimakon ingancinsa domin neman samun babbar riba. Har ma su kan je neman wasu kayayyaki marasa inganci ko kadan don sayarwa. Ibrahim ya kuma bayyana cewa, yanzu gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai kan sanya ido kan ingancin kayayyaki. Hukumar kwastam ta Yiwu ita ma ta kara sanya ido kan kayayyakin da za a fitar da su zuwa ketare, hakan ya sa an hana fitar da wasu kayayyaki marasa inganci. A ganinsa, kiyaye amanar kayayyaki kirar kasar Sin na bukatar kokari na 'yan kasuwa na bangarorin Sin da Afirka gaba daya.

Da karfe 10 da rabi na dare, 'yan kasuwa Hausawa na sallama da juna don komawa masaukansu domin hutawa da kuma jiran zuwan wata sabuwar rana da kuma dimbin kayayyakin kasar Sin. Amma a daidai wannan lokaci kuma, a can Afirka, a cikin kasuwar Alaba ta birnin Ikko, ana ta sayar da kananan kayayyakin wutar lantarki kirar kasar Sin, domin biyan bukatun jama'ar birnin da yawansu ya kai miliyan 18.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China