in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada muhimmancin gudanar da tsarin neman samun ci gaba bisa samar da sabbin kayayyaki
2013-03-05 09:51:23 cri

A ranar Litinin hudu ga wata, babban sakataren JKS Xi Jinping ya jinjinawa wadanda suke halartar taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, yayin da ya shiga shawarwarin da suke, Xi ya jaddada cewa, gudanar da tsarin neman samun ci gaba bisa samar da sabbin kayayyaki na da muhimmanci kwarai da gaske.

A gun taron sassan kimiyya da fasaha, Xi ya jaddada bayan sauraron bayanan membobi 11 na majalisar cewa, gudanar da tsarin neman samun ci gaba bisa samar da sabbin kayayyaki na da muhimmanci sosai, kuma babban mataki ne na kara saurin canza hanyar bunkasa tattalin arziki, da daidaita manyan matsalolin raya tattalin arziki, da kara karfin bunkasa tattalin arziki. A sabili da haka, dole ne kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar neman samun bunkasuwa da ke dacewa da tsarinta, da kara kwarin gwiwar samar da sabbin kayayyaki, da zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin kimiyya da fasaha, a kokarin samun sabon yanayin samar da kayayyaki a kasar Sin, tare da amfaninsa yadda ya kamata, da kara saurin canza matsayin kasar Sin daga wata babbar kasar raya tattalin arziki zuwa wata kasa mai karfi sosai a fannin bunkasa tattalin arziki. Kuma dole ne a kara karfin horar da kwararru, da samar musu kyakkyawan yanayi, da kara musu kwarin gwiwa wajen saddaukar da hikimomi da karfinsu wajen cimma burin kasar Sin.

Ban da haka, shugabannin kasar Sin, Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan, Zhang Gaoli su ma sun jinjinawa membobin majalisar, tare da yin shawarwari dasu kan yadda za a kyautata rayuwar jama'a, karfafa mu'amala tsakanin mashigin tekun Taiwan, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China