in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da Sin ta samu daga albarkatun teku a bara ya kai kudin Sin biliyan 5000.
2013-03-02 21:01:20 cri

Hukuma mai kula da harkokin teku ta kasar Sin ta ba da labari a ran 26 ga wata cewa, bisa kididdigar da aka yi, yawan kudin da Sin ta samu a fannin albarkatun teku a shekarar 2012 da ta gabata, ya kai kudin Sin RMB biliyan 5008.7, wanda hakan ya nuna karuwar da aka samu ta kai kashi 7.9 ciki dari, bisa na shekarar 2011. Haka kuma kudin da Sin ta samu a wannan fanni ya kai kashi 9.6 cikin dari bisa na dukkan GDP kasar.

Sanarwar ta tattalin arziki da ta shafi albarkatun teku ta bara, wadda hukumar ta fitar ta nuna cewa, a wannan shekarar ta 2012, Sin ta kara ba da taimako ga harhada magunguna ta yin amfani da albarkatun hallitun da ake samu daga teku, abin da ya ba da kyakkyawar damar bunkasa wannan sha'ani mai amfani, wanda kuma ya samu bunkasuwa matuka bisa na shekarar 2011.

Ban da haka, na'urorin samar da wutar lantarki ta amfani da karfin iska da aka kafa a kan teku sun samu bunkasuwa matuka. Bugu da kari, yawan ma'addinai da aka fitar daga teku sun karu, an kuma kyautata tsarin wannan sana'a yadda ya kamata.

Bugu da kari sanarwar ta nuna cewa, a shekarar 2012, a karo na farko ne yawan karuwar da aka samu wajen sha'anin hakar mai da gas daga teku ya samu ci baya kadan, sakamakon sauyawar farashin man fetur, da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki a kasar, da kuma kwaskwarima da aka yi a wannan fanni da dai sauran dalilai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China