in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da cikakken zama karo na farko na majalisar CPPCC karo na 12 gobe da yamma a Beijing
2013-03-02 20:59:39 cri

A ranar Asabar 2 ga wata, an shirya taron manema labaru a nan birnin Beijing, inda Mr. Lv Xinhua, kakakin cikakken zama karo na farko na majalisar CPPCC karo na 12 ya ce, za a kaddamar da wannan cikakken zama gobe Lahadi 3 ga wata da yamma a nan Beijing, sannan za a rufe taron a ranar 12 ga wata da yamma.

Mr. Lv Xinhua ya ce, bisa ajandar wannan babban taro, mambobin majaliasar CPPCC za su saurari rahoton da Jia Qinglin, shugaban majalisar CPPC na karo na 11 zai gabatar game da ayyukan da majalisar ta yi cikin shekaru 5 da suka gabata, sannan za su saurari rahoton da Mr. Wan Gang, mataimakin shugaban majalisar zai gabatar kan yadda aka daidaita shirye-shiryen da mambobin majalisar suka gabatar cikin shekarar da ta gabata. Bugu da kari, mambobin majalisar za su halarci cikakken zama karo na farko na majalisar dokokin kasar Sin karo na 12, inda za su saurari rahotonni da za a gabatar game da ayyukan da gwamnati, babbar kotun jama'ar kasar, da babbar hukumar bincike ta kasar suka yi.

Haka kuma, za su zabi sabon shugaban majalisar CPPCC, da mataimakansa, babban sakatare, da mambobin dindindi na majalisar.

Mr. Lv Xinhua ya ce, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na hukumar kasar za su halarci bikin kaddamar wanda kuma rufe wannan cikakken zama na majalisar, kuma za su tattauna kan yadda za a tafiyar da karkokin mulkin kasar tare da mambobin majalisar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China