in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta shiga wasan karshe a gasar AFCON ta bana
2013-02-07 14:48:32 cri

A ranar Laraba ne Najeriya ta fitar da Mali a gasar cin kofin kwallon kafan Afirka dake gudana a kasar Afirka ta Kudu, inda ta samu nasarar kaiwa ga wasan karshe na gasar ta AFCON ta shekara ta 2013.

'Yan wasan na Super Eagles sun doke Mali ne da ci 4 da 1 a wasan da suka yi a filin wasa na Moses Mabhida da ke birnin Durban, sakamakon da ya kawo karshen mafarkin Mali na daukar wannan kofi.

Dan wasan Najeriya mai suna Elderson Echiejile ne ya zura kwallo ta farko da ka bayan da Victor Moses ya garo masa kwallo ta bangaren dama.

Mali dai ta yi ta kokarin farke wannan kwallo, amma masu tsaron bayan Najeriya suka taka musu birki.

An tafi hutun rabin lokaci, 'yan wasan na Super Eagles na da ci 3 yayin da Mali ke nema, inda Brown Ideye ya ci kwallo ta biyu yayin da Emmanuel Emenike ya zura kwallo ta uku.

Ahmed Musa da ya shigo wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ya ci wa Najeriyar kwallonta na hudu a minti na 60, lokacin da ya ratsa masu tsaron gidan Mali.

A minti na 75 ne Mali ta samu damar zura kwallo daya tilo a wasan ta hannun dan wasanta Fantamady Diarra da aka sako bayan hutun rabin lokaci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China