in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardun da ake samarwa da iccen gora a garin Jiajiang
2011-10-14 18:49:19 cri
Assalam alaikum! Masu sauraro, a yankin makwararin kogin Qingyi dake kudu maso yammacin birnin Chengdu na lardin Sichuan, akwai wani kyakkyawan gari mai tsawon tarihi, wanda ake kiransa Jiajiang. Mazauna garin sun mayar da sana'ar samar da takardu a matsayin ginshikin zaman rayuwarsu zuriya bayan zuriya, har ma an lakabawa garin sunan "garin samar da takardun zane-zane na kasar Sin". Takardun da ake samarwa ta hanyar sarrafa iccen gora, da takardun Xuan da muka gabatar a shirinmu na baya, dukkansu takardu ne da masu zane-zanen gargajiya na kasar Sin suka fi son amfani da su. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu je garin Jiajiang dake lardin Sichuan, mu ganewa idanunmu yadda irin wannan takarda take.

Jiajiang, wani tsohon gari ne mai dadadden tarihi dake kudu maso yammacin birnin Chengdu. Tun fil azal, wato daular Tang ta kasar Sin, mazauna garin sun fara amfani da iccen gora don samar da takardu.

Takardun da ake samarwa da iccen gora a garin Jiajiang, takardu ne masu fari fat, kuma masu taushi. Fasahar samar da takardu ta hanyar sarrafa iccen gora a garin Jiajiang ta samo asali ne tun shekaru sama da 1300 da suka gabata, haka kuma ta samu ci gaba mafi sauri a daular Qing. A wancan lokaci, yawan takardun da aka samar a garin Jiajiang ya dauki sulusin yawan takardun da aka samar a kasar Sin baki daya. Tun shekarun 1940 na karnin da ya gabata, wani shahararren mai zane-zanen gargajiya na kasar Sin Zhang Daqian ya kawo sauye-sauye ga wannan nau'in takarda. Daga baya, sauran wasu masu zane-zanen gargajiya na kasar Sin sun yabawa sosai kan irin wannan nau'in takarda wadda aka samar da iccen gora.

A halin yanzu, garin Jiajiang dake lardin Sichuan ya kasance wani muhimmin wurin dake samar da takardu a fannin yin zane-zane da rubuce-rubuce, kuma takardun da ake samarwa a wannan wuri na da inganci sosai. Yang Zhanyao, wanda ke zaune a kauyen Jinhua dake garin Jiajiang na daya daga cikin mutanen da suka gaji fasahohin gargajiya na samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora. Yayin da yake bayani kan tarihin samar da takardu na gidansa, tsoho Yang Zhanyao ya ce:

"Mun gaji fasahohin samar da takardu na iccen gora daga kaka da kakanni, yanzu ina cikin zuriya ta 12 wajen samar da irin wannan takarda. Na fara tafiyar da wannan sana'a tun shekara ta 1961 bayan da na kammala karatu daga karamar makarantar midil."

Kawo yanzu, Yang Zhanyao ya shafe tsawon shekaru 50 yana aikin samar da takardu ta hanyar sarrafa iccen gora. Domin yabawa babbar gudummawar da yayi ga kiyaye al'adun gargajiya, a shekara ta 2006, an zabe shi don ya zama mutumin da ya gaji fasahohin gargajiya na samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora, har ma an lakaba masa sunan "sarkin takardu".

Mista Yang Zhanyao ya gayawa wakilinmu cewa, fasahar samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora ta kunshi matakai 72, wadanda kamata yayi a mayar da hankali sosai kan kowannensu. Saboda irin wahalhalun da ake fuskanta, akwai mazauna kauyen Jinhua da dama wadanda suka yi watsi da wannan sana'a wato samar da takardu. Mista Yang ya bayyana cewa:

"A halin yanzu, mutane sun fi son zuwa ci rani wajen, saboda aikin samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora ba abu ne mai sauki ba, kuma za'a samu karin kudin shiga idan aka tafiyar da aikin ci rani a waje. Musamman ma matasa, akasarinsu sun tafi ci rani, don haka yawan mutanen da suke tafiyar da sana'ar samar da takardu ya ragu sosai."

Duk da haka, a halin yanzu akwai matasa da dama a kauyen Jinhua wadanda suke koyon fasahohin samar da takardu daga Mista Yang Zhanyao, a kokarin ci gaba da kiyayewa gami da yayata fasahohin. Daya daga cikinsu Ma Wencheng ya gayawa wakilinmu cewa:

"Wannan aiki akwai ban sha'awa! Alal misali, takardun da sauran mutane suka samar za su iya lalacewa, amma takardun da muka samar ba za su lalace ba, wannan abu ne mai ban sha'awa gare ni."

Bisa labarin da muka samu, an ce, domin kiyaye tare da gadar fasahohin gargajiya na samar da takardu ta hanyar sarrafa iccen gora, hukumar gundumar Jiajiang ta zuba Yuan sama da dubu 500 don gina wani dakin adana kayan tarihi na samar da takardu. A cikin wannan daki mai fadin murabba'in mita dubu 12, an adana kayayyakin tarihi sama da 2300, da shahararrun nau'o'in takardu na gida da na waje, gami da zane-zane da dama da aka yi ta hanyar amfani da takardun iccen gora da sauransu. Har wa yau kuma, hukumar gundumar Jiajiang ta kafa wata kungiyar 'yan kasuwan dake gudanar da aikin samar da takardun zane-zane da rubuce-rubuce, wadda ke taka rawar a-zo-a-gani a fannin kiyaye takardun da ake samarwa ta hanyar amfani da iccen gora. A nata bangaren, shugabar kungiyar 'yan kasuwan dake gudanar da aikin samar da takardun zane-zane da rubuce-rubuce ta gundumar Jiajiang Madam Song Xiulian ta nuna cewa:

"A halin yanzu, muna mayar da hankali sosai kan raya tattalin arziki da bunkasa harkokin al'adu a gundumar Jiajiang, musamman ma a fannin al'adu. Takardun iccen gora tamkar wani kati ne na gundumarmu. Idan aka ambaci sunan Jiajiang, za'a tuna da cewa, garin Jiajiang shi ne asalin takardun zane-zane da rubuce-rubuce na kasar Sin."

A halin yanzu, samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora ba ma kawai wata sana'ar gargajiya ba ce, har ma yana taka muhimmiyar rawa a cikin zaman rayuwar mazauna garin Jiajiang. Mazauna wurin sun yi amfani da fasahohin samar da takardu a wasu sauran fannoni, ciki har da yin zane-zane, raye-raye, tare da rera wakoki. Alal misali, bisa ayyukan da mutane su kan yi wajen samar da takardu da iccen gora, an kirkiro wani nau'in rawa, wanda ke samun karbuwa sosai a halin yanzu a garin Jiajiang, haka kuma a kowace rana, a kan ga mutane sun yi irin wannan rawa a filaye da lambunan shan iska dake garin.

A matsayin daya daga cikin mutanen da suka gaji fasahohin samar da takardu ta hanyar sarrafa iccen gora a garin Jiajiang, Mista Yang Zhanyao ya bayyana fatansa ga makomar irin wannan takarda, inda ya ce:

"Da farko, ina fatan zan ci gaba da bunkasa fasahohin gargajiya na samar da takardu ta hanyar amfani da iccen gora gami da wadannan matakai 72, ta yadda za su samu bunkasuwa a nan gaba. Na biyu, ko da yake fasahohin samar da takardun, fasahohi ne na gargajiya, amma kamata yayi mu sanya wasu fasahohin zamani a ciki, mu nuna himma da kwazo wajen horar da mutane a wannan fanni, ta yadda fasahohin samar da takardu da iccen gora za su samu kiyayewa da bunkasuwa."

Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, kun dai ji yadda muka gabatar muku da wani nau'in takarda, wadda ake samarwa ta hanyar amfani da iccen gora a garin Jiajiang dake kudu maso yammacin birnin Chengdu na nan kasar Sin. Kuma a cikin shirinmu na gobe, za mu gabatar muku da wani bayani dangane da takardun da ake samarwa a Tibet.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China