in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar Dongba da ke da al'adun gargajiya
2011-10-14 18:48:33 cri
Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa cikin shirye-shiryenmu na "Asalin Takardun kasar Sin", a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da bayani game da takardar Dongba.

Masu sauraro, a yankunan da ke iyakokin lardunan Yunan, Sichuan da jihar Tibet da ke kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wata kabila mai suna Naxi da ke da yawan al'umma dubu 300 kawai, kuma suna da wata fasahar yin takarda ta musamman, kuma an gada wannan fasaha tun shekaru aru-aru da suka wuce, a cikin shekaru fiye da dubu da suka gabata, yayin da 'yan kabilar Naxi ke yin addu'a, su kan yin amfani da wannan takarda don rubuta littattafan addini, sabo da haka, aka lakaba wa wannan takarda suna "takardar Dongba".

"A wani gidan ibada na Beiyue da ke garin Lijiang a lardin Yunan, yara na kabilar Dongba na karanta littattafan addinin Dongba, haka kuma a kan allon da ke gabansu, an rubuta alamomi masu kama da zane-zane, kuma wadannan alamomi su ne kalmomin da al'ummar Dongba suka kirkiro, kuma sun koyi wadannan rubuce-rubuce a kan takardar Dongba zuwa yanzu, yayin da ake bayani game da takardar Dongba, malamin da ke koyar da yaran kabilar Dongba mai suna Shi Chun ya gaya wa wakilinmu cewa, yanzu, ba a samun mutane da yawa da suka iya sarafa takardar Dongba, galibinsu suna cikin kauyuka.

Kauyen Baidi ya kasance wani kauyen da ke kasan wani dutsen, He Yonghong dan kabilar Dongba ne, ya koyi fasahar yin takarda daga mahaifinsa, a wannan rana da safe, ya je saran itacen Yaohua a dutsen, bayan da ya koma gida, ya fara cire bawon itacen, don shirya yin takarda.

He Yonghong ya sa dukkan bawon itacen Yaohua mai launin rawaya a cikin tukwanen da ke dandalin gida, kuma yayin da ya yi takarda, ya bayyana cewa,

"Bayan da ruwa ya tafasa, sai a sa bawon itacen da soda a ciki, har sai bawon ya nuna cikin tsawon rabin sa'a, sai a fitar da su daga cikin tukwanen, a wanke, sa'an nan a daddake shi."

"Ana yni amfani da sanda ne wajen daddakawa."

Bayan da aka daka bawon, sai a sa su cikin ruwa, He Yonghong ya sa su zama ruwa-ruwa.

"Bayan da aka sa su ciki, sai a cakuda su har na tsawon mintoci 2."

Bayan da aka cukuda bawon cikin ruwa, har ya zama ruwa-ruwa, sai a nemi abubuwan da aka tanada, don sa bawo da ya yi ruwa-ruwa ya bushe, daga nan sai a samu takardar Dongba.

Haka kuma, He Zhiguo dan kabilar Dongba kuma wanda shi ma na iya yin takardun Dongba, ya bayyana yanayin wannan takarda, ya ce,

"Launin takarda fari ne, amma ba fari fat ba, kuma an yi takarda ce Dongba da hannu, kuma an gaje ta ne daga kaka da kakani."

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, an yi takardar Dongba ta hanyar gargajiya, kana idan aka kwatanta wannan takarda da sauran takardu, za a ga cewa, takardar Dongba ta fi kauri, sabo da haka, ba a iya cire takarda cikin sauri kuma ba ta saurin kama wuta. Haka kuma, abubuwan da aka yi amfani da su wajen sarrafar takardar, wato furannin Yaohua, ya kasance daya daga cikin tsire-tsiren da ke da guba, sabo da haka, kwari ba za su ciji wannan takarda ba, kuma ba su iya saurin batawa ba, kuma an gada wannan takardar Dongba da kyau, manazarciya a cibiyar nazarin al'adu na kabilar Dongba ta birnin Lijiang He Hong ta ce,

"Ana iya sarrafa wannan takarda cikin sauri, sabo da an gaje ta daga kaka da kakaninmu, kuma wannan na da muhimmanci, kuma kamar yadda muka sani, an samu wani littafi daga gidan daular Qing, yanzu, yana dakin aje litattafai na majalisar dokokin Amurka, kuma wannan na da tarihi na sama da shekaru 300."

Wani yaro dan kabilar Dongba mai suna Chen Si ya amince da darajar takardar Dongba, ya ce,

"Dole ne a yi amfani da takardar Dongba, don rubuta littafi na Dongba, idan ba a yi amfani da takardar Dongba ba, ba za a rubuta kalmar

Dongba da kyau ba, haka kuma idan ka yi amfani da sauran takardu, bayan shekara 1 ko 2, za su sun bace, kamata ya yi a dinga canja wadannan bayanai da aka rubuta, amma idan aka yi amfani da takardar Dongba, za a iya yin amfani da shi har tsawon dauloli da dama."

Takardar Dongba na da kyau, kuma idan aka hada takardar Dongba da littafin Dongba da kalmomin Dongba, za a samu wata takardar da ke da al'adu na musamman da aka sa ta cikin jerin sunayen abubuwan da aka gada daga kaka da kakaninmu, kuma sun samu karbuwa daga masu yawon shakatawa, sa'an nan ana bukatar wannan takardar ruwa a jallo.

Shugaban kwalejin nazarin al'adun Dongba da ke birnin Li Jiang Zhao Shihong ya ce, da ma, al'ummar Dongba sun yi takardar Dongba don rubuta littafi, amma yanzu, al'ummar na yin wannan takarda don neman moriyar tattalin arziki, sabo da haka, jama'a na dora muhimmanci game da wannan tsohuwar takarda, amma sabo da bambancin fasahar yin takardar, ingancin takardar Dongba da aka sayar a kasuwa ya sha bamban sosai, kuma wannan ya kawo babbar illa ga kiyaye da gadar wannan takarda, da al'adunta.

Game da dan kabilar Dongba mai suna He Zhiguo da He Zhihong wadanda ke da fasahohin yin takardar Dongba, yanzu suna cikin mawuyancin yanayi, He Zhiguo ya ce,

"Yanzu, sabo da masana'antu da dama sun durkushe, ba a iya yin takardar, kuma ba mu kammu ba ma yin takardar ba."

Amma duk da haka, He Yonghong ya ce, ba zai daina yin takardar ba. Ya ce,

"Idan ni ban iya yin takarda ba, zan koyar wa yarana, don su gada daga wannan zuwa zuriya zuwa zuriyoyi masu zuwa, tun da kuma ba za a samu kudi ba, dole ne a gaje wannan fasaha.

"A gidan ibada na Beiyue, a karkashin inuwar itace, yara 'yan kabilar Dongba suna taka rawar da suka saba yi yayin da suke addu'a, kuma malamansu sun gasa balangu, haka kuma, a wani wurin da ke dab da wannan gidan ibada, akwai wani shahararren wurin yawon shakatawa, kuma an samu masu yawon shakatawa da yawa a ko wace rana dake kawo ziyara, kuma ina fatan bayan shekaru dubun dubanta masu zuwa, yara da ke garin da ake yin takardar Dongba, za su ci gaba da kasance ainihin al'ummar Dongba.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na "Asalin takardun kasar Sin" a babi na karshe wato takardar Dongba, mun gode muku da kuka dora muhimmanci sosai kan shirye-shiryenmu, idan kuna so kara sanin abubuwan da suka shafi asalin takardu, kuna iya shiga shafinmu na Internet www.hausa.cri.cn.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China