in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana jin kamshin gora daga takardar Yuanshu
2011-10-14 18:47:02 cri
Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, muna muku lale marhabin a cikin shirin musamman na yau na "Asalin takardu a kasar Sin". Ni ce Salamatu Sabo. A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da gabatar muku da wani bayani mai lakabi: "Ana jin kamshin gora daga wata takardar Yuanshu".

Jama'a masu karatu, birnin Fuyang na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin yana dab da kogin Fuchun. Jama'ar wurin sun fi son shuka itatuwan gora sakamakon isashen ruwan sama da a kan yi a wurin. Lokacin da ake tafiya kan hanyoyin dake kan duwatsu, aka wuce gororin da aka shuka. Sabo da haka, ake kiran birnin Fuyang gari na yin takardu. A cikin shirinmu na yau za mu bayyana muku yadda ake yin takardun Yuanshu a wannan wuri.

"Zakarun da suka ci jarrabawa a babban birnin kasar su kan yi amfani da takardun Yuanshu lokacin da suke zana jarrabawa." Jama'a masu karatu, ka san mene ne ma'anar wannan jimla? A da, daliban kasar Sin su kan nemi mukamansu a hukumomin gwamnati ta hanyar rubuta jarrabawar da aka shirya musu. A hakika dai, lokacin da suke zana jarrabawa, su kan yi amfani da takardun Yuanshu. Sabo da haka, an iya gane cewa, a wancan lokaci, an fi son yin amfani da takardun Yuanshu.

Amma, ina bambanci tsakanin takardun Yuanshu da takardun da muka gabatar muku a cikin shirinmu na baya? Jama'a masu karatu, mun sani, an fi son yin amfani da totuwan katako, ko na karan shinkafa ko na alkama wajen yin takarda, amma ana yin takardun Yuanshu ne da totuwan karan gorori irin na feshi. Sakamakon haka, ana samar da takardu masu haske, kuma masu taushi sosai, har ma ana iya jin kamshin gororin feshin. A shekarar 2006, gwamnatin kasar Sin ta tabbatar da cewa, dole ne a kare fasahar yin takardun Yuanshu da totuwan karan gororin feshi.

A watan Mayu na wannan shekara, lokacin da wakilan gidan rediyon CRI suka isa birnin Fuyang, an soma shiga lokacin zafi a wurin. Bayan an yi ruwan sama, gorori sun yi saurin girma. Lokacin da wakilanmu suke yawo a cikin gandun daji na gorori, sun ga dimbin gororin feshi a ko ina.

Bisa littafin tarihin da aka rubuta, an ce, yau shekaru aru aru da suka gabata, aka soma yin amfani da gororin feshi wajen yin takardun da ake kira "takardun gora". Yau fiye da shekaru dubu 1 da suka gabata, wato, lokacin da kasar Sin take karkashin daular Song ta arewa, an zabi takardun Yuanshu da suka zama takardun da sarakunan daular suke amfani da shi. Sabo da haka, wannan takardun Yuanshu ya zama takardun da hukumomin daular suka yi amfani domin gabatar da bayanai ga sarki, ko zana jarrabawa domin daukar jami'ai.

A birnin Fuyang, ba ma kawai kowane iyali kan iya yin takardu da totuwan gora a tarihi ba, yanzu haka akwai kananan masana'antu da yawa da suke yin takardun gora. Dattijo Zhuang Fuquan mai kimanin shekaru 55 da haihuwa, ya girma a kauye, kuma shi da kakanni da kakaninsa duk sun iya yin takardun gora. A lokacin da ya kai shekaru 15 da haihuwa, ya fara koyon fasahar yin takardu da gora a matsayin sana'arsa. A cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, ya yi kokari sosai wajen koyon fasahar, kuma yanzu ya kware sosai wajen yin takardu da totuwan gororin feshi. A shekarar 2007, an zabi dattijo Zhuang Fuquan a matsayin kwararren da ya gaji wannan fasaha don koyar da fasahar yin takardu da totuwan gororin feshi.

Dattijo Zhuang Fuquan ya bayyana cewa, daga matakin farko na zaben gororin feshi zuwa matakin karshe na samar da kowane takarda, ana bukatar matakai fiye da 70, kuma a kan yi wajen kwanaki 60 ana yinsa. A ganin Zhuang Fuquan, mataki mafi wuya daga cikin matakan yin takarda shi ne "samun takarda". A lokacin da aka kai wannan mataki, dole ne a yi ta motsa totuwan gora da ruwa domin samun daidaito tsakanin totuwan gora da ruwa. Sannan ma'aikata su yi amfani da wani kayan aiki domin kokarin samun totuwan gora a kansa, sannan fa za a iya samun wata takarda mai inganci. Game da wannan fasaha, dattijo Zhuang Fuquan ya ce, "Ana bukatar a kalla shekaru 3 wajen koyon fasahar yin takardu masu inganci. A lokacin da ake tafiyar da matakin 'samun takardu', dole ne an samu daidaito tsakanin hannaye biyu, sannan a zura ido kan totuwan gora da aka samu daga ruwa. Idan ba a iya samun karfin daidaito ba, shi ke nan, ba za a iya samun takardu masu inganci ba."

Wasu mutane su kan dauka cewa, fasahar samun takardu ba ta da wuya, amma a hakika dai, ba kowane mutum ke iya mallakar wannan fasahar ba. Kuma idan ma'aikaci ba kakkarfa ba ne, a gaskiya, ba zai iya kammala wannan aikin ba. Mr. Guo Xianrun, wanda ya kai shekaru 30 ko fiye da haihuwa ya riga ya yi wannan aiki har na tsawon shekaru 5. Sabo da ya kan yi amfani da hannayensa a cikin ruwa, don haka, fatun hannayensa ya ji rauni sosai. Lokacin da yake tabo magana kan wahalolin da ya sha, ya fadi cewa, "Na kan tashi daga barci wajen karfe 4 ko 5 na kowane safe. Sannan na yi aiki har karfe 8 na dare. A cikin wannan yini daya, yawan takardun da na kan iya yi ya kai wajen dubu 1. A lokacin sanyi, hannayena su kan kumbura, har ma su yi miki. Sai a lokacin zafi, su kan sami sauki."

Haka kuma, a kan sha wahala sosai a wani mataki na daban wajen yin takardun Yuanshu, wato matakin busar da takardu. A lokacin zafi, a cikin dakin busar da takardu, yawan zafi ya kan kai digiri na 80 zuwa 100 bisa na celsius, kuma ma'aikata su kan yi aiki a cikin daki har na tsawo sa'o'i takwas.

A cikin wannan karamar ma'aikatar yin takardun Yuanshu, yawan ma'aikata bai wuce 20 ba, kuma yawan takardun da suke samarwa a kowace rana ya kan kai wajen dubu 1. Mazauna wurin sun ce, yanzu matasa ba su son koyon fasahar yin takarda sabo da ba ma kawai a kan sha wahala sosai ba, har ma ba kudin shiga ba ya da yawa. Sakamakon haka, yanzu ba wanda yake son gadan irin wannan fasahar gargajiya ta yin takardun Yuanshu.

Dattijo Zhuang Fuquan, yanzu shi ne shugaban wani kamfanin samar da takardu a birnin Fuyang, inda ake amfani da injuna wajen samar da takardu. Kuma yana fitar da kayayyakinsa zuwa kasashen Japan da Koriya ta kudu. Amma har yanzu wannan dattijo wanda ya kware sosai wajen yin takardun Yuanshu ta hanyar gargajiya yana kaunar fasahar gargajiya. Sabo da haka, a cikin kamfaninsa na zamani, akwai injunan gargajiya na yin takardun Yuanshu. Dattijo Zhuang ya ce, yana son gina wani dakin nune-nunen fasahohin gargajiya na yin takardu a garinsa, inda masu yawon bude ido za su iya ziyarta. Game da wannan shiri, dattijo Zhuang ya bayyana cewa, "Na fara sana'ar yin takarda tun lokacin da nake karami. Ban taba yin watsi da wannan sana'a ba. Yanzu ina son sake gabatar da matakai 72 na yin takardun Yuanshu domin farfado da fasahar gargajiya ta yin takarda. Sannan jama'a za su iya kawo ziyara domin fahimtar wannan fasaha. Ko da yake za mu sha wahala, amma ina cike da imani ."

A yankin Fuyang, ba ma kawai dattijo Zhuang Fuquan ke kokarin kare fasahar gargajiya ta yin takardun Yuanshu ba, har ma da sauran mutane da yawa suke kokarin yin haka. Wani dattijo, wato Mr. Li Shaojun wanda ya kai shekaru 63 da haihuwa yana daya daga cikinsu. Ya yi amfani da shekaru 16 yana ziyartar manya da kananan dakunan yin takardar Yuanshu, inda ya tattara dimbin bayanai kan yadda ake yin takarda, har ma ya rubuta wani littafi mai suna "Takardar Gora ta Fuyang", mai kunshe da kalmomi dubu dari 1 ko fiye tare da hotuna fiye da dari 5. Lokacin da ya bayyana dalilin da ya sa ya rubuta wannan littafi, dattijo Li Shaojun ya ce, "Ina da sha'awa sosai kan wannan fasahar gargajiya, ina son rubuta su. Na duba littattafai da yawa, amma yawan littattafan dake kunshe da wannan fasahar gargajiya ya yi kadan. Mu Sinawa ne mun kirkiro wannan fasahar yin takarda, idan mun yi watsi da ita, zai zama abin kunya a gare mu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China