in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar Lian-shi-zhi
2011-10-14 18:46:08 cri
Gundumar Yanshan, wata karamar gunduma ce a lardin Jiangxi, amma ta taka muhimmiyar rawa a tarihin kasar Sin na sarrafa takarda. A zamanin da, a nan kasar Sin, littattafai da yawa an wallafa su ne ta hanyar amfani da irin wannan takarda.

Zhang Shikang, wanda ya yi bayeyeniyar fasahar sarrafa takardar Lian-shi-zhi daga zuriya zuwa wata ya fara koyon fasahar sarrafa takardar daga wajen mahaifinsa a lokacin da yake karami. Kakani-kakaninsa sun kaddamar da aikin sarrafa takardar Lian-shi-zhi tun can da. A lokacin da yake tunawa da abubuwan da suka faru a baya, mista Zhang ya gaya mana cewa,

"A lokacin hunturu, ana sanyi kwarai da gaske. Amma tilas ne mu gudanar da wasu matakan sarrafa takardar Lian-shi-zhi a cikin ruwa. A wasu lokuta, matukar sanyi ya kan tilasta mu saka hannayenmu cikin ruwa mai zafi domin dumama su kadan. In mun yi yini guda muna sarrafa takardar cikin ruwan da ke dauke da sinadarin sarrafa takardar ba tare da kasala ba, to, mu kan ji matukar gajiya, musamman ma kugunmu. Dole ne mu kwanta da hankalinmu a lokacin da muke sarrafa takardar. In an taba takardar, ta kan lalace, shi ke nan, abun da ka yi ya zama banza."

A kan sarrafa takardar Lian-shi-zhi ne da hannu kawai, aikin da ke dogaro da fasahar da masu sarrafa takardar suke mallaka matuka, wadanda suka kyautata fasahar daga zuriya zuwa zuriya. Da wuya a sarrafa takardar bisa fasahar zamani.

In an kwatanta ta da wasu nau'o'in takardu masu dogon tarihi, takardar Lian-shi-zhi ta fi yin fintikau a fannonin hana ruwa shiga, da jure zafi, sa'an nan kuma ana iya adana ta cikin dogon lokaci. Shi Lixiong, wani kwararre masanin takardar Lian-shi-zhi ya yi karin bayani da cewa,

"Sakamakon faranta ta yadda ya kamata, takardar Lian-shi-zhi na iya jure zafi, abubuwan da aka rubuta a kanta wato dai ba za su kode ba cikin dogon lokaci, haka kuma, ana iya adana takardar na tsawon lokaci. Tawadar da ake amfani da ita tana iya kama takardar Lian-shi-zhi cikin sauki. Sakamakon adana takardar Lian-shi-zhi na tsawon lokaci, ya sa ana kiranta takarda mai tsawon tarihi na shekaru dubu guda."

A tarihin kasar Sin, dimbin shahararrun littattafai da aka wallafa su ta hanyar amfani da takardar Lian-shi-zhi suna da yawan gaske. Ban da wannan kuma, zane-zane, rubutattun wakoki da wakokin gargajiyar kasar Sin masu tsawon tarihin shekaru daruruwa, har ma dubu dubai suna iya ci gaba da kasancewa a duniya sakamakon rubuta su kan takardar nan ta Lian-shi-zhi. Mista Shi Lixiong ya kara da cewa,

"Yau shekaru misalin dari 8 da suka wuce, wato a zamanin daular Song da Yuan a kasar Sin, musamman ma bayan an shiga zamanin daular Ming, wato yau shekaru misalin dari 6 da suka gabata, takardar Lian-shi-zhi ta kai matakin koli a tarihinta. A wancan lokaci, ana amfani da ita a fadar sarakuna."

Sabili da haka ne takardar Lian-shi-zhi ta dade tana taka muhimmiyar rawa a fannonin abun da aka gada da kuma yayyata al'adun al'ummar Sin. Har ma a shekarun 1980, a kan yi amfani da takardar wajen wallafa littattafai ta hanyar da Sinawa suka saba bi tun zamanin da. Bugu da kari kuma, a kan sayar da takardar Lian-shi-zhi zuwa kasashen Japan da Korea ta Kudu da wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya.

Amma duk da haka, sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, makudan kudaden da a kan kashe wajen sarrafawa da kuma sarkakkiyar fasahar sarrafawa sun hana takardar Lian-shi-zhi ta biya bukatun kasuwanni a kwana a tashi. Ya zuwa karshen shekarun 1980, an daina sarrafa takardar Lian-shi-zhi a gundumar ta Yanshan. Masu sarrafa takardar da yawa kamar mista Zhang Shikang sun rasa aikin yi, ba su san abun da za su yi a nan gaba ba. Amma a shekara ta 2006, halin da takardar Lian-shi-zhi take ciki ya samu sabon sauyi. A wannan shekara, kasar Sin ta tanadi fasahar sarrafa takardar Lian-shi-zhi cikin takardar sunayen abubuwan tarihi na al'adu da ba na kaya ba a rukuni na farko. Baya ga haka kuma, a shekara ta 2008, a yayin bikin bude gasar wasannin Olympic a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, an gwada yadda Sinawa suke sarrafa takarda ta hanyar da suka saba bi tun fil azal, lamarin da ya sanya mista Zhang Shikang ya ji farin ciki matuka. A ganinsa, ga alama akwai damar farfado da aikin sarrafa takardar Lian-shi-zhi, har ma ya yi shirin koyar wa yaransa fasahar.

A daidai wannan lokaci, wasu sun gano darajar da takardar Lian-shi-zhi take da ita. A shekara ta 2009, mista Yan Zhonghua ya zuba kudin Sin yuan miliyan 2 ko fiye kan maido da aikin sarrafa takardar Lian-shi-zhi. A matsayin wanda aka haife shi a gundumar Yanshan, ko da yake mista Yan Zhonghua, wanda shi ne shugaban wani kamfani, bai san fasahar sarrafa takardar sosai ba, amma ya fahimci darajar da takardar take da ita kwarai da gaske. Mista Yan ya nuna cewa,

"A ganina, abin da nake yi na da ma'ana. Takardar Lian-shi-zhi an samu asalinta ne a gundumarmu ta Yanshan. In mu mazauna Yanshan muna iya yin bayeyeniyarta daga zuriya zuwa wata, to, lamarin zai ba da babban tasiri kan fasahar, da ma al'adun gargajiyar kasarmu."

A kokarin yin bayeyeniyar abun tarihi na al'adu da ba na kaya ba yadda ya kamata da kuma sake sarrafa takardun Lian-shi-zhi masu inganci, mista Yan ya aika da ma'aikatansa zuwa wurare da dama domin ziyartar masu fasahar sarrafa takardar. Ba shakka mista Zhang Shikang ya jawo hankalin mista Yan. Da mista Zhang Shikang ya samu cewa, zai samu damar ci gaba da sarrafa takardar Lian-shi-zhi, sai ya bar aikinsa a wani wuri da ke kawo masa kudin shiga da yawa, ya koma garinsa ba tare da yin wata-wata ba, ya shiga aikin da mista Yan ke gudanarwa. A game da kudurin da ya tsai da, mista Zhang bai yi da-na-sani ko kadan ba, yana mai cewar,

"Da ganin gwamnatin kasarmu ta sa ran alheri kan bunkasuwar takardar Lian-shi-zhi, tare da mai da hankali kan sarrafa takardar. Ta haka ina da karfin zuciya wajen ci gaba da aikina a gundumarmu. Haka zalika yayyata fasahar sarrafa takardar da kuma koyar da matasa, domin abubuwa ne masu kyau."

Yanzu haka an sake sarrafa takardun Lian-shi-zhi, wanda aka dakatar da sarrafawa har na tsawon shekaru 20 ko fiye. Sa'an nan kuma, ana ta kyautata fasahar, lamarin da ya sanya ake ta kyautata ingancin takardun. Sabili da haka takardun na kara samun lale marhabi. Mista Yan ya yi nuni da cewa, tabbatar da takardar Lian-shi-zhi a matsayin takardar da aka yi amfani da ita wajen wallafa littattafai ta hanyar gargajiya na daya daga cikin manufofinsa, inda ya ce,

"Tun daga shekarar bara, kamfaninmu ya fara hada kai da cibiyar nazarin fasahar sarrafa takarda ta Jiangxi domin kyautata ingancin takardar Lian-shi-zhi cikin sauri bisa ga hada fasahar gargajiya da ta zamani tare. Yanzu muna kokarin fito da ka'idodji kan sarrafa takardar Lian-shi-zhi."

Bayan jure wahalhalu da dama, takardar Lian-shi-zhi ta samu kyakkyawar makoma. Shi Lixiong, kwararre ne kan ilmin takardar ya yi bayani da cewa,

"Al'adun al'ummar Sin mai dogon tarihi, tilas ne a yi bayeyeniyar wasu al'adun gargajiya bisa ga kasancewar wasu abubuwa. A bisa wannan hali, takardar Lian-shi-zhi za ta ci gaba da kasancewa a duniya tare da yin bayeyeniyar al'adun gargajiyar kasar Sin daga zuriya zuwa wata." (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China