in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shiga Fang-ma-tan don binciken asalin takarda
2011-10-14 18:43:46 cri
A watan Maris na shekarar 1986, cikin kungurmin daji da ke dab da birnin Tian'shui na lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, an shafe kwanaki da dama ana ambaliyar ruwa, lamarin da ya haddasa zabtarewar kasa. Ruwa da laka sun kwarara zuwa gindin dutse, inda gidajen ma'aikata masu sare itatuwa suke. Bayan da ruwa ya yi sauki, ma'aikatan sun fara tsabtace filayen da ke kewayen gidajensu, Abin alajabi, suna cikin aikin, sai suka gano wata takarda wadda aka samar da ita shekaru dubu 2 da suka wuce a cikin laka. Takardar da aka lakaba mata suna 'takardar Fang-ma-tan', wato sunan wurin da aka gano ta ke nan, takardar da ta kasance mafi shekaru cikin tsoffin takardun da aka taba ganowa a duniya.

Fang-ma-tan, ma'anar wannan suna shi ne filin ciyayi da ake kiwon dawaki. Yanayin wurin na da kyau, kana akwai koguna da filayen ciyayi a can, don haka tun fil azal an fara yin amfani da wurin wajen kiwon dawaki. Tun daga shekaru 202 kafin haihuwar annabi Isa alaihissalan, har zuwa shekarar 907, wurin ya kasance wata babbar cibiyar zirga-zirga kan hanyar siliki wadda a lokacin ta hada kasar Sin, Persia, Saudi Arabia, da ma kasashen Turai. Tarihin wurin na tsawon shekaru dubu ya sa ake samun kayan tarihi mai daraja a Fang-ma-tan. Bayan ambaliyar ruwa da ta abku a shekarar 1986, wasu ma'aikatan wurin sun gano alamar wani tsohon kabari daga nan aka fara fahimtar tarihin wurin.

Mista Mao Huimin, wani ma'aikaci na hukumar al'adu ta birnin Tian'shui, ya bayyana cewa,

"Bayan da ma'aikata masu kula da yankin itatuwa suka tsabtace wurin, an samu bayyanar wani rami, inda aka gano kwararar ruwa mai launin fari-fari. Nan take wani ma'aikaci ya sanya hannu cikin ramin, ya diba wani daurin tsinkayen gora, abin da aka yi amfani da shi wajen rubutu a da can a kasar Sin. Don haka, bayan kwana daya sai aka sanar da hukumar al'adu labarin. Sa'an nan mun zo karbar wadannan kayayyakin tarihi, mun kai su hukumarmu domin a kare su. Daga bisani hukumar al'adu ta lardinmu ta tura wasu kwararru zuwa wajenmu domin su tsara kayayyakin."

Kwararrun sun tabbatar da cewa, tsinkayen da aka rubuta bakake a kansu, hade da wata taswirar da aka sassaka kan ice, wadanda aka gano a Fang-ma-tan, dukkansu sun kasance kayayyakin tarihi da aka kera su a shekaru 400 zuwa 200 kafin haihuwar annabi Isa. Don haka, hukumar kiyaye kayan tarihi ta lardin Gansu ta tura ma'aikata zuwa Fang-ma-tan don binciken kayayyakin tarihi a wurin, inda aka gano tsoffin kaburbura fiye da 100 . Mista He Shuang-quan, ya kasance daya daga cikin kwararru masu kula da aikin gano kayayyakin tarihi a wurin. Ya bayyana wa wakilin CRI cewa, bayan da aka bude wani tsohon kabarin da aka gina shi shekaru 200 kafin haihuwar annabi Isa, an gano wata takarda, wadda aka tabbatar da cewa ta kasance takarda mafi shekaru da aka taba ganowa. Mista He ya maimaita yadda aka gano takardar,

"Lokacin da aka bude kabarin, an ga takardar a kan kirjin gawar da ke kabarin, yanayinta tamkar kyallen siliki. Daga baya an tsabtace abin, an sanya shi karkashin madubin kimiyya, sa'an nan aka gano cewa hakika dai takarda ce ba siliki ba, wadda aka yi da bawon itace."

Takardu ba su da kauri, don haka za su yi saukin lalacewa. Shi ya sa aka yi mamakin yadda takardar ta kai yanzu a binne karkashin kasa har shekaru fiye da dubu 1? Wannan ce ta sanya bisa jagorancin Mista He, wakilin CRI ya je cibiyar binciken kayan tarihi ta lardin Gansu, inda ya gane ma idanunsa wannan takarda mai daraja.

Wakilinmu ya bayyana cewa, ya ga wani akwati na gilashi, dauke da wata takardar da fadinta bai wuce na hannu ba. Abin mamaki shi ne, duk da cewa an samar da takardar shekaru 2000 da suka gabata, amma babu bambanci sosai tsakanin takardar da takardun zamani, sai dai takardar ta tsufa har ma ta fara lalacewa. a jikin takardar an zana hotunan duwatsu, koguna, da hanyoyi. Kwararru sun kwatanta takardar da kayayyakin tarihin da aka gano a sauran wasu kaburbura, sa'an nan sun tabbatar da cewa, takardar ta kasance wata taswirar yankin da ke kewayen Fang-ma tan. Wajen amfani da wannan taswirar, Mista He ya yi karin bayani,

"Mun yi bincike kan taswirar, sa'an nan mun gano cewa ta kasance taswira ta daular Qin. Wasu bayanan da aka rubuta kan tsinkayen gora sun ce, wasu mutane masu kiwon dawakin sarkin daular Qin sun taba zama a wurin. Kana bayan mun yi bincike kan tsarin kaburburan, mun fara gano cewa, wurin ya kasance wani sasanin soja a lokacin, kana masu kaburburan sun kasance mutanen da aka sanya su zama a can musamman ma domin kiwon dawaki."

Mista He ya kara da cewa, ta la'akari da yadda aka tsara taswirar cikin tsanaki, ba zai yiwu ba ta zama karkashin mallakar farar hula. Dan haka, ana tsammanin cewa, mai yiwuwa ne mai taswirar ya kasance wani mutum mai mukami a cikin ayarin masu kiwon dawaki.

Mista He ya ci gaba da cewa, a wancan lokaci wani mutum mai sanye da tufafi na da ya hawa doki, dake rike da taswira a hannu, wanda ya jagoranci sojoji wajen kiwon dawaki da tsaron iyakar kasa a cikin kungurmin daji. Taswirar ta sa an fahimci wannan tarihi, ban da haka kuma yadda aka yi ta da bawan itace ya samar da ma'ana sosai. Kamar yadda kwararru suka bayyana cewa, takardar da aka gano a Fang-ma-tan ta kasance taswira mafi tarihi da aka gano wadda aka yi ta da takarda, ban da haka kuma ta kasance takarda mafi tarihi a duniya. Dagane da batun, farfesa Yong Jichun, wani shehun malami na jami'ar horar da malamai ta birnin Tian'shui, ya bayyana cewa,

"Akwai bambanci sosai tsakanin taswirar da aka saka kan ice da wadda aka zana kan takarda. Domin takarda za a iya tafiya da ita. Bayan da aka samar da takarda, a matsayin wani abin da ake rubutu a kai, tana da araha, wannan ya sa ta samar da sauki wajen tafiye-tafiye da ita, haka kuma ta taimakawa aikin yada al'adu, da wayar da kan jama'a, gami da ciyar da al'adun dan Adam gaba."

A kasar Sin,bayan da aka fara samar da tarkardar Fang-ma-tan a shekaru 200 kafin haihuwar annabi Isa, an kara shafe shekaru fiye da dari ana kokarin yada fasahar sarrafa takarda kafin ta gama gari tare da maye gurbin tsinkayen gora, itace, siliki, da dai sauran kayayyakin rubutu wadanda aka taba amfani da su a da. Zuwa lokacin daular Tang a kasar Sin, wato shekarar 800, mutanen Persia sun fara isar da fasahar kera takarda zuwa daular Larabawa, daga bisani aka gabatar da ita ga yammacin Asiya da arewacin Afirka, ta hakan takarda ta gama gari inda ta zamanto abin rubutu da ake amfani da shi a duk duniya. Wang Ruobing, wani marubuci da aka haife shi a birnin Tian'shui, ya bayyana ma'ana a bangaren tarihi ta takardar Fang-ma-tan da cewa,

"A da mun san cewa, takarda mafi tarihi a kasar Sin ita ce takardar Cai'hou da aka samar da ita a lokacin daular Han ta gabas, amma takardar Fang-ma-tan ta fi ta har shekaru 300. Duk da cewa ba a gano wata cikakkiyar takarda a Fang-ma-tan ba, amma kashin takardar da aka gano ya tabbatar da cewa, a lokacin daular Han ta yamma, wato shekaru 200 kafin haihuwar annabi Isa, an riga an samar da takardar da aka yi ta da bawon itace a kasar Sin. Kafin a fara sarrafa takarda, mutanen yammacin duniya sun yi amfani da fatar tunkiya wajen rubutu, yayin da Sinawa suke amfani da tagulla, kashin dabbobi, gora da itace wajen rubutu. A lokacin ba a iya yada al'adun dan Adam cikin sauri ba. Shi ya sa, bullowar takardar Fang-ma-tan a kasar Sin ta kasance wani al'amari mai muhimmanci a tarihin bil Adama." (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China