in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar Baqiao mai dadadden tarihi
2011-10-14 18:42:41 cri
A zamanin yanzu, kayayyakin lantarki na ta kara samun karbuwa a duniya, duk da haka, takardu suna ci gaba da zama kayan rubutu ga akasarinmu, har ma ana daukarta a matsayin daya daga cikin manyan kirkire-kirkire hudu a zamanin gargajiyar kasar Sin, wato baya ga compass, wato na'urar da ke nuna alkibla, da albarushi da kuma dab'i. Sakamakon wannan muhimmiyar kirkira, Bil Adam sun samu damar kara bunkasa al'adunsu. To, a shirinmu na yau, za mu kawo muku labarin takardar Baqiao, takardar da ta fi dadadden tarihi a nan kasar Sin.

Bayanan tarihin kasar Sin sun shaida cewa, a shekarar 105, wato zamanin daular gargajiya da ake kira Donghan, akwai wani jami'i mai suna Cai Lun da ya kirkiro fasahar yin takardu, jami'in da daga baya ya roki sarkin daular da ya amince da yada fasahar a duk fadin kasar, kuma sarkin ya amince da rokonsa, abin da ya sa aka dauki wannan jami'i mai suna Cai Lun a matsayin wanda ya kirkiro fasahar yin takardu a tarihin kasar Sin. Amma ya zuwa shekarun 1950, an samu karin haske kan wannan fasaha.

A ranar 8 ga watan Mayun shekarar 1957, wani mai yin tubali tare da wasu abokan aikinsu a masana'antarsu da ke unguwar Baqiao a bayan garin Xi'an, hedkwatar lardin Shanxi da ke arewa maso yammacin kasar Sin, sun gano wani kabarin da ke da tsawon shekaru sama da 2000 a yayin da suke kokarin hako kasa don yin tubali, inda suka gano wasu kayayyakin tarihi, ciki har da wani madubi da ma wata wuka. A kan madubin, akwai kuma wani dan karamin abu tamkar yadin Linen. Nan da nan sai suka nemi ma'aikatan da ke nazarin kayayyakin tarihi da su zo su duba. Malam Zhou Zhiqiang, wanda ke da shekaru sama da 70 a duniya, ya tuna da cewa, "A lokacin, mun gano wani madubi, kuma an rufe madubin da wani abu tamkar takarda. Wani ya bugo mana waya ya ce, wannan takarda har ta fi irin takardar da Cai Lun ya kirkiro tarihi."

Malam Zhou Zhiqiang ya tuna da cewa, a lokacin, wani manazarcin kayayyakin tarihi daga gidan nune-nunen kayayyakin tarihi a lardin Shanxi ya cire abin daga madubin, kuma nazarin da aka yi a kansa ya shaida cewa, wannan abin yana daukar sigar takardu. An gano shi ne a unguwar Baqiao, shi ya sa aka sanya masa suna takardar Baqiao.

Takardar Baqiao ta kasance rawaya, kuma tana da taushi da karfi. Bisa nazarin da aka yi, an gano tarin zaren linen a ciki, kuma bayan da aka yi nazari a kan zaruruwan, an gano yadda aka yayyanka su da tafasa su da kuma daka su har suka zama takarda, sai dai kawai fasahar ta kasance mai sauki sosai. Duk da haka, wasu masana sun dauki takardar Baqiao a matsayin takardar da ta fi tsawon tarihi a duniya, abin da ya sanya tarihin yin takarda a kasar Sin har ma a duniya ya zuwa karni na farko ko biyu kafin haihuwar Annabi Isa A.S.

Yanzu haka an adana takardar a gidan nune-nunen kayayyakin tarihi na lardin Shanxi, inda aka fara nuna ta ga al'umma yau da shekaru hudu da suka wuce.

Kamar yadda muka bayyana muku a baya, kafin a gano takardar Baqiao, an dauki Cai Lun a zamanin daular gargajiya ta Donghan a matsayin wanda ya kirkiro fasahar yin takarda, amma yadda aka gano takardar Baqiao ya sa dole a sake yin nazari a kan asalin takarda. Sabo da haka, takardar Baqiao a lokacin da aka gano ta ta jawo hankalin bangarori daban daban da kuma haifar da ka-ce-na-ce a kanta. Amma sabo da ta dade, ga shi kuma babu bayanai da yawa a kanta, shi ya sa har yanzu akwai mutane da yawa da ke shakkar ko takardar Baqiao takarda ce ta gaske. Yang Jin, wadda ke kula da harkokin nune-nune a gidan nune-nunen kayayyakin tarihi a lardin Shanxi ta bayyana mana cewa, "Duk da cewa an yi ta cece-ku-ce a kan takardar Baqiao tun farkon lokacin da aka gano ta, amma daukacin masana ta bangaren nazarin takardu suna ganin cewa, takardar ta kasance mafi tsawon tarihi a kasar Sin har ma a duniya baki daya. Sai dai kawai malam Cai Lun ya kara kyautata fasahar yin takarda tare da yada fasahar."

A gidan nune-nunen kayayyakin tarihi na lardin Shanxi, mun samu damar yin hira da Nerson Willy, wani jagoran masu yawon bude ido daga kasar Denmark, wanda ya ce, ko takardar Baqiao ta kasance asalin takardu a duniya ko a'a ba abu ne da ke daukar hankalinsa ba, sai dai kawai yana son bayyana wa jama'a fasahar yin takarda da aka kirkiro a kasar Sin da kuma muhimmancinta. Kamar yadda ya ce mana, "Ina ganin takarda na daya daga cikin muhimman kirkire-kirkire na 'yan Adam. Kasancewata jagoran masu yawon bude ido, ko da yake ba ni da masaniya sosai a kan takardar Baqiao, amma ina son bayyana wa jama'a fasahar yin takarda da aka kirkiro a kasar Sin da ma takardar Baqiao. Sabo da a ganina, takardar ta nuna tamkar asalin takadar da muke amfani da ita yanzu. Bayan haka, na san al'ummar kasar Sin a zamanin gargajiya, su kan yi rubutu a kan iccen gora, a maimakon takarda."

Kowa na da ra'ayinsa a kan tarihin takardar Baqiao. Zhou Lingjie, wata daliba ce da ta zagaya gidan nune-nunen kayayyakin tarihi na lardin Shanxi, inda ta bayyana mana ra'ayinta. Kamar yadda muka ji ta bakinta, "A ganina, lardin Shanxi wuri ne da ke da dadadden tarihi, sabo da haka, muna iya cewa, takardar Baqiao ta shaida tarihin ci gaban fasahar yin takarda. Bisa ga yadda na dube ta, ina ganin ta fi kama da takarda."

Masana sun ce, idan aka nazarci takardar Baqiao ta madubin likita, ana iya gano zaruruwan tsire-tsire a ciki, shi ya sa, muna iya cewa, takarda ce da aka yi da tsire-tsire. Babu shakka, takardar da Cai Lun ya yi bayan shekaru 200 ta fi ingantuwa, kuma masana sun yi zaton cewa, a zamanin daular gargajiya ta Xihan, takardar Baqiao ba ta samu karbuwa sosai ba, sabo da a lokacin, an fi yin amfani da siliki da gora wajen rubutu, a maimakon takarda. Sai dai kawai, kamar yadda Yang Jin, wadda ke kula da harkokin nune-nune a gidan nune-nunen kayan tarihi na lardin Shanxi ta ce, a zamanin daular gargajiya ta Xihan, an samu ci gaban tattalin arziki da al'adu, shi ya sa aka kara bukatar abubuwan rubutu da aka iya saukin tafiya da su, wadanda kuma aka iya kera su da yawa.

Ya yiwu za a ci gaba da ka-ce-na-ce a game da takardar Baqiao, amma wani abin da muke iya tabbatarwa shi ne, hanyar siliki da ta shahara a duniya ta bullo ne a zamanin daular Xihan, kuma bisa ga wannan hanyar gargajiya, fasahar yin takarda da aka kirkiro a kasar Sin ta samu damar yaduwa zuwa yankunan arewa maso yammaci. Bayan tsawon shekaru kimanin dubu daya, fasahar yin takarda ta yadu zuwa Farisa da ma sauran kasashen Larabawa, kuma a shekarar 1150, an samu masana'antar kera takarda ta farko a Turai. A yayin ci gaban zamani, fasahar takarda da aka kirkiro a kasar Sin ta yi ta kara ba da taimakonta ga wayin kan al'ummar duniya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China