Wannan wuri an nuna hikimomi tare da zaruntaka wurin ginashi an ginana sojojin fama feye da dubu a cikin wannan katon kabari a gaskiya ba zan iya bayyana ma mai sauraro yadda wannan
uriyakeba abin sai dai wanda ya gani, bayan wannan na fahinci cewa a lokacin da aka gina wannan kabari an rufesu da manyan itatuwa masu karfin gaske an kuma gina wannan kabari da zurfi kuma yana da lunguna daban daban inda a kagina sojoji iri daban daban kamar sojojin sam da na kasa da makamantansu,
hakam baya da wannan sarki ya mutu sai wasu kabilu suka kawo ma wannan wuri hari suka ruguzashi suka kuma kona shi tun a wannan lokacin dakakonashi kusan shekara dubu biyu amma har yanzu akwai sauran hafdin da aka kona wurin baya, bayaga wannan wato har yanzu bakauyen da ya gano wannan wurin yananan da ransa yagano wannan wurine a cikin shekara ta 1974 inda gwamnatin kasar sin ta yi kokarin gyarawan nan wuri yanzu ya zamo wurin yawon shakatawa kuma majalisar dinkin duniya tasashi a cikin wuraren tarihi na duniya wato hukumar UNESCO.
Daga karshe wannan wuri ya burgeni sosai da sosai wannan shine bayanina akan kabarin sojojin tera kuta na kasar sin.
Nine maisauraro,
Bello Abubakar Malam Gero Sokoto,
Nigeria.