in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARATA A WURIN BUKIN NUNE NUNEN KAYAN LAMBU NA BIRNIN XI'AN NA KASAR SIN
2011-09-13 16:54:51 cri
A ranar juma'a 09 ga watan 09 na 2011, na halarci cibiyar nune nunen kayan lambu ta birnin xi'an inda muka halarci wannan gagarumin bukin kayan lambu na duniya, inda na ga abubuwa masu ban sha'wa tare da mamaki, na ga kayan lambu iri daban daban kamar da na kasashen nahiyarmu ta afrika, nahiyar turai, amurka, girka da nahiyar asiya kai harma na kasar sin baki daya.

Mun zagaya lunguna da sako da dama na wannan fili inda muka sadu da mutane daban daban na kasashe na nesa da na kusa , kowanne su suna more idanuwannsu inda ma'aikata ba kama hannun yaro suke aiki bilhakki ana ta daukar mutane a cikin jirgin kasa, na gadina ana zuwa ana komowa da 'yan kallo na kasashe daban daban na duniya, a gaskiya wannan buki ya kai buki ba shakka kasar sin ta bunkasa.

Baya ga haka, na fahimci cewa kasar sin tana da arziki mai yawa domin kuwa kasar sin tana dauke da alumma masu tarin yawa, kuma a halin yanzu mutane na kasashen duniya mafi yawan su suna bukatar zuwa kasar sin domin kasar sin tana da tsaro tana kuma bin tafarkin garkiya tsakanin ta da abokanin hulda na kasashen duniya. Wannan yasa kasar sin ta sami martaba ga idanun duniya, bayan mun dan zagaya mun halarci wani katumemen dakin cin abinci a cikin wannan fili, inda muka ci abinci muka huta.

Bayan wannan sai muka cigaba da ziyarar dakuna dakuna na kasashe daban daban na duniya harma da na kasarmu NIGERIA, inda muka dauki hutuna kuma muka shiga domin ziyara muka taradda kayayyaki irin na mu na nahiyar afrika, abin gwanin ban sha'awa bayan kammala ziyarar wanda na muhimmam wurare sai muka yi harrama dawowa masauki, ba shakka wannan abu ya burge ni sosai kuma ya sa na kara son gidan rediyon cri a cikin rayuwata domin wannan wuri a kwanakin baya ina jin sane a cikin shirin gidan rediyon kasar sin ke gabatarwa a gare mu, to sai ga shi gidan rediyon ya gaiyace ni domin in ganarma idanuwa na wannan bukin, don haka ina godiya ga wannan gidan rediyo na cri musamman sashen hausa da dukkanin ma'aikatansa baki daya na gode na gode.

NINE MAISAURARONKU AKODA YAUSHE,

SHUGABA, BELLO ABUBAKAR MALAM GERO,

SOKOTO STATE<

NIGERA.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China