in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARATA A BIRNIN XI'AN NA KASAR SIN
2011-09-13 16:54:19 cri
Kamar yadda Allah mai komi mai kowa yasa, na sami cikakiyar gayyata daga sashen hausa na gidan rediyon kasar sin, a ranar 07 ga watan 09 na 2011, na shigo jirgin sama daga beijing zuwa birnin xi'an na kasar sin domin cigaba da ziyarce-ziyarcen wuraren tarihi na kasar sin, inda wakilan gidan rediyon kasar sin suka saukar da ni wani katabaren otel mai suna GRAND SOLUXE INTERNATIONAL HOTEL, XI'AN inda suka kula da ni kamar yadda ya kamata.

Bayan na huta, a ranar 08 ga watan 09 na 2011, na samu da mar ziyarar wani babban masallacin birnin xi'an mai da dadanden tarihi a kasar sin wanda aka gina tun cikin shekaru 742 wato tun lokacin daular Tang, wannan masallaci tarihi ya nuna dacewa dauloli da dama, sun yi amfani da shi kamar daular Song, Yuan, Ming da kuma daular Qing. Ba shakka wannan masallaci ya nuna mini cewa kasar sin na daya daga cikin kasashen duniya da musullunci ya fara inda a cikin wannan masallaci za ka ga abubuwa da dama na tarihi na tsawon lokaci tare da abubuwa masutarin yawa na tarihi kamar yadda shugaban wannan masallaci yayi muna bayani a gaskiya wannan abun alfahari ne a gare ni.

Haka ma mun tarad da mutane da dama wadanda suka fito daga kasashe daban daban na duniya sun zo ziyarar wannan wuri tare da ayarinsu, a karkashen ziyararmu a masallacin mun gabatar da sallar laasar a cikin wannan masallaci mai dadadden tarihi na birnin Xi'an na kasar Sin.

Bayan gama sallar laasar sai muka cigaba da shiga cikin garin Xi'an wato tsohuwar hedkwatar kasar Sin mai yawan al'umma, inda muka sadu da kabilu daban daban wadanda suka tarbe mu da fara, wasu daga cikinsu har ma suka dauki hotuna da mu. Wannan ya nuna mini cewa Sinawa mutane ne masu son al'umma tare da karrama su, bayan wannan sai muka garzaya wani katafaren dakin cin abinci, inda aka wumurci masu dakin abincin da su kawo muna abinci kowane iri muke bukata to daga nan fa sai nasa aka kawo mini wani abinci mai suna YANGROU PAOMO. Wannan abinci an yi shi ne da fulawa mai kama da burodin Larabawa tare da romo mai dankare dadi muka ci sannan muka koma masauki.

To a gaskiya wannan ziyara ta kara mun ilimin sanin kasar Sin tare da wuraren tarihi na kasar Sin domin kuwa wannan masallaci ina jin sunan nasa, amma ban taba ganin sa ba sai a wannan lokaci da sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ya ba ni goron gayyata ne na san wannan wuri mai dadanden tarihi na kasar Sin.

Don haka ina mai nuna godiya ta ga gidan rediyon kasar Sin musamman sashen Hausa na CRI da dukanin ma'aikatansa da wannan karimci na gode na gode.

Nine maisauraro,

Shugaba Bello Abubakar Malam Gero

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China