in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARA TA A BABBAN GIDAN AJIYAR KAYAN TARIHI NA XI'AN
2011-09-13 16:35:36 cri
Ranar karshe ta ziyarar mu a birnin Xi'an, wato Lahadi 11 ga watan Satumba, mun ziyarci babban gidan ajiye kayan tarihi na birnin Xi'an mai dadadden tarihi. Wannan gidan ajiye kayan tarihi ya hada kayan tarihi masu yawan gaske, wato bayan kayayyakin tarihi na daular Tang da ya fi yawa akwai kuma wasu kayan tarihin daban da suka hada da na daulolin da suka gabaci dualar Tang kamar daular Qin da ta Han. Har wa yau, cikin wannan gidan ajiye kayan tarihi akwai kayan tarihi na daulolin da suka biyo bayan ita daular ta Tang, kamar su daular Zhou, Song, Ming, da sauransu. Daga cikin kayan tarihin da na gani sun hada da kayan yaki kamarsu su kwari da baka, tukwanen girki da na cin abinci, tuluna ko butocin shan giya. Har ila yau, na ga butocin zuba shayi da kuma kofunan shan shayi na zinariya da na azurfa da ke da zane-zanen ado iri daban daban. Abin da ya fi ba ni mamaki da wadannan kayayyaki shi ne, yadda suke da nagartar kawowa ga wannan zamani ba tare da sun lalace ba, saboda bayanin da ka rubuta kusa da wadannan kayayyakin tarihi ya nuna cewa tun na zamanin da ne, wato an samar da su kimanin shekaru dari biyar zuwa dubu biyu da suka gabata. Babu shakka, wannan abin mamaki ne kuma nayi farin ciki da na sami ganin su da idanu na.

Wani abu da ya kara burge ni a wannan gidan ajiye kayan tarihi shi ne, yadda na ga wasu mutum-mutumi marasa girma dake alamanta yadda masu yi wa sarki hidima na zamanin daular Tang suka yi layi a jere kuma sahu-sahu suna kewaye da sarki wanda ke kan wata karaga mai tudu. Babu shakka, wadannan mutum-mutumi suna da ban mamaki, domin ya nuna yadda ake zaman fada a zamanin daular Tang (1368-1644).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China