in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARA TA A KABARIN SARKI QIN SHI HUANG DA KUMA FADAR HUA QING
2011-09-13 16:34:46 cri
A ranar 10 ga wata wato Asabar, mun ziyarci kabarin sarkin daular Qin na farko wato Qin Shi Huang. Wannan ziyara ta mu ta yi armashi domin kafin mu kai ga dakin da mutum-mutumin sojoji na sarki Qin shi Huang ya ke, mun yi nasarar yin ido hudu da ainihin manomin da ya gano kabarin sarki Qin Shi Huang a shekarar 1974 yayin da yake haka rijiya a gonar sa, wato Yang Xinman. Lokacin da muka isa dakin da mutum-mutumin sojoji na sarki Qin Shi Huang ya ke mun ga abin mamakin gaske, sabo da, idan mutum ya ga wadannan mutum-mutumi suna tsaye zai yi zaton ko basu wuce shekaru 50 da ginawa ba, amma idan mutum ya karanta allon bayani dake kusa zai gane cewa, an gina wadannan mutum-mutumi ne tun kimanin shekaru dubu biyu ko fiye. Wani abu da ya kara bani mamaki shi ne, mun ga keken doki da matukinsa da aka kera da tagulla wadanda aka gano cikin kabarin sarki Qin Shi Huang. Ban da wannan, akwai wasu kayan fada na sojojin sarki Qin da muka gani kamarsu kibiya da kwarinta, jallon ruwa da na giya, da sauransu duk na karfe. Duka wadannan kayan tarihi wata shaida ce dake tabbatar da cewa kasar Sin ta na da fusaha da karfi wurin yaki tun a zamanin da. Hakika, wannan abin al'ajabi ne da wadannan kaya suka kawo har wannan zamani ba tare da sun lalace ba. Mu kuma mutanen yanzu, gare mu abin burgewa ne mu samu damar kallon irin wadannan dadaddun kayan tarihi.

Bayan da muka kammala ziyara a kabarin sarki Qin Shi Huang, mun kuma ziyarci fadar Hua Qing inda sarakunan daular Tang suke wanka. Wannan fada na da ban mamakin gaske, bayan ta na da girma, an kuma gina ta ne a gindin dutsen Li Shan. Kamar yadda idanun mu ya nuna mana, a gindin wannan dutse akwai mabulbular ruwa irin ta halitta wato ba wacce dan adam ya samar ba, kuma an janyo ruwa daga wannan idanun ruwa ne zuwa dakunan da aka kebe kuma aka giggina wuraren wanka na musamman ga sarki Xuanzong, da kwarkwararsa da ya fi so, da kuma dansa a shekara ta 747. Wannan mabulbular ruwa ta halitta na da mamakin gaske, sabo da ruwan da ke fitowa daga cikin ta ya na da dumi sosai domin har hayaki yake fitarwa tamkar an dumama ruwa. Kai lalle wannan abin mamaki ya kai, wannan shi ya sa na gwada tarar wannan ruwa da hannu na don nima na ji dumin ruwan.

Babu shakka, duk wanda ya sami damar ziyarar kasar Sin to yana da kyau ya ziyarci fadar Hua Qing da ke gindin dutsen Li Shan don gane wa idon sa abubuwan ban mamaki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China