in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARA TA A WURIN BIKIN NUNE-NUNEN KAYAN FASAHAR LAMBU NA KASA DA KASA NA BIRNIN XI'AN
2011-09-13 16:34:06 cri
Yau Juma'a 9 ga wata mun ziyarci wurin da ake gudanar da bikin nune-nunen kayan fusahar lambu na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Xi'an. Babu shakka, yadda gwamnatin kasar Sin ta tanadi wannan katafaren fili a birnin Xi'an don gudanar da wannan biki ya nu na yadda kasar sin take bayar da muhimmanci ga batun kiyaye muhalli da kuma samar da iska mai tsafta don inganta lafiyar al'umma. Hakika, wannan bikin nune-nune ya kayatar da ni sabo da yadda na ga kasashe da dama na duniya sun halarci bikin kuma sun nuna irin tasu fasahar, wato idan mutum ya zagaya wannan wuri zai yi tsammanin cewa ya zagaya duk duniya ne cikin wani dan lokaci. Ga misali, idan mutum ya leka kowacce rumfa, zai iya fahimatar al'adu, tarihi da kuma irin fasahar da wannan kasa take da shi. Lalle, akwai abin burgewa sosai dangane da haka.

Yayin da muka ziyarci rumfar da kasar Nijeriya ta kafa mun ga kayan sassake-sassake da na sake-sake irin na gargajiya. Sa'an nan, mun ga hotunan ziyara da shugabanni da wasu manyan jami'an gwamnati na kasashen sin da Nijeriya suka kai kai wa juna a lokaci daban daban. Wannan rumfa ta kasar Nijeriya ta na da girma domin har wasu kasashen Afrika kamar kasar Guinea ta baje kolinta cikin rumfar.

Wani abu da ya bani sha'awa kuma, kasar Sin mai karbar wannan biki ta fi burge ni, sabo da ta nuna kayan fasaha da salon gine-gine masu yawa dake nuna yadda kasar Sin ta shahara wajen tsara lambu da wuraren shan iska musamman a lokaci zafi tun daga zamanin da zuwa yanzu. Ga misali, na ga yadda aka kwaikwayi lambun shan iska da kuma karamu masu fitar da ruwa masu yanayi irin na kasar Sin. Babu shakka, wannan wuri ya burge ni kwarai da gaske.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China