in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ZIYARA TA A BABBAN MASALLACIN BIRNIN XI'AN
2011-09-13 16:33:25 cri
Ranar Alhamis 8 ga wata, mun ziyarci masallacin birnin Xi'an mai dadadden tarihi. Kafin wannan ziyara tawa a karon farko a birnin Xi'an ban taba tsammanin akwai masallaci dake da tarihin kafuwa na fiye da shekaru 1,200 ba, amma a lokacin da na sanya kafa ta cikin wannan masallaci sai mamaki ya kama ni sosai. Sabo da na ga kayan tarihi na masallacin irin na zamanin da. Ko da yake, bamu ga wani kayan tarihi na lokacin daular Tang sun bace a wannan masallaci, amma duk da haka na ga gine-gine da aka yi tun zamanin daular Ming da suka kawo wannan zamani basu bace ba. Wannan ya tabbatar da cewa, masallacin ya sami kulawa ta musamman tun daga zamanin daulolin Song, Yuan, Ming da kuma Qing, har kuma zuwa kasar Sin ta zamani karkashin JKS.

Abin da ya fi burge ni da wannan masallaci shi ne, ya na da girma kuma na ga masu yawon shakatawa da kasashen daban-daban sun zo don ziyarar bude ido a wannan masallaci na birnin Xi'an mai dadadden tarihi.

Daga nan kuma, mun ziyarci babbar kasuwar birnin Xi'an inda muka ga kayayyakin gargajiya na kasar Sin kamar su, jakunkuna, riguna, huluna, kayan sake-sake da na zane-zane masu yanayin musamman na kasar Sin. Babu shakka, abubuwan da na gani a wannan kasuwa suna da ban sha'awa matuka. Kazalika, cikin wannan kasuwa dai mun ziyarci wani gidan cin abinci irin na al'ummar Musulmi, har ma muka ci wani irin abinci mai dadi da aka hada miyar sa da naman rago da ake kira cikin harshen Sinanci 'Yangrou Paomo'.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China