in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tafiya yawon shakatawa na Biyu a birnin Beijing
2011-09-08 22:01:00 cri
Ina mai godiya ga sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin da ya ba ni damar in kawo ziyara a kasar Sin a birnin Beijing, a wannan gayyatar da aka yi min ta ba ni damar kara sanin kasar Sin mai dogon tarihi inda a yau na sami damar kai ziyara a babbar ganuwar kasar Sin, wurin da nake jin labarinsa aka fara watsa labaruna kasar Sin da na duniya baki daya to sai ga shi a yau cikin hikimar ubangiji tare da taimakon sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin CRI na gane ma idanuwana da hannuwana da kuma kafafuwana ganuwar kasar Sin THE GREATWALL OF CHINA.

Ba shakka wannan abin yabawa ne tare da jinjinawa ga gwamnatin kasar Sin da dukkanin al'ummarta wajen kare martabar kayayyakin tarihi da alabun kasa baki baya wannan ya nuna azahiri dacewa kasar Sin kasa ce mai dadadden tarihi.

Abu na biyu shi ne mun zagaya a filayen wasannin olympic da kasar Sin ta gina a lokacin gasar, wadannan wurare muna jin labarinsu ne tun lokacin da kasar Sin ta sami damar daukar wannan gasa har aka kammala su aka soma wasannin olympic duk muna biye da gidan rediyon CRI yana fayyace muna yadda abubuwan ke gudana haka ma muna karanta mujallun kasar Sin, musanman na gidan rediyon CRI, muna samun labaru amma ba mu taba ganinsu ba sai a yau da muka zagaya tare da  masaukinmu muka ga abubuwa masu ban sha'awa, a gaskiya wannan abu ya burge ni.

Daga karshe ina mika godiyata ta musamman ga shugaban sashen Hausa malam sanusi da kuma masu yi muna jagora malam Fatima da malama Zainab a kan jan namijin kokarinsu da suka nuna muna suka zagaya da mu a ko ina suka nuna muna wurare daban daban ina mai godiya a gare su tare da fatar Allah ya kara dankon zumunci tsakanimmu da wannan gidan rediyo amin na gode nagode.  (SHUGABA BELLO ABUBAKAR MALAM GERO)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China