in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da ta burge ni
2011-09-08 21:56:39 cri
Ina mai nuna jin dadina tare da nuna farin cikina akan gayyatar da gidan rediyon kasar Sin ya yi min na in kawo ziyara gani da ido a sanadiyyar gasar kacici kacici akan cikon shekaru arba'in da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Nigeria.

Ba shakka wannan ziyara ta burge ni kuma ta ba ni damar ganin kasar Sin da idona kamar yadda muke samun labarin kasar Sin a cikin rediyon CRI a lokacin da ban zo ba tare da wuraren tarihi masu girma na kasar Sin musamman fadar sarakunan kasar Sin mai dogon tarihi, wannan abu ya kara jawo hankalina da in kara sadaukar da kaina a wajen sauraron gidan rediyon c r i  musamman sashen hausa.

Bayan haka kamar yadda kowa ya sani idan mutum yana bako, to a ko da yaushe yana bukatar a taimaka mishi, to hakikanin gaskiya sashen hausa ya burge ni da yadda dukkanin ma'aikatan wannan sashe suka kula da mu suka fara zagayawa da mu suna ilimantar da mu domin mu kara sanin kasar Sin musaman birnin Beijing na kasar sin, inda malama fatima da malama zainab sukavyi iyakacin kokarinsu domin ganin cewa sun biya bukatunmu kamar yadda shugabannin wannan gidan rediyo suka umurce su, muna godiya da wannan karimci na Sinawa.

Har wa yau abu mafi mahimmaci shi ne irin yadda aka tara dukkanin ma'aikatan sashen hausa da ma wasu sashe aka yi bukin karramamu, a gaskiya wannan abun yabawa ne a gare ni, bayan haka a ko da yaushe Hausawa na cewa tuwon girma miyarsa nama don haka ni kan ina nuna godiyata ta musamman a kan wannan cigaba da na samu a cikin rayuwata sanadiyar sashen hausa na c r i da ma gidan rediyon baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China