in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarata a karon farko a birnin Beijing 
2011-09-08 21:52:24 cri
Na fara ziyarata ta farko a birnin Beijing ranar Talata 6 ga wata, kuma babu shakka birnin Beijing ya burge ni da yawan gaske. Dalilin da yasa nace birnin Beijing ya burge ni shi ne, wato ya na da girma sosai kuma akwai manyan gine-gine irin na zamani, sa'an nan akwai tsafta kuma mutanen birnin Beijing sun nuna min kauna mai yawa musamman lokacin da na je dandalin Ti'anment dake tsakiyar birnin Beijing, Sinawa masu yawa sun nuna sha'awar daukar hoto tare da ni, kuma sun nuna sha'awarsu sosai ga tufafi na irin na gargajiya. Gaskiya wannan ya nuna cewa Sinawa suna son baki sosai, wato ba sa nuna kyama ga baki samsam.

A lokacin da na saka kafa ta a katafariyar fadar sarakuna ta birnin Beijing na ga abin mamakin gaske, wato bayan girman fadar na da ban al'ajabi, kuma yadda aka fasalta ko tsara gininta shi ma abin mamaki ne. Saboda maginan Sinawa a zamanin da sun nuna fusaha wajen yin gini mai amincin gaske, wato yanzu shekaru fiye da 600 ginin fadar sarakuna bai lalace ba. Lalle wannan abin mamakin gaske ne.

RA'AYI NA KAN ZIYARAR DA NA KAI A BABBAR GANUWAR KASAR SIN DA FILIN WASAN OLYMPIC NA BIRNIN BEIJING

A yau ranar Laraba 7 ga wata, na ziyarci babbar ganuwar kasar Sin wacce ta shahara sosai a duniya. Wannan ganuwa tana da ban mamakin gaske, saboda an gina ta da tubala masu karfi da kuma duwatsun da aka sarrafa, sa'an nan an gina ta ne akan manyan tsaunuka zuwa cikin kwazazzabai, kai gaskiya babbar ganuwa tana da ban al'ajab. Ni kaina yanzu na fahimci cewa, babbar ganuwa ta fi yadda ake ganinta a hoto ban mamaki. Kuma wani abu da ya kara burge ni da babbar ganuwa shi ne, har yanzu babbar ganuwa tana nan da kyawunta, wato kamar ba ta kai tarihin shekaru fiye da dubu biyu ba tun bayan da aka gina ta. Lalle, idan mutum ya na son ganin abin ban mamaki danagane da babbar ganuwar kasar Sin to sai ya zo ya gani da idanunsa, domin Hausawa sun ce, "Gani ya kori ji".

Babu shakka, yadda na gane wa idanuna babbar ganuwar kasar Sin ya tabbatar min da cewa al'ummar Sinawa suna da kwazon aiki, juriya da kuma jarumtaka. Abin da ya sa na fadi haka shi ne, na hau kan babbar ganuwar kasar Sin da kafafuwa na kuma na gaji sosai duk da cewa ban kai kan kolinta ba, to wannan ya sa na yi tunani cewa, idan hawa babbar ganuwa kawai yana da wahala, to lalle mutanen da suka gina ta jaruman gaske ne.

Dangane da haka, ina ba da shawara ga masu sauraro da suke da ikon zuwa kasar Sin, su zo su gane wa idanunsu abin al'ajabi da ke tattare da babbar ganuwar kasar Sin.

A yayin da na kai ziyara a filin da aka shirya gasar wasannin Olympic na birnin Beijing duk a ranar 7 ga wata, na gane wa ido na filin wasa mai fasalin 'shekar tsuntsu' kuma wannan fili ya ba ni sha'awa sosai domin injiniyoyi na kasar Sin nuna fusaha sosai wajen gina ta, saboda irin wannan filin wasa mai siffar shekar tsuntsu shi ne irinsa na farko da aka gina a duniya. Lalle kuwa wannan abin burgewa ne ga al'ummar kasar Sin, domin ya nuna cewa sun da ci gaba ta fannin fusahar gine-ginen zamani. Ban da wannan, na kuma ziyarci filin wasan ninkaya wanda ake kira 'water cube' wanda ke kusa da filin wasa mai siffar shekar tsuntsu. Shi ma wannan filin wasa na gasar ninkaya ya burge ni sosai, saboda an yi amfani da kayan zamani wajen gina ta. Wani abu da ya kara ba ni sha'awa da filin wasan Olympic na birnin Beijing shi ne, akwai makeken fili a tsakanin wadannan filayen wasa guda biyu da ke kama da filin Ti'anmen da ke tsakiyar birnin Beijing.(Nuraddeen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China