in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRI na rubuta bayanai kan bunkasuwar kasar da sauyewar duniya bisa sanin ya kamata
2011-06-09 17:06:04 cri
A cikin shekaru 70 da suka wuce, CRI ba ma kawai ya yi wa kasashen ketare bayani kan yadda kasar Sin take bunkasa ba, haka kuma ya rubuta bayanai kan sauyawar halin da ake ciki a duniya bisa sanin ya kamata, tare da sa kaimi kan samun fahimtar juna a tsakanin al'ummomin kasa da kasa.

To, masu karatu, tambayoyi 2 da ke cikin shirinmu na yau su ne, da farko cibiyoyin kula da harkokin kananan ofisoshin manema labaru nawa ne CRI yake shirin kafawa a ketare? Na biyu kuma, yaushe ne gidan rediyon CRI ya kaddamar da ziyarar sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Rasha zuwa Rasha? Bayan kun karanta shirinmu na yau, za mu gabatar muku da amsoshin wadannan tambayoyi!

A matsayinta na hukumar da ke watsa labaru cikin harsuna da dama a duniya, CRI na kokarin gabatar wa kasashen duniya abubuwan da suke faruwa a nan kasar Sin da ma duniya baki daya.

A watan Maris na shekarar 1999, yaki ya barke a yankin Kosovo, lamarin da ya sanya Wang Zhimin, wakiliyarmu a kasar Yugoslavia ta rasa abin da za ta yi, amma cikin sauri Wang ta nuna jaruntaka ta ziyarci mazauna wurin da yawa da suke fama da wahalar yakin. Ta gidan rediyon CRI, ta yi kokarin gaya wa kasashen duniya abubuwan da suka faru a Kosovo. Wang ta ce,"Ni ma ina cikin fargaba matuka da samun sanarwa game da barkewar yakin. Na rasa abin da zan yi. Ban taba fuskantar yaki ba, ban san makomar yakin ba. Na nuna jaruntaka na tuki mota zuwa makarantu da sauran wuraren da na sani. Na yi sa'o'i 8 ban ci abinci ba, ina tukin mota inda na zagaya kusan rabin birnin Belgrade a yini daya. A duk wurin da na ziyarta, mazauna wurin masu kirki sun karbe ni sosai, sun yi hira da ni, wannan ya sa hankalina ya kwanta, har na san yadda zan tattara labaru kan yakin."

Tun daga shekarun 1980 da CRI ya kafa ofisoshin wakilansa a ketare, ya zuwa yanzu akwai ofisoshin wakilan CRI guda 32 a duk duniya. CRI kuma ya yi shirin kafa manyan hukumomin kula da harkokin wadannan ofisoshinsa guda 8 a nahiyoyin Afirka da Turai da Arewacin Amurka da Latin Amurka da yankin Gabas ta Tsakiya cikin shekaru 10 masu zuwa, wadanda za su mai da hankali kan abubuwan da suke faruwa a ko ina a duniya.

A shekarun baya, sakamakon bunkasuwar kasar Sin, kasashen duniya sun fara juya hankali da kuma yin Allah-Allah wajen sauraron muryar kasashe masu tasowa. A duk yayin da muhimman al'amura a duniya suka faru, CRI ya kan rubanya kokarin bayyana ra'ayin kasar Sin kan wadannan al'amura. A game da wannan, Hong Lin, tsohon wakilin CRI a kasar Pakistan ya bayyana cewa,"Manema labaru na kasar Sin da na kasashen duniya ba su da ra'ayi daya kan wani batu. Ya kamata mu manema labaru na kasar Sin mu bayyana ra'ayinmu, mu yi tunani bisa basirarmu. Saboda muna wakiltar kasar Sin, haka kuma a wasu lokuta, muna wakiltar kasashe masu tasowa. Idan kafofin yada labaru na kasar Sin sun kasance muhimman majiyoyi na duniya, wannan zai taimaka wajen bunkasuwar kansu, haka kuma zai ba da taimako wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya."

Baya ga mai da hankali kan bunkasuwar kasar Sin da sauyawar halin da ake ciki a duniya, a shekarun baya, CRI ta yi ta sabunta hanyoyinta na sadarwa a tsakanin kasa da kasa, ta shirya wasu manyan harkoki a kasashen ketare da kuma yankuna, a kokarin taimakawa jama'ar kasashen waje su kara fahimtar kasar Sin da kulla zumunci a tsakaninsu da jama'ar Sin.

A shekarar 2006, bisa kudurin da shugabannin kasashen Sin da Rasha suka tsaida, kasashen 2 sun kaddamar da shekarun kasashen juna. Sabili da haka, CRI ya tsara wani shiri da tura wakilansa zuwa Rasha don su tattara labaru domin sada zumunci a tsakanin Sin da Rasha. A shekarar 2007, kafofin yada labaru da dama na Rasha sun zagaya larduna da birane 15 na kasar Sin domin tattara labaru, lamarin da ya samu cikakkiyar nasara.

Fan Bingbing, kwararriya ce a harshen Rashanci da ke aiki a gidan rediyon CRI kuma daya daga cikin masu tsara harkar sada zumunci a tsakanin Sin da Rasha ta gaya mana, dalilin da ya sa ta tsara wannan harka tana cewa,"Burina shi ne taimakawa mutanen Rasha su kara sanin Sinawa, haka kuma Sinawa su kara sanin mutanen Rasha. A farkon shekarun 1990, lokacin da na ziyarci Rasha, na yi matukar mamaki saboda mutanen Rasha ba su san kasar Sin sosai ba. Sabili da haka, na yi tunanin shirya irin wannan shiri, inda manema labaru na kasashen 2 za su iya tattara labaru a tsakaninsu, suna iya tuntubar juna, kana kuma, kafofin yada labaru na kasashen 2 suna iya yin mu'amala da kara fahimtar juna."

Haka zalika, bayan shekaru 2, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun ba da lambar yabo ga wanda ya ci lambar zinariya a gasar rera waka cikin harshen Rashanci a tsakanin Sinawa, wadda CRI ya shirya. Mista Putin ya yi farin ciki matuka yana mai cewar,"Abun da ya fi burge ni shi ne Sinawan da shekarunsu suka sha bamban a duniya suke sha'awar al'adun Rasha, matasa da yawa sun shiga gasar, lamarin da ya faranta mana rai kwarai da gaske!"

A ganin Mista Wen Jiabao, gasar rera waka cikin harshen Rashanci a tsakanin Sinawa da dai sauransu suna iya kara kusantar jama'ar Sin da Rasha sosai, haka kuma, wani harsashi ne da zai rika kyautata dangantaka a tsakanin Sin da Rasha. Wen ya ce,"Kasashen Sin da Rasha, manyan kasashe ne masu dogon tarihi. Jama'ar kasashen 2 da zumuncin da ke tsakaninsu, tamkar wani harsashi ne wajen bunkasa dangantaka a tsakanin kasashen 2. Hakan ya sa ya zama wajibi a gode muku, saboda kuna amfani da harsuna domin sa kaimi kan yin mu'amalar tunani da al'adu a tsakanin jama'ar kasashen 2, kuna amfani da kide-kide da wakoki domin kusantar jama'ar kasashen 2, lamarin da zai samar wa kasashen 2 kyakkyawar makoma."

Baya ga haka kuma, a shekarar 2010, CRI ya hada kai da wasu takwarorinsu na Sin da Viet Nam wajen shirya gasar rera wakokin kasashen 2, inda mutane fiye da dari 3 suka shiga gasar ta tsawon rabin shekara.

A shekarun nan, sassa daban daban na CRI sun hada kai da takwarorinsu na kasashen waje wajen shirya harkokin yin mu'amala. Wadannan harkoki sun yaukaka zumunci da fahimtar juna a tsakanin Sin da kasashen waje, tare da sa kaimi kan yin mu'amalar al'adu a tsakaninsu. Yin Li, mataimakin babban edita na CRI ya nuna babban yabo da cewa,"A matsayinsa na kafar yada labaru a duniya, CRI na da alhakin shirya harkokin da ke iya sa kaimi kan yin mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da kasashen waje, sada zumunci a tsakaninsu, da kara fahimtar juna. Yanzu ga alama mun cika burinmu."

To, masu karatu, kafin mu kawo karshen shirinmu na yau, bari mu yi bitar tambayoyin 2. Da farko cibiyoyin kula da harkokin kananan ofisoshin manema labaru nawa ne CRI yake shirin kafawa a ketare? Na biyu kuma, yaushe ne gidan rediyon CRI ya kaddamar da ziyarar sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Rasha zuwa Rasha?(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China