in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
 Muna son muryarka CRI (3)
2011-06-09 16:00:38 cri
Muna son muryarka CRI (3)

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, yau za mu gabatar muku da bayani na musamman game da gasar kacici-kacicin da muka shirya muku domin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar gidan Rediyon kasar Sin wato CRI. Masu sauraro, kowace rana, kuna sauraren gaisuwa da labarai da dumi duminsa da CRI ke gabatar muku da harshenku daga kasar Sin wadda ke da nesa sosai daga kasarku, muna fatan kuna jin dadin sauraren shirye-shiryenmu. To, kamar yadda aka saba, a cikin shirinmu na yau, za mu kara ma ku tambayoyi guda biyu kamar haka:

Ta farko, harsuna nawa ne CRI ke watsa labarai da su ta rediyo ko ta yanar gizo?

Ta biyu, a wace shekara ce aka kafa tashar yanar gizo ta CRI wato CRI Online?

Kuna iya samun amsa daga bayanin da za mu karanta muku.

A gidan Rediyon kasar Sin, da harsuna da aka fi yadawa a kasa da kasa kamar Turanci, Faransanci, Spanisanci, Rashanci, Larabanci, da kuma harsunan da kasashe ko kabilu kalilan ke yin amfani da su kamar Hausa, Swahili, Pushtu, Bengali, dukan sassan harsuna suna da KHz da tasoshin yanar gizo na kansu. Yayin da CRI ke watsa labarai da harsuna 61, muna kara kaunar jama'a da al'adun wadannan kasashe, amma ba harsuna kawai ba. ************

A ran 29 ga watan Agusta na shekara ta 1968, sashin harshen Romania na CRI ya fara watsa labarai a hukunce, dalibi Luo Dongquan wanda ke karatu a kasar Romania yana sauraren rediyo tare da abokan karatunsa, yayin da suka ji muryar CRI da ta fito daga wani tsohuwar na'urar rediyo, sun yi shewa dalilin farin ciki.

Luo Dongquan ya gaya mana cewa, (音响1, 骆东泉) "A wancan lokaci, muna karatu a kasar Romania, yayin da muka samun labari game da kafuwar sashin harshen Romania a kasar Sin, mun yi farin ciki sosai, a ran 29 ga watan Agusta na shekara ta 1968, daliban kasar Sin dake karatu a kasar Romania dukanmu muna zauna tare domin jiran murya daga birnin Beijing, tun daga nan, na kudirta cewa, zan je CRI in yi aikin watsa labarai da harshen Romania bayan na kammala karatu a Romania."

Bayan shekara daya wato a shekara ta 1969, an yi hayan Luo DongQuan domin ya yi aiki a sashin harshen Romania na CRI. Ya bayyana mana cewa, karanta labarai da harshen Romania ya yi kama da rera waka, yana da dadin ji ainun. Yanzu ya riga ya mayar da Romania a matsayin garinsa na biyu. Ya ce, (音响2,骆东泉) "Na fara koyon harshen Romania yayin da nake da shekaru 17 da haihuwa, kawo yanzu, fiye da shekaru goma na mayar da Romania garina na biyu. Na kan gaya wa jama'ar Romania cewar na fi son burodin Romania, ana iya cewa, na girma tare da cin burodin Romania. A sanadin haka, ina kaunar jama'ar Romania, na mayar da su kaman 'yan uwana, in na hadu da su, na kan saje mu yi ta hira da su, lallai ina kaunar harshen Romania."

A gidan rediyon kasar Sin, ko ina ana iya ganin ma'aikata wadanda suke daukan harshen waje a matsayin babban sha'aninsu na muddin rai, amma ba sai aiki kawai ba. A zukatunsu, kasa babba ko karama, babu banbanci, al'adu kuma ba iyakar kasa, a ko da yaushe, suna alfaharin yin cudanya da masu sauraro da wani harshe.**************

Sashin Bengali na CRI yana da dogon tarihi sama da shekaru arba'in, a cikin wadannan shekaru, muryar sada zumunta da ta zo daga kasar Sin tana ci gaba kowace rana. Masu sauraro na kasar Bangladesh masu yawan gaske sun girma tare da sauraren shirye-shiryen CRI. Yawancinsu sun mayar da masu watsa labarai da Bengali na kasar Sin aminansu na ko da yaushe. Shi Jingwu wanda ya rike aikin watsa labarai da Bengali cikin shekaru fiye da goma ya bayyana cewa, a ganin masu sauraro, watsa labarai da harshensu babbar biyayya ce da kasar Sin ke nuna wa al'adunsu. Ya ce, (音响3,石景武) "Koda yake kasar Bangladesh tana da yawan mutane, amma fadin kasar ba shi da girma, shi ya sa, jama'ar kasar su kan mayar da kasar Sin babbar kasa, suna ganin cewa, kasar Sin ta kan nuna biyayya ga dukan kasa da kasa, domin wannan, sinawa da yawan gaske suna koyon Bengali kuma suna watsa labarai da harshen kabilarsu, wannan ya burge su kwarai. Masu sauraro su kan rubuto mana wasiku inda su kan bayyana cewa, ana iya cewa, kasar Sin ta nuna musu biyayya sosai saboda CRI yana watsa labarai da harshen kabilarsu, suna jin dadin sauraren shirye-shiryen CRI sosai."************

Sha'anin watsa labarai ga kasashen waje na CRI yana samun cigaba bisa bukatun zamani da sauye-sauyen yanayin kasa da kasa. Yanzu dai, CRI yana kokarin ciyar da gine-ginen tsarin yanar gizo gaba. A shekara ta 1998, aka kafa tashar yanar gizo mai taken "CRI Online" a turance, wannan tashar yanar gizo ta kunshi harsuna da yawa. Ba ma kawai masu sauraro suna iya sauraren shirye-shiryen da aka karanta da harsunan kasashensu ba, har ma suna iya karanta labaran da aka rubuta da harsunansu a shafin yanar gizo na CRI. Kawo yanzu, yawan harsunan da ake amfani da su a tashar yanar gizo ta CRI ya riga ya kai 61, haka kuma CRI ya zama hukumar watsa labarai ta kasa da kasa wadda ta fi yawan harsuna a duniya. Irin wannan dandalin zamani na kafar watsa labarai ya jawo hankalin matasa da yawa. Xi Meng mai aiki a sashin harshen Pushtu na daya daga cikinsu.

Harshen Pushtu yana daya daga cikin harsunan da ake amfani da su a kasar Afganistan, yana da tarihi na tsawon shekaru fiye da dubu uku. An kafa sashin Pushtu na CRI a shekara ta 1973, a shekara ta 2010, an fara watsa labarai na FM na Pushtu na CRI a biranen Kabul da Kandahar na Afganistan, ana iya cewa, wannan ya bude wani sabon shafi ga jama'ar kasar domin su kara fahimtar kasar Sin. Xi Meng ya gaya mana cewa, tashar gidan rediyo CRI ne daya kadai ne wanda ke watsa labarai da harshen Pushtu ta bakin ma'aikatan kasar ketare a duniya, haka shi ma ya burgi masu sauraron Afganistan sosai. Domin kara karfafa cudanya tsakanin kasashen biyu na Sin da Afganistan, sashin Pushtu ya wallafa kamus na farko na harsunan Sinnanci da Pushtu.*************

A cikin harsuna 61 da CRI ke amfani da su, harshen Esperanto yana da tsarin musamman saboda harshen ba na wata kasa ko na wata kabila ba ne, harshe ne da aka kirkiro. Amma a CRI, ana daukan harshen wani harshe mai ban mamaki. Sashin Esperanto shi ma yana da tarihi sama da shekaru 50. Wang Shanshan tana aiki a sashin, a shekara ta 2004, ta taba halartan babban taron harshen Esperanto a karo na 89 da aka shirya a birnin Beijing bisa matsayinta na mai sa kai. Wang Shanshan ta sheda cewa, dalilin da ya sa aka kirkiro wannan harshe shi ne domin nuna fatan dan adam na kasancewa daidai wa daida, saboda wannan harshe ya zama shi ne harshe na biyu ne na dukan jama'ar kasa da kasa. Ana iya yin cudanya bisa tushe daya da harshen. A CRI, a ko da yaushe, ana kokarin gaya wa masu sauraro cewar, muna cikin duniya daya.

A karshe, bari mu maimaita tambayoyi biyu na yau, harsuna nawa ne CRI ke watsa labarai da su ta rediyo ko ta yanar gizo? Ta biyu, a wace shekara ce aka kafa tashar yanar gizo ta CRI wato CRI Online?

Masu sauraro, karshen shirinmu na yau ke nan daga nan sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin. Jamila take cewa, ku zama lafiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China