in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daga zangon daga kago na garin Yan'an zuwa tasoshin rediyon FM a biranen da kuke zaune
2011-06-13 11:12:44 cri
Ibrahim: Jama'a masu karatu, bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kafuwar gidan rediyon CRI da aka kafa shi ne a lokacin da aka yi yakin duniya na biyu, wato yakin fama da Facsist, yanzu ya zama wata muhimmiyar kafar watsa labaru ta kasa da kasa dake amfani da harsuna 61 domin watsawa duniya shirye-shirye, mika gaisuwar sada zumunci ga jama'ar kasa da kasa, bayyana aniyar jama'ar Sin ta nema da kuma tabbatar da zaman lafiya da adalci, da kuma girmama da darajta al'adu da wayewar kai iri daban daban da suke kasancewa a duniya. Tun daga yau, a cikin shirinmu na musamman, za mu karanta muku bayanai 4, inda za ku kara fahimtar yadda gidan rediyon CRI ya samu ci gaba cikin shekaru 70 da suka gabata, kuma muna fatan za ku shiga wata gasar kacici kacici mai taken "Muryar dake bayyana tarihin CRI" domin murnar cika shekaru 70 da kafa gidan rediyon CRI. Kamar yadda muka saba yi a cikin gasannin kacici kacici da muka shirya a baya, da farko dai ga tambayoyi biyu na shirinmu na yau:

Tambaya ta farko ita ce, Wane harshe aka fara yin amfani da shi a lokacin da aka bude gidan rediyon CRI?

Tambaya ta biyu ita ce, a wane birni ne gidan rediyon CRI ya kafa rediyo na zangon FM na farko a kasashen waje?

Sanusi: Jama'a masu sauraro, za ku iya samun amsoshin wadannan tambayoyi biyu a cikin bayanin da za mu karanta muku. A farkon shekaru 40 na karnin da ya gabata, a lokacin da Sinawa suka yi kokarin yaki da sojojin Japan wadanda suka kawo wa kasar Sin hare-hare, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ke aiki a garin Yan'an dake arewa maso yammacin kasar Sin ya tsai da kudurin kafa gidan rediyon Xin Hua domin sa kaimi kan jama'ar Sin da su yi kokarin fama da 'yan Fascist sojojin Japan. Sannan a ran 3 ga watan Disamba na shekarar 1941, shi ne karo na farko da aka fara yin amfani da harshen Japan wajen watsa labaru ga sojojin Japan wadanda suke kasar Sin. Sakamakon haka, wannan rana ta zama ranar da aka kafa gidan rediyon CRI.

Ibrahim: Ko da yake a wancan lokaci, dakin da ake amfani da shi wajen daukar murya wani kago ne da aka haka a kasa, karfin injin watsa sautin rediyon watts dari 3 ne kawai, amma tun daga wannan rana, ya kasance gidan rediyon dake watsa labaru ga masu sauraro na kasashen waje a nan kasar Sin. Marigayiya Hara Kiuoshi, ita ce mai ba da rahoto na farko ta gidan rediyon CRI ta tuna da cewa, "A lokacin da na yi aikin watsa labaru a Yan'an, babu kyakkyawan yanayi, amma sauran mutanen da suke aiki a Yan'an sun goyi bayanmu kwarai."

Sannan jama'a masu sauraro, bayan an kawo karshen wutar yakin duniya na biyu, a shekarar 1947, gidan rediyon Xin Hua na Yan'an ya fara yin amfani da harshen Turanci wajen watsa labaru ga jama'a masu sauraro na kasashen waje. Yanzu a kowace kusurwar duniya, har ma a teku, kana iya kama shirye-shiryen Turanci na gidan rediyon CRI.

Sanusi: Jama'a masu sauraro, an kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin ne a shekarar 1949. A gun bikin kafuwar sabuwar kasar Sin, marigayiya Ding Yilan, tsohuwar ma'aikaciyar gidan rediyon CRI ita ce ta ba da rahoto daga babban gini na Tian Anmen. Daga baya a shekarun 80 na karnin da ya gabata, ta zama shugabar gidan rediyon CRI.

Bayan an kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, an dawo da gidan rediyon Xin Hua zuwa Beijing, babban birnin sabuwar kasar Sin. Sannan an canja sunan wannan gidan rediyon zuwa gidan rediyon CRI. Yanzu yana amfani da harsuna 61 wajen watsa labaru ga duniya. Sakamakon haka, ya zama gidan rediyon dake kunshe da harsuna mafi yawa a duniya baki daya.

Ibrahim: A karshen shekarun 70 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofarta ga sauran kasashen duniya. Wannan ya zama wani kyakkyawan yanayi ga gidan rediyon CRI wajen neman ci gaba cikin hanzari. Kuma ya dauki matakai masu tarin yawa na yin gyare-gyare kan manufofin watsa labaru da yake aiwatarwa da shirye-shirye da kuma salonsu. Marigayiya Ding Yilan, tsohuwar shugabar gidan rediyon CRI ta jagoranci wata tawagar wakilan gidan rediyon zuwa rangadin aiki a kasashen Amurka da Jamus da kasashen Latin Amurka domin kokarin kafa ofisoshin wakilan gidan rediyon a kasashen waje. Game da yadda take fama da aiki, yaronta Mr. Deng Zhuang ya gaya wa wakilinmu cewa, "Gidan rediyon CRI ya tsara shirin kafa ofisoshin wakilansa a kasashen waje a kokarin neman labaru da bayanan da masu sauraro suke bukata ta yadda za a iya inganta shirye-shiryensa. Mamana ta mai da hankalinta sosai kan wannan aiki. Tana fatan gidan rediyon CRI ya wakilci Jamhuriyar Jama'ar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen watsa labarun kasa da kasa, shi ne niyya da burin da take son cimmawa."

Sanusi: Bugu da kari, a lokacin da ake samun ci gaban fasahohin da suke shafi harkokin watsa labaru, gidan rediyon CRI yana kokarin sauya hanyoyinsa na watsa labaru. A watan Faburairu na shekara ta 2006, wani gidan rediyon da gidan rediyon CRI ya kafa da kansa a birnin Nairobi na kasar Kenya ya fara watsa shirye-shirye ta zangon FM, shi ne gidan rediyon FM na farko da kasar Sin ta kafa a kasashen waje. Game da wannan gidan rediyon FM, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin wajen kasar Sin a wancan lokaci ya gaya wa manema labaru na gida da na waje, cewar "A kwanan baya, na ziyarci wasu kasashen Afirka. Na gano cewa, dangantakar dake tsakaninmu da kasashen Afirka ta samun ingantuwa sosai. Na sani cewa, shirye-shiryen da gidan rediyonku na CRI ke watsawa a wadannan kasashe na Afirka suna karbuwa sosai."

Ibrahim: Bayan watanni 9 ke nan, gidan rediyon CRI ya kafa gidan rediyon FM na biyu a Vientian, babban birnin kasar Laos. Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ya ziyarci kasar shi da takwaransa na kasar Laos Mr. Choummaly Sayasone sun halarci bikin kaddamar da rediyon. Har ma Mr. Choummaly Sayasone da iyalinsa sun zama masu sauraron gidan rediyon CRI. Mr. Choummaly Sayasone ya fadi cikin harshen Laos, cewar, "Shirye-shiryen gidan rediyon CRI suna samun karbuwa a kasar Laos. Ni kaina da jama'ar Laos masu tarin yawa muna sauraran shirye-shiryenku dake kunshe da labaru da dumi-duminsu da ilmantarwa. Jama'a masu sauraro na Laos suna samun ilmi game da kasar Sin, gami da zaman rayuwar yau da kullum."

Sanusi: Jama'a masu sauraro, gidan rediyon CRI ya kafa kananan gidajen rediyon FM ba ma kawai a kasashen Kenya da Laos ba, har ma ya kafa kananan gidajen rediyon FM a biranen Yamai da Maradi da Zinder da Agadez na Jamhuriyar Niger a watan Satumba na shekarar 2007 da 2008. Ya zuwa ran 1 ga watan Yuni na bana, yawan kananan gidajen rediyon FM da gidan rediyon CRI ya kafa a kasashen waje ya kai 60, inda ake watsa shirye-shiryen da tsawonsu ya kai sa'o'in 1200 a kowace rana domin biyan bukatun jama'a masu sauraro.

Ibrahim: To, jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na gasar kacici-kacici mai taken "Muryar dake bayyana tarihin CRI" daga nan sashin Hausa na CRI. Yanzu bari mu maimaita tambayoyi 2 da muka gabatar muku yau:

Tambaya ta farko ita ce, Wane harshe ne aka fara yin amfani da shi a lokacin da aka bude gidan rediyon CRI?

Tambaya ta biyu ita ce, a wane birni ne gidan rediyon CRI ya kafa rediyo na zangon FM na farko a kasashen waje?

Sanusi: Muna fatan za ku ba mu amsa kafin ran 31 ga watan Oktoba na bana. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China