in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin masu sauraron gidan rediyon CRI
2011-06-13 11:13:46 cri
Masu sauraro, a sassa daban-daban na duniya, akwai dimbin masu sauraro dake dinga sauraren shirye-shiryen CRI a kowace rana, kuma dalilin haka su kan kara sanin abubuwan dake faruwa a kasar Sin, da sauye-sauyen da kasar ke samu. Matukar maida hankali kan shirye-shiryen CRI ya kai wurin da wadannan masu sauraro za su iya gane muryar kowane mai gabatar da shiri na CRI, kuma sauraren shirye-shiryen CRI ya zama wani muhimmin batu a cikin zaman rayuwarsu na yau da kullum. To, tambayoyi biyu da za mu gabatar muku a yau sun shafi ku masu sauraro. Tambaya ta farko, kungiyoyin masu sauraro nawa ne gidan rediyon CRI ke da su a kasashen waje a halin yanzu? Tambaya ta biyu ita ce, menene sunan kungiyar masu sauraro ta farko ta gidan rediyon CRI?

Masu sauraro, yanzu bari mu gabatar muku da wani bayani dangane da wasu masu sauraron gidan rediyon CRI.

Masu sauraro, muryar da kuke saurara, murya ce ta wata shahararriyar mai gabatar da shirye-shirye ta CRI cikin harshen Swahili. Sunanta Madam Chen Lianying, kuma ta shafe tsawon shekaru 40 tana nuna himma da kwazo wajen gabatar da labarun kasar Sin ga masu sauraro a nahiyar Afirka cikin harshen Swahili, a kokarin karfafa dankon zumunci tsakanin jama'ar Sin da Afirka. A kasashen Kenya da Tanzaniya, akwai mutane da dama wadanda su kan saurari shirye-shiryen da Madam Chen Lianying take gabatarwa a kowace rana, har ma sun lakaba mata sunan "Mama Chen". "Mama Chen" ta ba mu wani labarin kamar haka:

"Wata rana na kai ziyara a wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Kenya, inda na tarar da mutanen Afirka da dama dake magana da harshen Swahili, jin haka ya sa ni ma na shiga cikin hirarsu. Ko da suka ji muryata, sai suka gane na zo daga gidan rediyon CRI. A ranar na yi matukar farin-ciki saboda masu sauraronmu a Afirka suna iya gane muryata, kuma kowa ya san 'Mama Chen' a wurin."

A dakin nuna tarihin gidan rediyon CRI, kowane sashin harshen waje na da nasa akwatin adana kayayyaki dake dauke da kyaututtuka, tsarabobi, da hotunan da ake nunawa da masu sauraro suka aiko mana daga sassa daban-daban na duniya.

A cikin akwatin adana kayayyaki na sashin harshen Vietnam, akwai wata tuta mai launin ja dake jawo hankali sosai. Shugabar sashin Vietnam Madam Wu Zhaoying ta bayyana labarin wannan tuta, inda ta ce:

"Shekara ta 1995 ta kasance shekara ta cikon shekaru 45 da kafa sashin Vietnam na CRI, albarkacin wannan rana wata mai sauraronmu daga birnin Ho Chi Minh mai suna Pham Thi Minh Trang ta dauki zare da allura domin saka wata tuta, inda ta rubuta kalmomin gaisuwa gare mu. Ko shakka babu kwarin-gwiwar da masu sauraro suka nuna ya kara sanya mana karfi wajen kara kyautata shirye-shiryen da muke gabatarwa."

Har wa yau kuma, da aka zo lokacin hunturu, ma'aikatan sashin Vietnam su kan ambaci sunan wata mai sauraro Phan Thi Ngoc. Ko da yake ba su taba ganinta ba ido da ido, amma a duk lokacin da ake ambatar wannan suna nata, ma'aikatan sashin Vietnam su kan ji dadi sosai. Madam Wu Zhaoying ta ci gaba da bayyana cewa:

"Akwai wata mai sauraronmu mai suna Phan Thi Ngoc. Ta san ana tsananin sanyi a birnin Beijing a lokacin hunturu, shi ya sa ta dinka rigunan sanyi da dama gare mu. A cikin wasikar da ta rubuto mana, ta ce, ana sanyi sosai a birnin Beijing, ya kamata masu gabatar da shirye-shirye su sanya rigunan sanyi, ta yadda ba za su kamu da mura ba, kuma za su gabatar mana da shirye-shirye masu dadin-ji. Lallai wannan lamari ya burge mu kwarai da gaske."

Masu sauraro, a shekara ta 1961, an kafa kungiyar masu sauraron gidan rediyon CRI ta farko a kasar waje, wato kungiyar masu sauraron gidan rediyon Beijing a kasar Japan. Ya zuwa yanzu, adadin yawan kungiyoyin masu sauraron gidan rediyon CRI a kasashen duniya ya kai 3165. Masu sauraro su ne suka kafa wadannan kungiyoyi, kuma burinsu shi ne kara fahimtar kasar Sin, da karfafa dankon zumunci tare da kasar ta hanyar sauraren shirye-shiryen CRI.

A lungun kudu maso gabashin gidan rediyon CRI, akwai wani yankin da aka dasa wani nau'in fure mai suna Cherry Blossom, kuma a watan Afrilun kowace shekara, furannin su kan fito, wadanda ke da kyan-gani da kamshi sosai. Shugabar sashin harshen Japananci na gidan rediyon CRI Madam Fu Ying ta ce, kungiyar masu sauraron gidan rediyon CRI dake lardin Nagano na kasar Japan ta bada wadannan itatuwan furannin Cherry Blossom kyauta ga CRI a shekara ta 1996, inda ta ce:

"Tsoffin masu sauraronmu daga lardin Nagano na kasar Japan sun zo da wadannan itatuwan furen Cherry Blossom. Gaba daya akwai itatuwa 21 a halin yanzu. A kowace shekara, akwai masu sauraro daga lardin Nagano wadanda su kan zo CRI domin duba wadannan furanni. Yanzu wadannan furanni sun kasance tamkar furannin zumunci tsakanin jama'ar kasashen Sin da Japan."

Dadin dadawa kuma, gidan rediyon CRI ya kan shirya gasannin kacici-kacici iri-iri a kokarin fadakar da masu sauraro kan ainihin halin da ake ciki a kasar Sin, kuma masu sauraro da dama sun samu damar kawo ziyara a kasar Sin. Shahararriyar mai gabatar da shirye-shirye daga sashin Swahili Madam Chen Lianying ta bayyana cewa:

"Bayan da aka kawo karshen gasar kacici-kacici dangane da kulla da zumunci tsakanin kasashen Sin da Tanzaniya cikin shekaru 45 da suka gabata, mun gayyato masu sauraro biyar don su kai ziyara a bikin EXPO na Shanghai, haka kuma sun samu damar kawo ziyarar yini biyar a nan birnin Beijing. Mun bayar da rahotanni na musamman dangane da ziyarar da wadannan masu sauraro suka yi a kasar Sin, kuma bayan da masu sauraronmu a kasashen Afirka suka saurari rahotannin da muka gabatar, sun aiko mana wasikun dake cewa, sun yi farin-ciki sosai kamar su ne suka kawo ziyara a kasar Sin."

A watan Mayun shekara ta 2005, a lokacin da kasa da kasa suke murnar cika shekaru 60 da samun galaba kan mayakan fascist, ma'aikaciyar sashin Rashanci na CRI Tian Tian ta samu wata wasikar e-mail, wadda tsohon mai sauraro na kasar Rasha Mista Fradkin Jevgenij mai shekaru sama da 70 a duniya ya rubuto mata. Tian Tian ta bayyana cewa:

"Mahaifin Fradkin Jevgenij ya taba halartar yakin duniya na biyu. A cikin wannan e-mail, Mista Fradkin ya aiko mana wasikar da mahaifinsa ya rubuta a fagen yaki, da hoton da shi da mahaifansa gami da kanwarsa suka dauka tare a shekara ta 1943. Sashin Rashanci na CRI na da wata al'ada, wato a lokacin muhimman bukukuwa ko kuma ranakun tunawa da wasu manyan al'amura, ya kan tsara shirye-shirye na musamman ta rediyo ko kuma yanar gizo ta Intanet, inda masu sauraro su kan ba mu hadin-kai sosai, su kan taimaka mana wajen tara bayanai da al'amuran da suka faru a kansu."

To, masu sauraro, yau mun gabatar muku da bayani na musamman, dangane da wasu labaran da suka shafi masu sauraron gidan rediyon CRI, wanda kuma ya kasance shiri na karshe cikin gasar kacici-kacici kan cika shekaru 70 da kafa gidan rediyon CRI. Yanzu bari in maimaito muku tambayoyi biyu da muka tsaida a shirinmu na yau. Tambaya ta farko ita ce, kungiyoyin masu sauraro nawa ne gidan rediyon CRI ke da su a kasashen waje a halin yanzu? Sa'an nan tambaya ta biyu ita ce, menene sunan kungiyar masu sauraro ta farko ta gidan rediyon CRI?(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China