Za a zabi fitattun kungiyoyin masu sauraro goma daga cikin dukkan kungiyoyinmu a duk duniya, dole ne kungiyoyin da za su shiga zaben ya kasance suna da cikakken tsarin aiki, su kan saurari shirye-shiryen CRI da kuma karanta shafin yanar gizo na CRI, ban da wannan kuma, su kan yada al'adun kasar Sin da CRI ta yadda za a kara habaka tasirinsu a duniya. A karshe, abu mafi muhimmanci shi ne su nuna kwazo da himma domin shiga aikin taya murnar cika shekaru 70 na kafuwar CRI. Bayan kammala aikin, za a watsa labaran da suka shafi wadannan kungiyoyi goma ta rediyo da harsuna 61 kuma za a buga takardun da abin ya shafa a kan shafin yanar gizo na CRI. Abu mai faranta rai shi ne za a nada musu sunan "nagartattun kungiyoyin masu sauraron CRI na shekara ta 2011", a sa'i daya kuma, za a gayyaci wasu wakilai zuwa kasar Sin a farkon watan Disamba na bana domin halartar bikin ba da lambobin yabo da sauran ayyukan da za a shirya musu.
Kawo yanzu, gaba daya yawan kungiyoyin masu sauraron CRI ya riga ya kai dubu uku da dari daya da sittin da biyar. Wasu kungiyoyi ne na masu sauraron shirye-shiryen rediyon kasar Sin, wasu kuwa kungiyoyin masu karatun shafinmu na yanar gizo ne. Cikin dogon lokaci, wadannan kungiyoyin masu sauraron CRI a kasashen ketare na taka muhimmiyar rawa wajen yada al'adun kasar Sin da yin farfaganda kan CRI da ingiza fahimtar juna da aminci tsakanin jama'ar kasar Sin da ma kasashen duniya baki daya.(Jamila Zhou)