in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayyanai kan kasar Libya
2011-03-25 08:40:29 cri
Kasar Libya na arewacin nahiyar Afrika, kuma tana kusa da tekun Bahar Rum a arewa, yayin da a gabas, kudu da yamma take dab da kasashen Masar, Sudan, Chadi, Nijer, Aljeriya da Tunsiya. Girman wannan kasa ya kai murabba'in kilomita miliyan 1.76, filaye da kashi 95 cikin 100 hoko ne da hamada. Yawan mutane da kasar take da shi ya kai miliyan 6.2, yawancinsu 'yan kabilar Larabawa da Berber masu bin addinin musulanci.

A ran 24 ga watan Disamba na shekarar 1951, Libya ta sanar da kafa mulkin 'yancin kai wato an kafa kasar tarrayar Larabawa wadda daga baya aka kyautata sunanta zuwa daular Libya. A ranar 1 ga watan Satumba na shekarar 1969, rundunar sojojin kasar a karkashin Gaddafi ta aiwatar da juyin mulkin kasa wanda ya hambarar da sarki Idriss tare da kafa jamhuriyyar Libya. Daga baya, a cikin shekarar 1977, an canja sunan kasar zuwa kasar jamhuriyyar Larabawa ta kasar Libya mai tsarin gurguzu. Kuma daga watan Afrilu na shekarar 1986, an fara yin amfani da sunan babbar kasar jama'ar Larabawa ta Libya mai tsarin gurguzu.

Tripoli babban birnin kasar Libya ya kasance wata tashar jiragen ruwa mafi girma a kasar wanda take kan gabar kudu ta tekun Bahar Rum, yawan mutanen birnin ya kai kimanin miliyan 1.7, dadin dadawa shi ne cibiyar siyasa da tattalin arzikin kasar, yawan kayayyakin masana'antun da wannan birni ke samar ya wuce rabi na dukkan kasar. Wannan birni na da gine-ginen gargajiya irin na wasan fada na tsohuwar daular Rome da fadace-fadace, har da masallatai na gargajiya masu dimbin yawa, hakan ya sa ya zama wurin yawon bude ido da na kiwon lafiya mai kyau a yanayin zafi.

Muhimmin albarkatun kasar Libya shi ne man fetur, yawan ma'addinan da aka gano ya kai ganga biliyan 43. Bayan man fetur, kasar na da gas, yawansu da aka gano ya kai cubic mita biliyan 1480. Tun lokacin da aka gano man fetur a kasar cikin sheakru 50 na karni na 20, sha'anin hakar da tace man fetur ya samu bunkasuwa cikin sauri. Kuma sha'anin man fetur ya zama muhimmin sha'ani na tattalin arzikin da kasar ke dogara kansa, yawan kudin shiga da kasar ke samu a wannan fanni ya kai kashi 95 bisa 100.

Gwamnatin Libya ta dauki manufofin samar da gatanci masu inganci ga jama'arta bisa kudin da ta samu daga sha'anin man fetur. Jama'ar kasar suna da ikon samun jiyya da ilmi kyauta, kuma suna iya samun rangwame daga gwamnati ta fuskar hatsi, halawa, shayi da dai sauran kayayyakin zaman rayuwa, kuma ta kyautata yanayin gidajen kwana ta hanyar daukar matakin gina gidajen kwana na hada karfin jama'a da na gwamnati tare.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China