in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan batutuwan da suka abku a kasar Libya a shekara bana
2011-03-23 15:34:06 cri
Bisa labarin da aka bayar a ran 20 ga wata, an ce, jiragen ruwan yaki na sojojin Amurka da na Britaniya da ke a bahar Rum sun harba makamai masu linzami zuwa kasar Libya. A wannan rana, jiragen sama na sojan kasar Faransa sun kai hare-hare har sau 4 ga kasar Libya, wadanda suka lalata tankokin da motoci na sojojin gwamnatin kasar Libya.

A ran 16 ga watan Faburairu, an yi zanga-zanga a wasu birane na kasar Libya, sun bukaci shugaban kasar da ya yi murabus daga mukaminsa, kuma an samu rikici tsakanin masu zanga-zanga da sojojin tsaron kasar.

A ran 20 ga wata, daya daga cikin diyan shugaban kasar Libya ya yi jawabi ta gidan talebijin, inda ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne za a samu yakin basasa a kasar.

A ran 22 ga wata, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta yanke shawarar dakatar da kasar Libya shiga taron kungiyar. Dalilin mawuyancin hali da rashin kwanciyar hankali a kasar Libya, sun sa kasa da kasa janye jama'arsu daga kasar.

A ran 26 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D ya zartas da kuduri na 1970, inda an yanke shawarar a sa takunkumin sayen makamai ga Libya, da hana shugaban kasar da iyalinsa zuwa kasashen waje, da haramta wa shugabar kasar na yin amfani da kudadensa da ke a bankunan kasashen waje.

A ran 1 ga wata, babban taron M.D.D ya zartas da wani kuduri, inda ya dakatar da kasar Libya daga kungiyar UNHRC. Wannan ne karo na farko da babban taron M.D.D ya dakatar da wata kasa daga kungiyar.

A ran 12 ga wata, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta yi taron gaggawa a birnin Alkahira, inda ta yi kira ga M.D.D da ta kafa yankin hana shawagin jiragen sama a kasar Libya.

A ran 13 ga wata, bayan kwato birane daban daban daga hannun masu zanga-zanga, sojojin gwamnatin kasar Libya sun fara dosan babban birni na biyu na kasar Libya.

A ran 17 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D ya zartas da kuduri na 1973, inda aka yanke shawarar kafa yankin hana shawagin jiragen sama a kasar Libya, tare da yin kira ga kasashen da abin ya shafa da su dauki matakai don kiyaye tsaron jama'ar kasar Libya.

A ran 18 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Libya ya bayyana cewa, kasar ta amince da kudurin da M.D.D ta dauka na kafa yankin hana shawagin jiragen sama a kasar, da kawo karshen duk wani aikin soja ba tare da bata lokaci ba.

A ran 19 ga wata, a birnin Paris, an bude taro kan aiwatar da kudurin shimfida zaman lafiya a kasar Libya. Jami'an kungiyar tarayyyar kasashen Larabawa da na kungiyar EU da wasu shugabannin kasa da kasa sun halarci taron, bangarori daban daban su yi kira ga gwamnatin kasar Libya da ta daina aikin soja.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China