in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarihin CRI Online
2011-01-14 22:54:08 cri
Kafin shekarar 1998, gidan rediyon CRI yana gabatar da shirye-shiryen rediyo da harsuna 43. A shekarar 1998, rediyon CRI ya kaddamar da tashar yanar gizo da aka sani da CRI Online cikin harsuna biyar, da suka hada da daidaitaccen Sinanci da harshen Cantonese, Turanci, Jamusanci da kuma harshen Spaniyanci.

A shekarar 2003, an kara wasu harsuna 26 da ake amfani da su wajen samar da bayanai a CRI Online, ciki har da Mongoliyanci, Malay, Thai, filipino, Polish, Hungarian, Serbian, Hausa, Indiyanci, Tamil, Laotian, Albanian, Czech, Turkanci, Kiswahili, Farsi, Pushto, Nepali, Urdu, Cambodian, Sinhalese, Bengali, Burmese, harshen Hakka, Minnanese da kuma Chaochow na kasar Sin. Idan an yi la'akari da harsunan Faransanci, Portugese, Korean, Rashanci, Larabci, Indonesian, Vietnamese, Romanian, Bulgarian, Esperanto, Italiyanci da Japonanci, wadanda tuni aka kaddamar da shafunansu, gaba daya yawan harsunan da ake amfani da su wajen samar da bayanai a CRI Online ya kai 43.

A shekarar 2004, kafar CRI Online ta hada kai da gidan rediyon jihar Xinjiang ta kasar Sin domin kaddamar da shafunan yanar gizo cikin harsunan Uygur, Kazakh da kyrgyz. Sa'an nan, a shekarar 2005, kafar ta CRI Online ta hada gwiwa da gidan rediyon jihar Tibet, inda suka gabatar da shafunan yanar gizo cikin yaren hla-sa da khampa na Tibet. Sakamakon haka, yawan harsunan da aka yi amfani da su a CRI Online ya kai 48.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China