A watan Afrilu da Agusta na shekara ta 2007, gidan rediyon CRI ya hada kai tare da kamfanonin sadarwa na China Unicom da China Mobile, a kokarin watsa labarai ta kafofin wayar salula da talabijin, kuma ya taimaka wa masu yin amfani da wayoyin salula wajen samar da hanyoyin sauraron shirye-shirye kai tsaye ko karbar shirye-shirye daga Intanet, wato ke nan an nuna cewa, gidan rediyon CRI ya samu babban ci gaba, inda ya tashi daga wata kafar yada labaru ta hanyar rediyo kawai zuwa wata kafar yada labaru ta hanyoyin zamani.
A watan Satumba na shekarar 2007, an bude tashoshin Intanet na CRI Webcast a hukunce, kuma an fara watsa shirye-shirye da harsuna daban daban a kasashe da dama.
Haka kuma a watan Disamba na shekarar 2007, gidan rediyon CRI ya kafa kwalejin koyon harshen Sinanci ta gidan rediyo a hukunce, kuma yana kokarin koyar da Sinanci a kan Intanet kuma da hanyoyin zamani, kuma yana koyar da Sinanci da yaren masu sauraro. Haka kuma ana koyar da dukkan kungiyoyin masu sauraron CRI Sinanci a nahiyoyi 5, kuma wannan ya zama wani gagarumin aiki ne na yada harshen Sinanci a duniya.