in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rumfar Nijeriya a bikin EXPO na Shanghai
2010-08-20 18:19:13 cri
Bangon rumfar Nijeriya a bikin EXPO na Shanghai yana dauke da siffar babban dutsen da ake kira Zuma Rock, wanda ke arewacin birnin Abuja, hedkwatar kasar, wanda kuma ake daukarsa a matsayin kofa ta birnin, haka kuma tamkar alama ce gare shi. Sa'an nan, an shafa wa rumfar Nijeriya launukan tutar kasar. A bakin kofar rumfar, an sanya wasu itatuwan kwakwa, domin bayyana irin yanayin halittu a Nijeriya.

Rumfar Nijeriya tana kokarin nuna wa jama'a wasu abubuwa daga fannoni uku da suka hada da "kasar da ke mashigin teku na yammacin Afirka" kuma "kasar da ke tasowa" kana da yaanyin "kasuwanci a Nijeriya", don bayyana yadda za a bunkasa birnin da ke da al'adu da kabilu iri daban daban. Cikin dakin "kasar da ke mashigin teku na yammacin Afirka", a kan nuna wa jama'a wasu alamu na al'adun gargajiyar Nijeriya da kuma yadda kasar Nijeriya ta ke a zamanin yanzu. Sa'an nan, dakin "kasar da ke tasowa" yana nuna wa jama'a bunkasuwar Nijeriya a fannoni daban daban tare kuma da samar musu labaran da suka shafi kasar. Har wa yau, dakin yana kuma nuna yadda kasar Nijeriya za ta kasance a nan gaba.

Ana iya karkasa rumfar Nijeriya zuwa gida biyar, ciki har da tattalin arziki da al'adu da tarihi da wasanni da kuma abinci. Har wa yau kuma, tana shirin yin wasu takardun bayanai, don tallata Nijeriya da kara jawo jama'a su zuba jari a kasar. A lokacin bikin EXPO, Nijeriya za ta gudanar da wasu bukukuwa a yayin ranar bude rumfar da ranar Nijeriya da kuma taron dandalin tattaunawar ciniki da zuba jari da za a yi a watan Agusta. Sa'an nan, hukumomin jihohi 36 na kasar su ma za su gabatar da shirye-shiryensu masu kayatarwa wadanda ke iya bayyana yanayin musamman da suke da shi ta fannonin yanayi da kabilu da al'adu da sauransu.

Akwai rumfunan nune-nune guda 42 da bikin baje kolin duniya na EXPO na Shanghai ta samar da mahalartar bikin in suna sha'awar yin hayarsu. Bangaren Sin ne ya kafa rumfunan, indakuma yake shirya nune-nune a cikin yawancinsu. Amma ta yaya ake iya gabatar wa kasashen duniya wata kasar da ba a san ta sosai ba? Kuma yaya ake bayyana sigar musamman ta ko wace kasa ta hanyar abubuwan da aka baje koli? Zhang Tianran, mai kula da shirya nune-nune a dakin kasar Nijeriya ta yi mana bayani a game haka.

"Bayan mun samu wannan aiki, da farko ba yadda za mu yi. A ganin galibin Sinawa, Nijeriya, wata kasa ce da ba su san ta ba." a cewar Zheng Tianran. A wancan lokaci, bangaren Nijeriya ya gabatar da cewa, ya fi kyau a ziyarci Nijeriya. Zheng Tianran da ma'aikatansu sun yi shakku saboda ba su da isassun ma'aikata, kuma ba su dace da yanayin wurin ba. Duk da haka, bangaren Nijeriya ya tsaya kan gayyatar su zuwa Nijeriya.

A karshen bara, Zheng Tianran da wata mai aikin zayyana ta daban Huang Tianran 'yan mata 2 sun bar birnin Shanghai a lokacin hunturu, sun isa Nijeriya mai yanayin zafi. Nijeriya kuma ta mai da hankali sosai kan zuwansu. Ta gayyace su ganawa da tsohon shugaban kasar. Wannan tsohon shugaban Nijeriya shi ne ya sa hannu kan kwangilar halartar bikin EXPO na Shanghai. Daga baya kuma, wadannan 'yan mata 2 na kasar Sin sun yi mako guda suna zazzagaya birane 2 na Nijeriya, wato biranen Abuja da Lagos. Sun kara fahimtar Nijeriya ta hakika. Sannu a hankali, Zheng Tianran ta sauya tunaninta. A maimakon al'adun gargajiya na wurin, rumfar nune-nune ta Nijeriya ta iya bayyana yadda wannan kasa take kasancewa a halin yanzu.

A wannan kasar da ke yammacin Afirka, birnin Abuja ya yi kama da yadda dimbin manyan birane suke kasancewa. Akwai bishiyoyi da yawa, haka kuma, motoci iri daban daban na kaiwa da kawowa a kan hanyoyi, sa'an nan kuma, gine-ginen zamani, kamar manyan filayen wasa, filayen jiragen sama, babban ginin sadarwa na duniya da gidan wasan kwaikwayon kasar, suna da kayatarwa a wannan kasa.

Zheng Tianran, da Huang Tianran sun taba ganawa da wasu jami'ai da kwararru a fannin al'adu a kasar Nijeriya,, inda suka saurari bayanai game da tarihi da al'adu na kasar. Saboda haka, suka bayyana surar rumfar kasar Nijeriya kamar 'Dutsen Zuma', wato daya daga cikin abubuwan mamaki guda 7 na nahiyar Afrika, wanda kuma ya zama alama ce ta birnin Abuja.

A rumfar kasar Nijeriya da fadinta ya kai muraba'in mita 300, wadannan masu sana'ar zane biyu ba su nuna al'adun gargajiya irin na Afrika sosai ba, ban da wani dakin nune-nune dake bayyana abubuwan da suke iya wakiltar tsohon tarihin Afrika kuma, a sauran dakuna biyu an bayyana irin yanayin da kasar Nijeriya ke ciki a zamanin yau, musamman ma an yi bayani sosai kan manyan masana'antu guda 9 na kasar Nijeriya. Bayan haka kuma, an gabatar da wata taswira da wani litaffi ta hanyar kamputa, inda 'yan kallo za su iya samun labaru game da yanayin da kasar ke ciki a fannonin sufuri, ma'adinai, tashoshin ruwa, da sauransu.

A kan wani bango na dakin nune-nunen, an lika wasu hotuna, wadanda yawancinsu sun fito ne sakamakon ziyarar da Zheng Tianran, da Huang Tianran suka yi a kasar Nijeriya, ciki har da ni'imatattun wurare, da sabbin titunan birane, da kuma kasuwanni masu ci, da sauransu. Amma, abin da ya fi burge wa shi ne, murmushin da jama'ar kasar suke nunawa. Zheng Tianran ta ce, 'Wannan ne karo na farko da na yi ayyukan nune-nune game da wata kasa, da wuya a yi bayyani kan wata kasar da fadinta ya kai muraba'in kilomita dubu 920 a cikin wani daki mai fadin muraba'in mita kusan 30.' Zheng ta kara da cewa, a karshe dai ta nemi wata hanya mai kyau, wato idan ana fatan fahimtar wata kasa, abin da ya fi muhimmanci shi ne, ka fahimci ra'ayin jama'ar kasar tukuna.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China