in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan taron koli na G8
2010-06-24 16:36:31 cri

Kungiyar G8 ta hada da kasashen Amurka da Ingila da Faransa da Jamus da Italiya da Canada da Japan da kuma Rasha. Kana taron koli na kungiyar G8 ya fito ne daga taron koli na kasashe 7 na yammacin duniya.

A watan Nuwamba na shekarar 1975, shugabannin kasashen Faransa da Amurka da Jamus da Japan da Ingila da kuma Italiya sun yi taron koli na tattalin arziki a garin Rambouillet dake karkarar birnin Paris bisa kiran da kasar Faransa ta yi domin cimma daidaito kan manufofin da wadannan kasashe suka tsara, ta yadda za a farfado da tattalin arzikinsu. A gun taron koli a karo na biyu da aka yi a shekarar 1976, kasar Canada ta halarci taron bisa gayyatar da aka yi mata, alkacin nan ne kungiyar kasashe 7 ta kafu, an fara kira wannan taro "taron koli na kasashe 7 na yammacin duniya". Daga bisani kuma, a kan kira wannan taro a kowace shekara a wadannan kasashe 7 daya bayan daya. Kana tun daga shekarar 1977, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya kan halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa.

A watan Yuli na shekarar 1991, a birnin London, an taron koli na kasashen yamma bakwai. Bisa matsayin kasa mai karbar bakunci, kasar Ingila ta gayyaci shugaban kasar tarayyar Soviet ya yi shawarwari da shugabannin kasashen bakwai bayan taron, wato shawarwari na "Bakwai da daya". Daga nan, bayan taron da ake yi a kowace shekara, shugaban Rasha ya kan halarci shawarwari na "Bakwai da daya". A shekarar 1994, an amince da kasar Rasha ta shiga tattaunawa kan batun siyasa.

A gun taron koli na kasashen yamma bakwai da aka yi a shekarar 1997 a birnin Danver na kasar Amurka, bisa gayyatar da aka yi masa, Yeltsin, shugaban kasar Rasha ya halarci taron bisa matsayi na daban a hukunce, kuma ya ba da sanarwa ta karshe bisa sunan taron koli na kungiyar kasashe takwas wato G8 tare da shugabannin kasashe bakwai. Sannan taron koli na kasashen yamma bakwai ya zama taron koli na kungiyar G8. Amma game da batun tattalin arziki, taron ya ci gaba da tsarin kasashen bakwai, kuma kasar Rasha ba ta shiga tattaunawa game da tattalin arzikin duniya ba.

A watan Mayu na shekarar 1998 a birnin Birmingham na kasar Ingila, an yi taron koli na kungiyar G8. A gun taron a wannan karo, kungiyar kasashen bakwai ta zama kungiyar G8 a sahihance kasar Rasha, ta zama mambar kungiyar G8 da gaske, kuma ta halarci dukkan tattaunawa ta G8. Amma, a hakika, kungiyar kasashen takwas tana ci gaba da bin tsarin G7.

A watan Yunin shekara ta 2002, a yayin taron koli na kungiyar G8 da aka yi a kasar Canada, an karbi kasar Rasha don ta zama membar kungiyar G8. Haka kuma a wajen wannan taro, shugabannin kasashe 8 sun cimma matsaya a game da batutuwa da dama, ciki kuwa har da ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci, da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, da yanayin tattalin arzikin duniya, gami da tallafawa kasashen Afirka da sauransu.

Da farko, taron koli na kasashen yammacin duniya 7 ya mayar da hankali kan batun tattalin arziki. Tun daga farkon shekarun 1980 na karni na 20, baya ga batun tattalin arziki, wannan taron koli ya fara mayar da hankali a kan muhimman batutunwan siyasa na duniya. A cikin 'yan shekarun nan, baya ga batutuwan da suka shafi harkokin siyasa na duniya da tattalin arziki, batutuwan sauyin yanayi da kiyaye muhalli sun zama abubuwan da aka tattauna a yayin taron.

An ce, muhimman batutuwan da za'a tattauna a wajen taron koli na G8 a wannan shekara sun hada da nauyin da za'a sauke a kai, da tabbatar da lafiyar yara da mata, da tsaron makaman nukiliya, gami da ayyukan yaki da ta'addanci. Ban da wannan kuma, batutuwan da za'a tattauna za su shafi sake farfado da kasar Haiti, da ayyukan yaki da fataucin muggan kwayoyi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China