in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan taron koli na G20
2010-06-24 10:43:46 cri

An kafa kungiyar kasashe 20 (G20) a ran 25 ga watan Satumba na shekarar 1999, kasashe mambobi sun hada da Amurka, da Japan, da Jamus, da Faransa, da Birtaniya, da Italiya, da Canada, da Rasha, da Sin, da Argentina, da Australiya, da Brazil, da India, da Indonesia, da Maxico, da Saudiyya, da Afirka ta kudu, da Korea ta kudu, da Turkiyya, har da kungiyar gamayar Turai (EU).

A ran 16 ga watan Disamba na shekarar 1999, ministocin kudi da shugabannnin manyan bankuna na kasashen membobin kungiyar G20 sun bude taro na farko na kungiyar G20.

A ran 15 ga watan Nuwamba na shekarar 2008, a sakamakon yaduwar matsalar hada-hadar kudi, shugabannin kasashen mambobin kungiyar G20 sun yi taro a Washington. Kuma a watan Afrilu da watan Satumba na shekarar 2009, kungiyar G20 ta yi taron koli na biyu a birnin London da taron koli na uku a birnin Pittsburgh.

Tun daga ran 26 zuwa ran 27 ga watan Yuni na shekarar bana, a Toronto na kasar Canada za a gudanar da taron koli na kungiyar kasashen 20 a karo na hudu. Shugaban kasar Sin Hu Jintao zai halarci taron.

A ran 22 ga wata, a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, za a bude taron kolin kungiyar G20 ne bisa halin da ake ciki yanzu na farfadowar tattalin arzikin duniya, duk da cewa tushen farfadowar ba shi da inganci, kuma halin da ake ciki ba shi da daidaici. A gun taron, bangarori daban daban da abin ya shafa za su yi shawarwari kan batun kara yin hadin gwiwa da mu'amala, don ci gaba da sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya.

A ran 3 ga wata, yayin da ministan kudi na kasar Canada Jim Flaherty ya kawo ziyara a kasar Sin, ya fallasa manyan batutuwan 4 da za a yi shawarwari kansu a gun taron, wato batutuwan tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci, aiwatar da shirin yin gyare-gyare hukumomin kudi don kyautata tsarin kudi na duniya, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin hukumomin kudi na duniya, da sa kaimi ga zuba jari don yin ciniki cikin 'yanci, da yin rigakafin da kariyar cinikayya.

Za a yi taron koli na kungiyar G8 a karo na 36 daga ran 25 zuwa ran 26 ga wata a birnin Huntsville na jihar Ontario ta kasar Canada.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China