in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na H
2010-06-21 16:37:43 cri

A yayin gasar karshe ta cin kofin FA na Ingila da aka yi a makon jiya, shugaban kyaftin din kwallon kafar maza ta kasar Jamus Ballack Michael ya ji rauni mai tsanani a kafa, a sanadin haka, dole ne ya huta har na tsawon makwani takwas, hakan ya sa, ba zai buga wasa a yayin gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Afirka ta kudu ba. Kevin Prince Boateng shi ne ya taka kafar Ballack, kuma yana wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta Portsmouth ta Ingila. A ran 18 ga wata, an buga hoton Ballack a kusan dukkan manyan jaridu na kasar Jamus, inda Ballack ke gogare da sandunan guragu biyu tare da bandeji a kafa, ban da wannan kuma, ana iya ganin hawaye na fita a idannunsa. Hakan ya bata ran masu sha'awar kwallon kafa na kasar Jamus matuka. Ana tsammani cewa, kila Boateng ya yi wannan laifi ne da gangan saboda zai bugawa kasar Ghana wasa a yayin gasar cin kofin duniya wadda ita ma tana cikin rukuni na 4 tare da kasar Jamus.

Ran 19 ga wata, daidai da agogon kasar Faransa, 'yan wasan wannan kasa wadanda ke shirye-shiryen shiga gasar cin kofin duniya sun je wani filin wasan skiing tsakanin duwatsu a karkashin dutsen Alps, dukkan 'yan wasa sun hau karshen kan wannan dutsen kankara, kuma sun sa takalma na musamman ne, kuma ba su yi amfani da kayan skiing ba, makasudin yin haka shi ne domin nuna niyyarsu ta samun sakamako mai gamsarwa a yayin gasar cin kofin duniya da za su shiga ba da dadewa ba, a sa'i daya kuma, suna fatan za su kara sabawa da yanayin kasar Afirka ta kudu.

Ran 19 ga wata, ministan kula da yawon shakatawa na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, kungiyar kwallon kafar maza ta kasar Korea ta Arewa ba ta tabbatar da tsarin ziyara cikin lokacin da aka tanadi ba, shi ya sa, kila ba za ta je Zimbabwe domin yin atisaye kafin gasar cin kofin duniya ba. Kazalika, ministan kula da ayyukan ba da ilmi da wasan motsa jiki da kuma wake-wake da raye-raye na kasar Zimbubwe shi ma ya bayyana cewa, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar ba ta samu wannan labari ko kadan ba daga wajen kasar Korea ta arewa. Kafin wannan, kasar Korea ta arewa ta tsai da cewa, za ta je kasar Zimbabwe domin yin atisaye kafin a fara gasar cin kofin duniya ta bana bisa gayyatar da Zimbabwe ta yi mata, kuma za ta sanar da tsarin ziyara ga kasar Zimbabwe kafin ran 19 ga wata.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Ingila tana nuna kwazo da himma domin shiga gasar cin kofin duniya da za a fara a ran 11 ga watan Yuni na bana. Ban da wannan kuma, sabon shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila Rio Ferdinand ya fito fili ya bayyana cewa, Ingila ta riga ta cika dukkan sharudan shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2018. Kuma kungiyar wakilan Ingila wadda ta hada da jakadan neman samun damar shirya gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 David Beckham ita ma ta shirya takardar neman wannan dama, amma wasu mutane suna tsammani cewa, Ingila za ta gamu da matsala saboda yanayi.

Yanzu ga wani bayani na musamman kan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta Afirka ta kudu.

Masu sauraro, a cikin shirin "wasannin motsa jiki" da muka gabatar muku a makon jiya, mun gabatar muku bayani game da rukunin G wato rukuni na 7. A cikin shirinmu na yau, za mu kara yin bayani kan rukunin H wato rukuni na 8. Wannan rukunin shi ma ya hada da kasashe hudu wato Chile da ake kiranta da sunan "kungiyar Barcelona ta nahiyar kudancin Amurka", Honduras wadda ta sake shiga gasar cin kofin duniya bayan shekaru 28 da suka wuce, Switzerland wadda ta shahara wajen kera agogo da kuma Spaniya wadda ita ce sabuwar zakarar gasar cin kofin Turai.

A cikin jerin sunayen kasa da kasa da babbar hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasashen duniya ta sanar a watan Nuwamba na shekarar 2009, Spaniya ta zama lambawan a maimakon Brazil. A sabili da haka, an dauka cewa, abin bukata ga Apaniya a yayin wannan babbar gasa shi ne neman samun zama zakara. Kamar yadda kuka sani, 'yan wasan Spaniya sun fi son nuna fasahar wasan kwallon kafa mai kyan gani kaman wasan yin fada da sa wato "bullfight". Yanzu, babban mai horas da 'yan wasan Spaniya Vicente Del Bosque ya riga ya zabi fitattun 'yan wasa da za su shiga wannan babbar gasa, ana iya cewa, Spaniya tana cikin shiri. Ko shakka babu, Spaniya ba za ta samu matsala wajen lashe sauran kasashe uku dake cikin rukuni na 8 ba wato Chile da Honduras da Switzerland, kuma za ta kai ga wasan kusa da na karshe. Amma, bayan gasa a cikin rukuni na 8, Spaniya za ta sha wahala a yayin gasar fid da gwani wato kila za ta gamu da kasashe masu karfi, misali Brazil da Portugal da Kote Divor da Italiya da Jamus, shi ya sa dole ne Spaniya ta yi kokari matuka idan tana son zama zakarar gasar cin kofin duniya ta Afirka ta kudu.

Game da Switzerland, sanin kowa ne cewa tana da karfi, amma 'yan wasa basa wasa tare yadda ya kamata. Babban mai horas da 'yan wasan Switzerland Ottmar Hitzfeld 'dan asalin Jamus ne, kawo yanzu, shekarunsa na haihuwa sun riga sun zarce sittin, duk da haka, ana fatan zai taka rawar gani a yayin wannan babbar gasa.

Honduras kuwa tana da tsari na musamman, babban mai horas da 'yan wasan Honduras Reinaldo Rueda Rivera 'dan asalin Colombia ne, ya taba yin aiki a wata jami'a ta Colombia, amma abin bakin ciki shi ne ba shi da isasshiyar fasahar horas da 'yan wasa. Abun ba da mamaki shi ne, an rubuta babban harafi na H a rigar 'yan wasan Honduras, ma'anarsa ita ce kasar Honduras, wannan ya bayyana cewa, 'yan wasan Honduras suna darajanta damar shiga gasar cin kofin duniya da suka samu kwarai, ko za su yi nasara, ko a'a, a ko da yaushe suna nuna kishi da biyayya ga kasarsu.

Ita ma Chile tana iyakacin kokari koda yake yawancin 'yan wasan wannan kasa su ne samari, amma kullum matasa sun fi kuzari. Game da wannan, babban mai horas da 'yan wasan Chile wato 'dan asalin Agentina Marcelo Bielsa ya kwarre wajen fasahar wasan kwallon kafa kuma yana kara yin nazari kan yadda zai kara kyautata fasahar wasan Chile. Bielsa ya fi son aiwatar da dabarar kai hari a yayin gasa, a sanadin haka, ana ganin cewa, tsarin 'yan wasan Chile ke ciki ya yi kama da na Barcelona, wato kallon fasahar wasan 'yan wasan Chile yana da kyan gani kwarai. To, bari mu sa ido mu jira gasar da za a yi tsakanin Spaniya da Chile a ran 21 ga watan Yuni na bana.(Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China