in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na G
2010-06-21 16:37:43 cri
Bayan da aka jefa kuri'a cikin kungiya kungiya a yayin gasar cin kofin duniya ta Afirka ta Kudu, a ganin kafofin yada labaru, rukuni na G, shi ne rukuni mafi hadari, rukunin da ya kunshi kasashen Brazil da ta ci kofin duniya har sau 5, kasar Portugal din da ke da Cristiano Ronaldo, da kasar Kodivwa din da ta yi fice wajen kai hari da ma tsaron gida, da Korea ta Arewa din da ba a san ta sosai ba. Kowa na tunanin cikin su 2 wace kasa ce za ta fito daga wannan rukuni?

Brazil, kasa daya tak da ta ci kofin duniya har sau 5 a duniya. Wannan ya sa a dukkan gasannin cin kofin duniya, ana kallonta a matsayin wadda za ta lashe kofin. Ko da yake tana cikin rukuni mafi hadari a wannan karo, amma kamar yadda Dunga, babban mai horas da 'yan wasan Brazil ya fada, Brazil ba ta da wani fargaba, za ta fito daga rukunin.

Carlos Queiroz, mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Portugal bai kwantar da hankalinsa kamar yadda Dunga ya yi ba. Portugal ta kusan rasa damar bayyana a Afirka ta Kudu. A kan hanyarta ta zuwa Afirka ta Kudu, ta gamu da matsaloli da dama, wannan ya sa har yanzu ba ta taka rawa mai kyau ba. Ta haka, a ganin masu sharhi kan kwallon kafa, Portugal ba za ta taka rawar gani ba a Afirka ta Kudu.

Watakila Korea ta Arewa da ba a san ta sosai ba ta fi tsoratar da sauran kasashe saboda kishin da suke da shi da taimakawa juna sosai da sosai a filin wasa da kuma dabarun wasa da ba a san su sosai ba. Haka kuma, wasu 'yan wasan kwallon kafa na Korea ta Arewa suna wasa a kasashen waje, kuma za su iya taka muhimmiyar rawa a Afirka ta Kudu. Duk da haka kasar tana fuskantar kasashe masu karfi a fagen wasan kwallon kafa a rukuni na G, inda za ta fuskanci babbar matsala wajen shiga fitattun kasashe 8 a yayin gasar kamar yadda magabatansu suka yi yau shekaru 44 da suka wuce.

Kasar Kodivwa dai tana da karfi, amma kullu ta kan gamu da rashin sa'a. Sau biyu kasar tana samun kanta cikin rukuni mafi hadari a yayin gasar cin kofin duniya. Amma 'yan wasan kwallon kafa na Kodivwa sun yi aniyar ba da mamaki a Afirka ta Kudu. Ba kasar da ta fi Kodivwa kwararrun 'yan wasan kwallon kafa a duk nahiyar Afirka, ko masu kai hari, ko tsaron gida, kamar Didier Drogba, Salomon Kalou, Didier Zokora, Yaya Toure, Emmanuel Eboue, Kolo Toure da kuma Boca Junior. Yawancin 'yan wasan Kodivwa suna wasa a shahararrun kungiyoyin kasashen waje, wannan ya sa ko da yaushe ake daukar Kodivwa a matsayin kasa mafi karfi a fagen wasan kwallon kafa a Afirka yanzu haka. Masu sharhi kan wasan kwallon kafa da dama sun yi hasashen cewa, Kodivwa za ta kasance cikin fitattun kasashe 8 a Afirka ta Kudu, za ta kai wani muhimmin matsayin da kasashen Afirka suka taba kasancewa a tarihin gasar cin kofin duniya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China