in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na F
2010-06-21 16:37:43 cri

Ran 19 ga wata, wani jami'i na ma'aikatar kula da huldar kasa da kasa da harkar hadin gwiwa ta kasar Afirka ta kudu ya bayyana a birnin Mexico na kasar Mexico cewa, kasar Afirka ta kudu tana sanya matukar kokari domin shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a bana cikin yanayin zaman lafiya, ta yadda dukkan mahalarta za su ji dadin kallon wasannin da za a yi, kuma su koma gida lafiya. Wannan jami'i ya kara da cewa, kasar Afirka ta kudu tana yin yunkurin gabatar da wata babbar gasa mai inganci a tarihin gasar cin kofin duniya. Ban da wannan kuma, hukumar 'yan sandan kasa da kasa ita ma za ta ba da taimako domin tabbatar da bude wannan babbar gasa cikin lumana da kuma kammala lami lafiya.

Ran 20 ga wata, a yayin bikin murnar fara aiki da sabuwar rumfa ta filin jirgin saman birnin Johannesburg, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da za a yi ba da dadewa ba ta samar da babbar dama ga kasarsa wajen kara bunkasa manyan gine-gine, haka kuma kasar Afirka ta kudu za ta more wadannan manyan gine-gine cikin dogon lokaci. Domin saukar bakuncin gasar cin kofin duniya, kasar Afirka ta kudu ta sake gina filayen jiragen sama da yawa a biranen da za a bubbuga wasanni a gasar cin kofin duniya, musamman ma a birnin Johannesburg saboda wannan filin jiragen sama ya fi muhimmanci. Mun sami labari cewa, tun daga shekarar 2005, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta kashe kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan biyu da miliyan dari bakwai domin yin manyan gine-gine.

Kwanakin baya, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kasar Ingila ta sanar da cewa, a makon jiya, an yi wa dan wasanta na gaba 'dan asalin kasar Spaniya Fermando Jose Torres Sanz tiyata a gwiwarsa, hakan ya sa dole ne ya yi hutu inda ba zai buga wasa ba har na tsawon makwanni shida, don haka, yanzu ba a san ko zai kasance a gasar cin kofin duniya ta kasar Afirka ta kudu ko a'a ba.

Ran 15 ga wata, daidai agogon birnin Beijing, a hukunce aka fara mataki na karshe na aikin sayar da tikitin kallon gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta kasar Afirka ta kudu. Tun daga wannan rana, masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Afirka ta kudu suke sayen tikiti a ofisoshin sayar da tikiti guda 11 da aka kafa a birane 9 da za a gudanar da wannan babbar gasa, kuma suna iya sayen tikiti a wurare guda 600 da bankuna daban daban suka kafa. Wannan shi ne karo na farko da masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar suke sayen tikitin kallon gasar da kudi kai tsaye amma ba ta hanyar yanar gizo da katin banki ba. Bisa kididdigar da hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta yi, an ce, bisa wannan mataki, gaba daya za a sayar da tikitocin kallon gasar dubu dari biyar, ya zuwa ran 19 ga wata, an riga an sayar da tikitocin da yawansu suka kai dubu dari daya da arba'in da biyar.

Yanzu ga wani bayani na musamman kan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta Afirka ta kudu.

Masu sauraro, a cikin shirin "wasannin motsa jiki" da muka gabatar muku a makon jiya, mun gabatar muku bayani game da rukunin E wato rukuni na 5. A cikin shirinmu na yau, za mu kara yin bayani kan rukunin F wato rukuni na 6. Wannan rukunin shi ma ya hada da kasashe hudu wato Italiya, Paraguay, Slovakia da kuma New Zealand. Koda yake kasar Italiya tana cikin wannan rukuni, amma an kimmanta cewa, wannan rukuni ba zai jawo hankalin 'yan kallo kamar yadda sauran rukunonin ba. Dalilin da ya sa haka shi ne domin a cikin wannan rukuni, babu taurarin 'yan wasa da yawa.

Kamar yadda kuka sani, a shekarar 2006, kasar Italiya ce ta zama zakara a yayin gasar cin kofin duniya a kasar Jamus, amma a halin da ake ciki yanzu, a sanadin tabarbarewar tattalin arziki, babbar gasar kwallon kafa tsakanin kungiyoyin cikin gida ta kasar Italiya wadda aka taba kiranta da sunan "karamar gasar cin kofin duniya" ba ta jawo hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa kamar yadda abin yake a da ba. Shi ya sa, babban mai horas da 'yan wasan kasar Italiya Marcello Lippi ya bayyana cewa, "Yanzu, a ganina, abu mafi muhimamnci gare mu shi ne zaman jituwa, ina fatan 'yan wasan kasar Italiya za su hada kansu kamar 'yan uwa cikin iyali daya, kuma za su yi hadin gwiwa cikin shiri tsakaninsu. Ban da wannan kuma, zan kara lura da raunin da wasu 'yan wasa suka ji, kuma ina kokarin neman wasu sabbin 'yan wasa, ta yadda za mu shiga gasa yadda ya kamata." Lippi ya fayyace cewa, ya riga ya zabi 'yan wasa 17 ko 18 domin shiga gasar cin kofin duniya a bana, kuma yana fatan Alessandro Nesta zai sake shiga gasar a madadin kasar Italiya. Amma a shekarar 2006, Alessandro Nesta ya taba sanar da cewa, ba zai sake bugawa a kungiyar kasar Italiya ba har abada, kila domin ya ji rauni a yayin gasar cin kofin duniya ta Jamus wanda ya hana shi ci gaba da wasa a gasar. Sau da yawa Lippi ya gaya wa Nesta cewa, yana da muhimmanci kwarai ga kasar Italiya, yanzu, ana jiran Alessandro Nesta da ya canja ra'ayinsa.

Ko shakka babu, kasar Italiya za ta zama ta farko a rukuni na 6, to, wace kungiya ko kasa ce za ta zama ta biyu?

A halin da ake ciki yanzu, kasar Paraguay ta zama ita ce ta 29 a fegen wasan kwallon kafa a duniya. Idan ta yi kokari, kila za ta lashe kasar Italiya a yayin karawar da za ta yi tsakaninta da kasar Italiya. Amma abun bakin ciki shi ne 'dan wasan gaba na farko na kasar kuma fitaccen 'dan wasan kwallon kafa na Amurka ta kudu na shekarar 2007 Salvador Cabanas ya ji rauni a kansa. A watan Janairu na bana, aka harbe shi da bindiga kuma ya ji rauni mai tsanani a kai. Ana iya cewa, ba mai yiwuwa ba ne Salvador Cabanas ya kasance cikin gasar.

Game da kasar Slovakia, abu mai faranta rai shi ne 'yan wasan kasar suna da hadin kai, amma fasahar wasa ta kasar ba ta cika kyau ba, saboda haka, muddin dai, sun yi kokari matuka kuma fiye da kima, wato kila za su kai ga zagaye na gaba.

Amma a bayyane ne kasar New Zealand ba ta karfi, ta taba shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 1982, amma ba ta sami sakamako mai gamsarwa ba. Dukkan 'yan wasan kasar 'yan wasa ne na cikin gida, wato ba ta hayar 'yan wasa daga kasashen waje. Kila ba za ta sami kome ba a yayin gasar, wato mai yiwuwa ne ta kasa yin komai a gasar.(Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China