in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na E
2010-06-21 16:37:43 cri
Masu karatu, bari mu leka kasashen da ke cikin rukuni na E, wato Holland da Denmark da Japan da kuma Kamaru.

Ada ya fito fili a gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya da za a yi a Afirka ta Kudu shi ne bambanta masu karfi da kuma marasa karfi ba tare da wata matsala ba. A cikin rukunoni da dama, in ba mu yi la'akari da sharrin kwallo ba, to, galibi dai ba za mu bukaci gudanar da wani nazari kansu ba, za mu iya tabbatar da kasashen da za su iya fitowa daga ko wane rukuni.

Ga alama, wannan gaskiya ne, malam. Amma ba za mu san cewa, ko kasashen Afirka za su yi amfani da damar shirya wannan gasa don taka rawar gani sosai a gasar da za a yi a nahiyarsu ko a'a. Ya fi kyau mu ci gaba da sa ido kan dukkan abubuwan da suka shafi gasar. Ina fatan kasashen Afirka za su ba duniya mamaki.

Bari mu mai da hankali kan rukuni na 5, inda kasashen Holland da Denmark suka fi karfi, musamman ma Holland. Duk da haka, ba za mu raina Japan da Kamaru ba. Yanzu Kamaru tana matsayin ta 20 a duniya a wasan kwallon kafa. 'Yan kwallo irinsu Alexandre Song Billong da Njitap Geremi da kuma Samuel Eto'o na Kamaru sun riga sun taka muhimmiyar rawa a wasan kwararru a wasan kwallon kafa ta kasar Birtaniya. Ban da wannan kuma, ko da yake 'yan kwallon Japan ba su da karfin jiki, amma tunanin zamani a game da wasan kwallon kafa da dabarun taka leda za su taimaka musu matuka, kuma hakan ya bai wa Japan karfin karawa da ko wace kasa.

Duk da haka, ana da dan damuwa ga Kamaru. Kusan ba ta taba karawa da sauran abokan karawarta 3 da ke wannan rukuni ba a da. A cikin rukuni na 5, Japan ta fi karawa da kasashen Afirka. A gasanni iri daban daban, Japan ta taba karawa da Kamaru har sau 3, inda ta sami nasara sau 2, yayin da ta yi canjaras da Kamaru sau 1. Sa'an nan a cikin wadannan gasanni 3 ta jefa kwallaye 4 cikin ragar Kamaru, yayin da Kamaru ta jefa mata kwallo daya kawai. Amma gasannin 3 da suka yi gasanni ne na sada zumunci kawai. Kuma sakamakon gasannin ba zai iya nuna ainihin karfinsu ba. Kamaru ita ma tana fuskantar matsalar da kusan dukkan kasashen Afirka ke fuskanta, wato 'yan kwallo sun gaza wajen nuna dabarar wasan da ta fi dacewa, a maimakon haka, kowa ya fi nuna kwarewarsa fiye da wasa tare. Kungiyar da ke da irin wadannan 'yan kwallo kan ba da mamaki kullum. Idan har ba ta da wata matsala, za ta iya lashe dukkan abokan karawarta, amma idan ta gamu da wata matsala, to, kowa zai iya lashe ta. Bugu da kari kuma, kasa ta farko da za su kara ita ce Japan a Afirka ta Kudu a watan Yuni na bana.

Za a yi wannan gasa a Afirka. Wannan shi ne abun farin ciki ga kasar Kamaru, saboda za ta yi gasa cikin yanayi da muhallin da ta sani kuma ya dace da su sosai. Denmark za ta kara da Holland a zagaye na farko, in wata daga cikinsu ta sha kaye, kuma Kamaru ta samu nasara, to, zakin Afirka zai yi tunanin samun nasarar fitowa daga rukunin. Haka zai kawo wa wannan kungiya nasara da kuma matsala a lokaci guda, saboda ta kan nuna zakuwa kwarai da gaske, amma a wani lokaci suna iya zama dari dari. Muddin ta yi watsi da matsin lamba a tunani, to, za ta fito daga rukunin, amma in ta yi zumudi fiye da kima, ta yi kuskure mai ban mamaki, sai ta koma gida ba tare da samun kome ba.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China