in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na D
2010-06-21 16:37:43 cri

Ran 8 ga wata da asuba, agogon birnin Beijing na kasar Sin, aka kammala dukkan gasanni na matsayi na uku na babbar gasar neman zama zakara a Turai. Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen na kasar Jamus ta yi nasarar kaiwa ga zagaye na gaba wato wasan kusa da na karshe koda yake kungiyar Manchester ta lashe ta da ci 3 da 2, amma kulob din Bayern Munchen ya fi yawan jefa kwallo cikin raga. A yayin wata gasa daban da aka yi tsakanin kulob Bordeaux da Lyon, Bordeaux ne ya yi nasara, amma Lyon ya samu damar kaiwa zagaye na gaba bisa yawan makin da ya samu. Wannan shi ne karo na farko da kulob din Lyon ta shiga gasar kusa da na karshe ta gasar neman zama zakara ta Turai.

Ran 7 ga wata da asuba, agogon Beijing, an yi wasan neman shiga matsayi na uku na gasar neman zama zakara a Turai har guda biyu, inda kulob din Barcelona ta kasar Spain ta lashe Arsenal ta kasar Ingila, a yayin wannan gasa, 'dan wasa Lionel Andres Messi ya jefa kwallo cikin ragar Arsenal har sau hudu. Ban da wannan kuma, Inter Milan ta lashe kulob din CSKA Moscow ta kasar Rasha kuma ta samu damar kaiwa zagaye na gaba. Wannan shi ma karo na farko ne da Inter Milan ta samu nasarar kaiwa wasan kusa da na karshe bayan shekarar 2003.

Ran 7 ga wata, agogon Beijing, kungiyar kasar Japan ta yi wasan sada zumunci da 'yan wasan kasar Serbia wadda ta kai ziyara a kasar Japan. A karshe dai, an doke kasar Japan da ci 3 da nema. A gun wani taron ganawa da manema labaran da aka yi, babban mai horas da 'yan wasan kasar Japan Takeshi Okada ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na karshe da kasar Japan ta yi wasan sada zumunci kafin a sanar da sunayen 'yan wasan da za su shiga gasar cin kofin duniya ta bana. A yayin wannan wasa, yawancin 'yan wasan kasar Japan sabbin 'yan wasa ne da aka shigo da su ba da dadewa ba, kasar Serbia kuwa dukkan 'yan wasan da suka shiga wannan wasa 'yan wasa ne masu neman shiga gasar.

Bisa labarin da kafar watsa labarai ta kasar Agentina ta bayar, an ce, mai tsaron gida na kasar Agentina Sergio Romero ya ji rauni a gwiwa a lokacin da yake wasa, koda yake an yi masa jiyya cikin gaugawa, amma bai sami sauki sosai ba, shi ya sa kila ba zai buga wasa ba har na tsawon watanni shida. Wannan zai yi tasiri ga kasar Agentina a yayin gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Afirka ta kudu a watan Yuni na bana.

Kwanakin baya, tauraron 'dan wasa na kasar Brazil Ronaldinho ya sake nuna fatansa cewa yana son sake bugawa kasar Brazil kwallo domin shiga gasar cin kofin duniya, kuma ya sami goyon baya daga wajen babban mai horas da 'yan wasan kulob din AC Milan da yayansa da kuma shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Brazil. Yanzu suna yin kokarin shawo kan Dunga, babban mai horas da 'yan wasan kasar Brazil. In Dunga ya yarda, Ronaldinho zai cimma burinsa.

Yanzu ga wani bayani na musamman kan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta Afirka ta kudu.

Masu sauraro, a cikin shirin "wasannin motsa jiki" da muka gabatar muku a makon jiya, mun taba karanto muku wani bayani game da rukunin C wato rukuni na 3. A cikin shirinmu na yau, za mu kara yin bayani kan rukunin D wato rukuni na 4. Rukunin shi ma ya hada da kasashe hudu wato Jamus da Serbia da Ghana da kuma Australia, ana daukar wannan rukuni a matsayin wani rukuni mai cike da rikici saboda za su yi kazamin karawa tsakaninsu.

Kamar yadda kuka sani, kasar Ghana tana kara karfi sosai, a watan Janairu na bana, kasar Ghana ta sami lambar azurfa a gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka, ana iya cewa, kasar Ghana tana cikin shiri. A halin da ake ciki yanzu, kasar Ghana tana da shahararrun 'yan wasan kwallon kafa da yawa, misali, Michael Essien da Sulley Muntari da Amoah, wadannan 'yan wasa sun taba buga a wasan kwallon kafa a Turai. Ban da wannan kuma, kasar Ghana ta fito ne daga yammacin Afirka, saboda haka, 'yan wasan wannan kasa suna nuna kishi yayin da suke buga kwallo. Abu mai faranta ran mutane shi ne yanzu babban mai horas da 'yan wasa kasar Ghana shi ne 'dan kasar Serbia Rajevac, shi ya sa, ko shakka babu ya fi fahimtar halin da kasar Serbia ke ciki. Duk da haka, kasar Ghana ba ta da 'dan wasan gaba tauraro mai karfi, a sanadin haka, kasar Ghana ba ta kware ba wajen kai hari, yana da kyau ta kara ba da muhimmanci kan wannan bangare.

Game da kasar Jamus, a zukatun yawancin masu sha'awar wasan kwallon kafa a duk fadin duniya, ko shakka babu, kasar Jamus tana da karfi, kuma ta taba zama zakarar gasar cin kofin duniya har sau uku. Kamata ya yi kasar Jamus za ta lashe sauran kasashe uku na wannan rukuni, amma, a hakika dai, kila ba haka al'amari yake ba. Tun bayan da aka kammala gasar cin kofin Turai a shekarar 2004, sai aka fara shakku kan karfin 'yan wasa na kasar Jamus. Kuma a shekarar 2006, kasar Jamus ta taba samun damar zaman lamba uku a yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa, kuma a shekarar 2008, kasar Jamus ta taba zama ta uku a yayin gasar cin kofin Turai ta wasan kwallon kafa. Ana iya cewa, kasar Jamus ta taba samun sakamako mai gamsarwa, yanzu tabbas ne babban mai horas da 'yan wasan kasar Jamus Joachin Low da 'yan wasa irinsu Ballack Michael da Philipp Lahm da Mesut Oezil za su ci gaba da sanya kokari matuka domin neman samun damar kaiwa ga zagaye na gaba.

Amma kasar Serbia ita ma tana da karfi, ana kiranta da sunan "kasar Brazil a Turai", fasahar wasa ta kasar Serbia ta fi jawo hankulan 'yan kallo saboda tana da kyan gani kwarai. Bayan gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006, kasar Serbia ta kara shigo da sabbin 'yan wasa matasa da yawa, misali, 'dan wasan baya Nemanja Vidic da 'yan wasan tsakiya Dejan Stankovic da sauransu.

Ita kuma kasar Australia ta taba lashe kasar Croatia ta nahiyar Turai da kasar Japan ta nahiyar Asiya a yayin gasar cin kofin duniya a shekarar 2006, har ta taba samun damar kaiwa ga zagaye na gaba da kasashe 16 mafiya karfi suka fito bayan fafatawar da syja yi. Shi ya sa, bai kamata ba a kasa kula da ita. Yanzu karfin kasar Australia ta yi kama da na shekarar 2006, babban mai horas da 'yan wasan kasar Autralia na yanzu Danny Welbeck ya bayyana cewa, dole ne su kara daga matsayinsu, saboda dole ne kowa ya yi iyakacin kokari domin cim ma burinsa. Kasar Australia za ta kara a karo na farko da kasar Jamus. (Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China