in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na C
2010-06-21 16:37:43 cri
Masu karatu, bari mu yi nazari kan rukuni na C, wanda kasashen Aljeriya da Birtaniya da Amurka da kuma Slovenia ke ciki.

Ga alama za mu iya bambance wadda ta fi karfi da kuma, wadda ba ta da karfi sosai a wannan rukuni.

Birtaniya ta dade tana kan gaba a duniya a wasan kwallon kafa. Ko da yake ba ta sake lashe kofin duniya ba tun bayan da ta lashe kofin a shekarar 1966, amma ba za mu rena mata ba. Amurka kuma an mayar da ita kamar hamada ce ta wasan kwallon kafa, inda wasan bai sami karbuwa sosai ba. Amma ta shiga jerin kasashe 8 mafiya karfi a yayin gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya a shekarar 2002. Aljeriya da kuma Slovenia sun yi kama da juna a fannoni da dama, domin sun samu damar zuwa Afirka ta Kudu ne a sakamakon samun nasara a karin gasannin tacewa. In an kwatanta su da saura, ga alama, su ne a baya-baya a nahiyoyin da suka fito. In dai ba a sharrin kwallo ba, Birtaniya da Amurka za su fito daga rukuni na C, amma a wasu lokuta, watakila matsalolin da ke damunka za su shafi ka.

A ranar 11 ga watan Yunin bana, wato ranar bude gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu, 'yan Masar da ke kasancewa cikin yankin da agogon wurin ya kusan yin daidai da na Afirka ta Kudu za su nuna rashin jin dadi a zukatansu. Za su yi tunani kan cewa, me ya sa a nahiyar Afirka, a kan yi karin gasa guda kawai domin tace wadda za ta bayyana a Afirka ta Kudu? A hakika in ba ka taki sa'a ba, to, karin gasanni dari daya za su kasance tamkar ba komei ba a gare ka. Wa ya taki sa'a? A wajen 'yan Aljeriya, wadanda ba su bayyana a gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya ba har na tsawon shekaru 24. Sun lashe 'yan kwallon Masar da ci daya ba ko daya, kuma sun sami damar zuwa Afirka ta Kudu a karshe.

A kan siffanta Aljeriya kaman yanyawa ce a hamada. Amma ta sha wahalhalu a kan hanyarta ta shiga gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya, an sha cutar ta. A shekarar 1982, Aljeriya ta ba duniya mamaki kwarai da gaske. A rukunin da take ciki, ta lashe kasar Jamus ta Yamma da ci 2 da 1. Watakila ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka, wadda ta shiga gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya. Amma abun da ya faru ya wuce zatonta matuka. A zagaye na karshe, Jamus ta Yamma ta lashe Austria da ci 1 ba ko daya. Kasashen 2 da ke da kakanin-kakani iri daya dukkansu sun bayyana a kasar Spaniya da ta shirya gasar. Abun da ya faru da Aljeriya ya sanya kungiyar FIFA ta yi gyare-gyare kan tsarin wasanni na gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya, wato an fara dukkanin gasannin tacewa na zagaye na karshe a lokaci guda, da zummar yi kokarin magance hadin baki a tsakanin kasashe. Duk da haka gyare-gyaren ba su canza makomar Aljeriya ba. A shekarar 1986, ba ta bayyana a kasar Mexico da ta shirya gasar ba, daga baya ta bar fagen gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya.

A gasannin tace wadanda za su bayyana a Afirka ta Kudu, ko da yake ma iya cewa, hakika Aljeriya ta taki sa'a. Amma a kan hanyarta ta zuwa Afirka ta Kudu, ta lashe kasar Senegal wacce ita ma kasa ce mai karfi a fagen kwallon kafa. Bayan haka, ko da yake ba a dauki Aljeriya a matsayin daya daga cikin kasashen Afirka da suka yi fice a wasan kwallon kafa ba, amma 'yan Aljeriya sun nuna gwaninta matuka a wasan. Kada mu manta. Shahararren dan kwallo Zinedine Zidane na Faransa asalinsa dan Aljeriya ne. Yanzu wasu 'yan kwallon Alheria suna wasa a Turai. Haka kuma, Aljeriya ta ci gajiyar gyare-gyaren da kungiyar FIFA ta yi kan tsarin asalin 'yan kwallo. Babban mai horas da 'yan wasanni na Aljeriya yana iya zabar fitattun 'yan kwallon da suka samu horo a Faransa na horas da sabbin jini, musamman ma wadanda suka taba jagorantar Faransa a gasannin duniya. Wadannan 'yan kwallo matasa asalinsu 'yan Aljeriya ne. Watakila wadannan abubuwa ba za su wadatar ba, Aljeriya ba za ta sami kyakkyawar nasara a wannan karo ba. Kungiyar FIFA ba ta karfafa tunani kanta ba, ba a mai da hankali kanta sosai ba. Amma kamar yadda Rabah Saadane, babban mai horas da 'yan kwallon Aljeriya ya fada, dukkan wadannan abubuwa sun taimakawa Aljeriya ta sake jawo hankalin mutane kanta a wasan kwallon kafa.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China