in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na B
2010-06-21 16:37:43 cri

Wasu labaran da suka shafi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da za a yi a kasar Afirka ta kudu:

A watan jiya wato watan Fabrairu na bana, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Kote Divor ta taba sanar da cewa, tsohon babban mai horas da 'yan wasan kwallon kafa ta kasar ya yi ritaya, amma har yanzu ba a nada sabon babban mai horas da 'yan wasan kasar ba tukuna, kila za a zabi daya tsakanin Sven Goran Eriksson wanda ya taba zaman babban mai horas da 'yan wasan Ingila da Bernd Schuster, tsohon babban mai horas da 'yan wasan Real Madrid.

Kwanakin baya, mai horas da 'yan wasan kasar Agentina Diego Armando Maradona ya fayyace cewa, ya riga ya zabi 'yan wasa biyu da za su shiga gasa ta farko da za a yi tsakanin kungiyarsa da "Super Eagles" ta kasar Nijeriya a birnin Johanesburg a ran 12 ga watan Yuni. Wadannan 'yan wasa biyu su ne Lionel Andres Messi da Javier Alejandro Mascherano.

Yanzu a kasar Afirka ta kudu, ana gudanar da wani shiri na musamman game da "rage kiba" inda hukumar 'yan sanda ta bukaci dukkan 'yan sanda na kasar da su motsa jiki domin kiyaye nauyin jiki, ta yadda za su yi aikin kiyaye kwanciyar hankali a yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da za a yi a kasar a watan Yuni yadda ya kamata.

Kwanakin baya ne hukumar kula da bayar da agajin gaugawa ta birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu ta bayyana cewa, za ta samar da aikin kiyaye zaman lafiya mai inganci a dukkan fannoni a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a watan Yuni na bana. Misali, hadarin fitar da iska mai guba da rushewar dakunan wasan motsa jiki da hadarin jirgin sama da aukuwar ambaliyar ruwa da dai sauransu. Hukumar ta yi alkawari cewa, ta riga ta kammala dukkan ayyukan share fage domin tabbatar da gudanarwar wannan babbar gasa cikin nasara.

Kawo yanzu dai, ya rage watanni biyu kawai a fara gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a kasar Afirka ta kudu, amma ba a tafiyar da aikin sayar da tikitin kallon gasar yadda ya kamata ba. Kwanakin baya, hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana cewa, gaba daya akwai tikitoci miliyan biyu da dubu dari tara da hamsin, amma, kawo yanzu, ba a sayar da tikiti dubu dari shiga da hamsin da suka rage ba. Kila ba za a sayar da dukkan tikitin ba ke nan. Kafofin watsa labarai sun yi bincike kuma sun bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin farashin masaukin baki da sufuri da kuma matsalar kwanciyar hankalin da ake fuskanta a kasar.

Yanzu ga wani bayani na musamman kan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta Afirka ta kudu.

Masu sauraro, a cikin shirin "wasannin motsa jiki" da muka gabatar muku a makon jiya, mun taba karanto muku wani bayani game da rukunin A wato 1 da kungiyar kasar Afirka ta kudu, kasa da ta shirya wannan gasa ke ciki, a cikin shirinmu na yau kuwa, za mu kara yin bayani kan halin da rukunin B wato 2 ke ciki yanzu. Abu mai ban sha'awa shi ne rukunin 2 ya hada da kasashe hudu da suka fito daga nahiyoyi hudu, misali kasar Agentina ta zo daga Latin Amerka, kasar Korea ta kudu da ta zo daga Asiya, sai kasar Nijeriya ta zo daga nahiyar Afirka, ban da wannan kuma, kasar Girka ta zo ne daga nahiyar Turai. Wadannan kasashe hudu za su kara da juna domin neman samun damar kaiwa ga zagaye na gaba da kasashe 16 mafiya karfi za su fito bayan fafatawar.

Kowa ya sani, a shekarar 1994, a karo na farko ne kasar Nijeriya wato "Super Eagles" ta kai ga wasan karshe a yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da aka yi a kasar Amurka. Amma ta samu zama ta 9 kawai, ana tsammani cewa, kila ta gamu da fitaccen 'dan wasa na kasar Italiya Roberto Baggio, in ba haka ba, za ta sami sakamako mai gamsarwa. Duk da haka, a nahiyar Afirka, har ma a fadin duniya, ana daukar kasar Nijeriya a matsayin "bakin doki" wato "black horse", ana fatan za ta yi kokarin neman samun zama zakara a gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a bana.

Kamar yadda kuka sani, a gun gasar zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka bana, kasar Nijeriya ta yi nasara sau shida kuma ta sami maki 18, ta zama kasa daya tilo da ta samu cikakkiyar nasara a nahiyar Afirka. Abu mafi ba da mamaki shi ne a yayin gasar, Nijeriya ta lashe kasar Afirka ta kudu har sau biyu. Wannan ya alamanta cewa, kasar Nijeriya tana cikin shiri. Domin neman samun sakamako mai gamsarwa a yayin wannan babbar gasa, yanzu kasar Nijeriya ta yi hayar shahararren mai horas da 'yan wasa Lars Lagerback daga kasar Sweden inda ta ba shi albashi mai yawa, abin bukata ga Nijeriya a karon farko shi ne kaiwa ga wasan kusa da na karshe. Ko shakka babu, shahararrun 'yan wasan kasar irinsu John Obi Mikel da Obafemi Akinwunmi Martins da sauransu za su yi iyakacin kokari. A yayin gasar da za a yi tsakanin kasashen dake cikin rukunin B, da farko dai, kasar Nijeriya za ta kara da kasar Agentina, abu mafi muhimmanci ga 'yan wasan kasar Nijeriya shi ne cike da imani, idan sun yi nasara, to, za su cike da imani a nan gaba.

Game da kasar Agentina, lallai tana da karfi, kuma wannan shi ne karo na 15 da ta shiga gasar a mataki na karshe ta gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa, kuma a shekarar 1986, ta taba samun damar zaman zakara, amma, sau daya ke nan, bayan wannan, ba ta sake zama zakara ba a yayin gasar cin kofin duniya.

Amma kasar Korea ta kudu tana kokari, a yayin kowace gasa, a ko da yaushe, 'yan wasan kasar Korea ta kudu su kan yi kokari matuka, ko su samu nasara, ko ba su cika burinsu ba, kullum suna cike da imani, ana iya cewa, imani shi ne makami mafi muhimmanci na 'yan wasan kasar Korea ta kudu.

Ita kuma kasar Girka, ta taba shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 1994, kuma wannan shi ne karo na biyu da ta shiga gasar, kuma ta sake zama a cikin rukuni daya tare da kasar Nijeirya da kasar Agentina.(Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China